← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 42 OF 247

Sashe 42

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature __________________________ A hankali ta bu e idanunta wadanda suka kumbura suntum da su sakamakon kukan da tasha jiya, urawa ceilling din dakin idanu tayi na an wani lokaci zuciyarta cike fal da tunanin meya faru da ita a jiya? tamkar tayi loosing memory inta, da sauri ta sanya hannu ta shafa kayan jikinta, lokaci aya ta yunkura ta mi e zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, ko'ina na bedroom dinsu ta soma bi da kallo kafin ta sauke idanunta akan batool da ke kwance gefenta tana bacci, tayi mamakin ganin kayan bacci a jikinta, ar gown ce da bata wuce gwiwarta ba, launin purple colour, ta rude sai faman shasshafa jikinta take yi burin ta ta tunano ya akai aka canza mata kayan jikinta! kamar ma hada wanka akayi mata, hannu tasa ta an bugi kanta a kokarinta nata farkar da kwakwalwarta ko taci gaba da yin aiki yadda ya dace. ofar akinsu akayi da sauri taja bargo ta lullu6e kanta, tunkafin ma taga wanene. Atare suka shigo dakin, boss tare da Ummi da ke abiye da shi cikin shiga ta kimono robe, ta yafa gyale a kafadarta, hannun kowannan su ru e da aramin tray na kayan abincin. "Barka da safiya daughter" wani irin wurgi tayi da bargon gefe aya ya fa a kan Batool, ta ago tana faman zare mashi idanunta. Sunyi mamakin ganin yadda ta zabura, ummi tace"ko dai har yanzu jikin ne"? Ko kallo unaisah batai mata ba idanunta na akan taj, wanda ke sanye da facemask, A hankali take tariyo abun da ya faru jiya, lokaci daya ta rushe masu da matsanancin kuka wanda yayi silar farkawar batool. Hankalinsu atashe su ka soma ambaton sunanta, tare da tambayarta meke damunta! Ko ciwonta ya motsa. Sauko tayi daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja kofa ta rufe tana cigaba da yin kukan Kallon juna ummi da taj sukayi a lokaci aya, fuskokin su dauke da matsanancin damuwa, atare suka daura trays din hannun su kan table suka nufi bakin kofar toilet Batool dake zaune kan gadon sai faman mutsustsuke idanu takeyi tana ambaton sunan unaisah... Magiya suka dinga yi mata akan ta bu ofar "Dan Allah unaisah Ki fada mana meke damunki? Ko cikin ki ke maki ciwo? Idan akwai inda ke maki radadi ki fadamin Yanzun nan zanje na karbo maki magani, wallahi mun damu dake jiya ko runtsawa bamuyi ba, har sai da muka ga kinyi bacci" cikin sigar lallashi ummi takeyi mata magana. "My daughter ki yi shiru ki saurare ni, nasan meke damunki, ni nasan dama dole kiji haushi, inaso ki kwantar da hankalin ki, saboda mun riga da mun gano wacece tayi maki aika aikarnan kuma in sha Allah zamu hukuntata, idan ma kinaso zamu kawo maki ita, ki rama abunda tayi maki" Maimakon unaisah ta sassauta kukanta, jin lallashinta da suke yi mata sai ma takara sautin kukan nata tamkar zata fasa kunnuwansu, da gudun gaske sajeed Ya fado dakin Yana haki daga shi sai gajeran wando bai jima da shigowa ba naufal Ya shigo shima yana tambayar meye faru da angel dinsu? Shigowa suka dinga yi, daga me hamma sai mai mi a daga gani basu jima da farkawa daga bacci ba, dama da tunaninta suka kwanta bacci jiya shiyasa suka farka da ita aransu, atare Jemimah da Azeeza suka shigo kowannan su kayan bacci ne a jikin shi, ba su jima da shigowa ba, Parveen ta shigo hannun ta ru e da brush, sumar kan nan a haukace gyaran gashin da akayi masu duk ya tarwatse kowa fa hankalinsa Ya tashi matu a, Jemimah sai kuka takeyi masu hada tsallanta tana fadin dama tasani mutanan nan sai da suka cutar mata da Angel dinta, wallahi bazata yale su ba dole ta rama mata... Gaba ayan su sunyi curko curko abakin kofar toilet din "Please ku kwantar da hankulan ku, ku bari muyi kokarin shawo kanta sai muji meke damunta" ummi ta fada tana duban su kafin ta mayar da dubanta ga boss man. "nifa ina tunanin watakil ko tayi zaton kai ne kayi mata wanka a daren jiya shiyasa take kuka" Dafe kanshi yai da hannu aya saboda shi ma ya yarda da maganar ummi, cikin muryar lallashi Yace"Unaisah, bani ne nayi maki wanka ba, Aunty umminku ce, bayan na dawo dake jiya na kawo ki gida da taimakonta kika tsarkake jikinki har kikayi wanka.. " kafin Ya kare maganar, cikin muryar kuka tace"ni ba wannan bane damuwana ba, daddy meyasa za ka yi min haka? Hankali atashe taj ya an zaro idanu Ya dubi ummi babu alamun ya fahimci abunda Unaisah take nufi sai ma cewa yayi"kinyi mafarki ne da daddynki"? A tsiwace tace"ba mafarki nayi dashi ba, a zahiri na ganshi jiya, saboda me zaka dinga 6oye min kanka daddy, ko ka daina sona ne" ta fa a tana haki Dariya ce ta kubcewa ummi ganin yadda taj ya daura hannayensu biyu saman kanshi alamar Ya shiga Uku gaba daya yabi ya ru e Sai lokacin Ya tuna da abun da Ya faru Jiya, da kanshi Ya cire facemask dinsa Ya jefar da shi saboda baya ahayyacinsa ashe idonta biyu taga fuskarshi Muryarshi tamkar zai fashe da kuka Yace"am really sorry my Angel, nayi laifi ay min afwa, nasan ban kyauta maki ba, amma dan Allah ki fahimce ni, ki nutsu ki saurari me zan fada maki.." kafin ya kare maganar ta katse shi da cewa"ni bazan saurari komai ba daddy, kawai ka daina sona ne ba ka damu dani ba, kuma ba ka yi kewata ba shiyasa kake 6oye min fuskarka..." ta fada tana jan majina kafin taci gaba da cewa"Daddy, what did I do to deserve this punishment from you? Daddy kasan kuwa irin kalubalan rayuwar dana fuskan ta? Daddy duk halin da na shiga ban ta6a mantawa dakai ba, bana kwana batare da na sanya ka acikin addu'ata ba, kullum zullumina ya rayuwar daddyna ta are? Meya faru da shi bayan Ya jefa ni cikin ruwa, Ya rayu ko ya mutu.... " Ba ta kare maganar ba saboda kukan daya ciyota, ta kuma fashewa da wani kuka tamkar ana zare ranta, abunne Ya tsaya mata aranta ya 6ata mata rai duk irin kewansa da tayi amma shine ya boye mata kansa. Gaba aya hankulansu Sajeed Ya koma kan fuskar tajuddeen, kalaman Angel ne suka fahimtar da su wanene shi Muryar na rawa Azeeza tace"dama kai ne daddyn Angel wanda kullum take bamu labarin shi"? Da sauri Parveen tace"idan bazan manta ba, duk in muka zauna fira unaisah saita bamu labarinka, itace tafara sanya mana kwa ayin ganin ka, da zumudin son muje gidan su don muyi rayuwar an ci, har fada mana takeyi daddyn ta zai kar6emu kamar ya'yansa..... Kasa karasa maganar tayi nan take ta fashe da kuka. Cikin karyayyar murya Batool tace"ashe kai ne daddyn Angel, Ni burin da nake dashi idan Allah yasa na ha uwa dakai shine inyi maka godiya saboda Angel ta fa a min kaine ka ilmantar da ita, ka tsaya mata tsayin daka har ta samu ilmin addinin da take da shi, uwa uba kaine silar da Angel tazo duniya...." tana magana hawaye na wanke fuskarta. "Wallahi ba mu ta6a sanin wanene mahaliccin mu ba, sai a sanadin zuwan Angel GIDAN KURKUKUN ADDARA, , In da mu ka yi rayuwar kulle, cikin duhun jahil ci, harta toilet atare muke shiga da an uwanmu maza Angel itace ta tsawatar mana ta fada mana cewa babu kyau mu daina haramunne wani yaga tsiraicin wani......" kuka ne ya kubce ma batool, ummi dake sauraransu a matu ar ru e take an zare idanunta akan fuskokinsu, gaba aya sun jefa ta a cikin ru ani lamarin yayi mu ar girgiza ta, tayi matukar razana. Bata gama shan mamaki ba cikin sanyin murya haris Yace"Allah ne kadai zai iya biyanka daddy, zuwan Angel cikin rayuwarmu tamkar baiyanar haske ne a cikin duhu, wallahi baki bazai iya furta irin wahalar da unaisah tayi akanmu ba, duk da kasancewar ta arama a cikin mu amma tana da kaifin basira kuma tana da hankali, Angel ta zama jigo na rayuwarmu, ta share mana hawayenmu a lokacin da muke kukan radadin kuncin rayuwar da muke aciki, Angel uwace agare mu, saboda ta kwatar mana ancin mu da aka tauye mana......" zu6ewa haris yayi kan gwiwowinsa hawaye naci gaba da sintiri kan fuskarsa, Gaba aya sun gama kashe ma tajuddeen jikinsa, yayi sanyi la was zuciyarsa ta karaya, wasu irin zafafan hawayene masu umi suka soma wanko fuskarshi yayin da yake kallonsu aya bayan daya, yana mai jin tsantsar tausayin su da kaunarsu azuciyarshi, Angel ta gama masa komai a duniyar nan baisan ma ina zai tsoma kanshi ba tsabar yadda Yake jin mahaukacin sonta na kara nunkuwa acikin zuciyarshi, ba zai iya misalta irin alfarin da ya ke da ita, burin kowani ubane ya sami a kamar Angel wadda zata kare masa martabarsa da kimarsa a idon duniya, wadda zata daukaka darajarsa ta kuma yi silar shigar shi aljanna, hannu aya ya daura akanshi Yana cigaba da kallon su jikin shi har kerna kerma ya ke yi. Duk wannan abun dake faru a kunnan chief owais da Big guy wadanda basu jima da zuwa bakin kofar dakin ba, sunzo zo ne don su duba jikin Unaisah sai kuma suka ji abunda ba suyi tsammani ba wannan dalilin ne yasa suka dakata suna sauraron su Cikin shesshe ar kuka Naufal Yace"daddy duk yadda zamuyi maka bayani ba lallai ka fahimce mu, amma wallahi muna kaunarka muna son ka daddyn Angel" wasu hawayen nan suka kuma wanke fuskar taj, idanunshi sunyi jawur da su gaba aya ya rasa bakin magana sai dai kallonsu da yake tayi gwanin ban tausayi "Unaisah itace take arfafa mana gwiwa, itace komai namu, itace muke gani muji dadi, unaisah ko mun 6ata mata rai bata yin fushi damu ba, sai ma taja mu ajikinta saboda tasan bayin kan mu bane, rayuwa mu ke a cikin duhun jahilci, ....." gaba aya suka dubi batool da ta dauko maganar hawaye na sintiri kan kuncinta, dakatawa tayi da yin maganar
Chapter 42 · 0% Book details