Sashe 60
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
~Takun arshe Dedicated to Aunty Kubra An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists Daga al alamin Boss Bature _AUNTY XEE Thank you for being there for me. Your support has been a lifeline. __________________________E20 Tashin hankalin da ba'a saka masa rana!, Idanunshi azazzare Yake duban su, jikinshi ya soma kakarwa, tsabar ki ima zuciyarshi tamkar zata fasa irjinshi saboda bugun da takeyi masa, bakomai ne yafi aga masa hankali ya zautar dashi ba face kalmar zasu kwanta da gawawwakinsu, Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un wannan wace irin musiba ce? Cikin karyayyar murya yace"Ni yakamata ku hukunta saboda ni nayi maku laifi, na ro e ku ko dan sanayyar dake a tsakanina daku....." Wata irin mahaukaciyar dariya suka tuntsire da ita jikinsu har jijjiga yakeyi kamar ana bugun ganguna, wani daga cikinsu ne ya kuma cewa"Ba sani, ba sabo a tsaka nin mu, saboda ka tabka babban kuskure salsabeel ka yi ha'inci, don haka dole ka fuskanci hukunci mai tsanani daga gare mu" Sunan Allah Ya ci gaba da ambato acikin zuciyarshi, duk addu'ar da tazo mashi yinta yakeyi ba autawa, har jaraba Yin amfani da sihirin shi yayi don ya ku6utar da kanshi da kuma Gawawwakin amma abun yaci tura, arfin sihirin shi bai kai na su ba, sun riga da sun yi mashi mugun auri na sihiri ba zai iya ta6uka komai ba. Ja da baya ya soma yi ganin suna tunkaro shi, cikin matsanancin tashin hankali, kafin ya urema bangon akin tuni aya daga cikinsu yai zazzafan taku ya dam i wuyan salsabeel da kafcecen hannun shi, nan take numfashinsa ya soma arin aukewa, aga shi yai sama tun Yana kiciniyar wace kanshi harya fara gazawa idanunsa sun ka a jawur sun fiffito waje, nan take ya soma bleeding ta baki ta hanci, wani irin ra in azaba ne Ya ziyarci salsabeel tamkar ana yi mashi askanan wuta a jikin shi, fuskarsa tayi jawur jini ya kwanta a fatarsa, hawaye da gudu suke kwararowa ta cikin idanunsa bakomai zuciyarshi ke tariyo mashi ba A lokacin face kalaman mahaifiyarsa Tamira, Idanunsa na akan gawarta.... Numfashinsa na kiciniyar aukewa gaba aya ya gama jigata har ya fidda rai da rayuwa, a lokacin da basuyi tsammani ba suka jiyo sautin dirar wani abu a bayansu, da sauri giant in daya sha e wuyan salsabeel ya sake shi jiki ba wari ya kife asa kan shi Ya daki asa da yar numfashin sa ke fita da hucin zafi, kusan atare Giants in suka juya baya don ganin menene Ya fa o cikin akin da har Ya bada sautin mai kuwar gaske. Da wani irin tsantsar Al'ajabi suke kallon shi, yadda kasan saukar aradu Haka Ya fa o masu Yana huci kamar Mayunwacin Zaki, kwata kwata babu riga a jikin shi sai dogon wandon kakin Giant, jikin shi sai tsuma ya ke yi tsabar fusata, ta ko'ina zufar 6acin rai ce ta ke tsastsafo masa, harta tsokokin jikinsa motsi su ke yi, da wani irin hucin zafi numfashin sa ke fita. Shin Wanene Wannan? To bakowa bane face GARKUWA, dalilin dayasa shi dawowa kurkukun saboda hankalin shi ya i kwanciya yasan mawuyacin abu ne Salsabeel ya samu fita daga cikin kurkukun tare da gawawwakin salin alin, ranshi na bashi cewar wani mugun abun zai iya faruwa da Salsabeel in, shiyasa lokacin da su ka shiga cikin makewayin bayan ya bu e ma su Angel kofa ya i bin su yace su fara yin gaba shi zai taho da Akwatin kayan su tare da back pack in su, za su tarar dashi a bakin ofar da zasu 6ulla idan sun arasa, yayi hakanne don ya samu damar dawowa ya taimaki rayuwar salsabeel saboda baya son ya rasa shi ko dan saboda halaccin da ya yi mashi a rayuwa bazai ta6a mantawa ba, yaji mutuwar tsohuwa Tamira don haka bazai bari rayuwar salsabeel ta salwanta ba Kallon kallo su ka soma jefawa junan su tsakanin Giants da Garkuwa, wato gaba da gabanta, Aljani Ya taka wuta, banbancin Danish da sauran Giants shi arfin sa Na Evil giants ne masu Star Uku kai ko a cikin su Ya zarce su Power, babban kuskuran da Elders sukayi shine dam a amanarsu gare shi saboda ya zama garkuwarsu a duk lokacin da za'a kawo masu hari, ba su ta6a tsammanin garkuwarsu zai Iya cin amanarsu ba, shiyasa suka bashi sihirin da ya fi na kowani giant na gidan kurkukun addara, a halin yanzu babu mai iya karawa da shi sai Elders wato Leaders in su, Danish Yana da kwatankwacin arfin giants ari a jikin shi, ba en shai anun dake a jikin shi wani irin arfi ne da su na fitar shari'a, kuma basa ji basa gani umarnin shi ka ai suke bi, hatta su kansu elders ba su isa su hana shai anun bin umarninsa ba, kuma su sukayi kuskuren aurashi akan turbar da yake ashe da rabon su yi danasani mai girman gaske, Duk da Salsabeel baya acikin hayyacinshi Hankalin shi ba aramin tashi yai ba, ganin Danish Ya dawo! Muryarshi na rawa ya furta "meyasa! Meyasa Danish? Meyasa ka dawo? Ina ka baro su Angel? Sautin muryarshi ko fita batayi shi ka ai yake sambatun shi ba tare daya iya agowa da kan shi ba, saboda raunatar da yayi. aya daga cikin giant dinne Ya ambaci sunan shi"Garkuwarmu"! Yana huci Yace"Ni ba garkuwarku bane! Garkuwar su ne! idan har kuna son zama lafiya to ku yale salsabeel da gawawwakin nan, Idan ba haka ba, zanyi maku abun da baku ta6a tsammani ba"! da kakkausar murya ta majiyi arfi ya fa a yana nunasu da yatsan hannun shi. A lokacin kusan suman tsaye sukayi saboda mamakin kalaman shi! ha a yayi matu aure ma su kai sun firgita da jin furucin sa. "Amma dai wasa kake mana ko"? Girgiza kai yayi "na ta6a yi maku wasa makamancin wannan!? "Idan kuwa har dagaske ne, Elders sunyi kuskuren yarda dakai maci amana! Ka bamu mamaki! Ina ka samu warin gwiwar da har ka Iya gaya mana magana a gaban idon mu ba tare da jin shakkarmu ba?" Shiru yayi baice masu komai ba. "Tun wuri ka yi gaggawar Janye udurinka, Saboda kai namune baka isa ka juya mana baya ba, har abada kai mallakin gidan kurkukun addara ne, kuma garkuwarmu, Idanma mafarki ka ke yi to ka farka tunkafin lokaci Ya ure maka, duk wani abu da zakai ta ama dashi anan ka same shi, kuma da zarar elders sunji maganar nan, kasan me zai biyo baya......" wanda yayi maganar Ya fa a yana mai yi mashi kashedi. "Har abada ba zanyi danasanin bijiremaku ba, Shawarar da zan baku shine kuyi gaggawar barin wurin nan idan kunaso ku tsira da rayukanku saboda ni banzo da niyyar na cutar da wani ba, an uwana kawai nakeso na ku6utar daga sharrin ku." Babu yadda Danish bai yi da su ba akan subar salsabeel amma suka sanya kafiya, dama su giants basu da tsoro kuma basa karaya sai dai komai zai faru ya faru, Kafin kace me fa a ya kaure tsakaninsu tamkar a filin Ya i, tuni ura da kururuwa sun kara e cikin da in, bakajin komai sai gurnaninsu mai matu ar firgitarwa, gaba aya sun riki a sun koma dodanni masu ban tsoro sai kaima juna farmaki su ke yi kamar abokan gaba, Kakin Giant in dake jikinsu Ya faffasa saboda garkuwa ne agare su, idan har ba ciresu yayi ba to bazai iya yin galaba akan su ba balle har Ya yi nasarar kashe su, wani irin bahagon naushi ya soma sakar masu akan idanuwansu duk wanda ya nausa nan take wayar idanuwansa ke zazzagowa cikin Jini Ta fa asa, gaba aya Ya zautar dasu Ya naka a masu lugudan wahala, Har saida numfashinsu Yabar gangar jikinsu tukunna Ya zu unna Yana huci batare daya canza halittarsa ta mutane ba Yabi su aya bayan aya ya farke irjin kowannan su ya 6an6aro zuciyoyin su Ya tura abaki Yana ci saboda Ya ara arfin sihirin shi. akyar Salsabeel Ya samu warin gwiwar mi ewa numfashinshi na fita sama sama, muryarsa da rauni Yace "Danish meyasa ka baro su Unaisah Ka dawo don ka taimaki rayuwata, Idan wani abu ya same su fa"? Danish bai tanka mashi ba, har Sai da Ya gama abunda Yakeyi tukunna Ya girgiza jikinshi ya riki a ya dawo ainihin suffarshi ta mutane. Ruko hannun salsabeel yayi acikin nashi yana faman fitar da huci Yace"Saboda rayuwarka tana da mahimmanci, bazan bari na rasa ka ba, nasan cewa zasu iya farmakar ka shiyasa na dawo don na ceci rayuwarka, Inaso na cika maka burinka na ganin ka binne gawarwakin su tsohuwa tamira sannan in ku6utar da kai. Girgiza kai Salsabeel yayi hawaye cike fal da idanunsa yace"Danish ka tafi kawai, Zasu Iya riskarka, wallahi ba zasu yale ka ba, ni kuma bazanso ka ara shan wahala arayuwarka ba, Yanzu lokaci ne da yakamata kayi rayuwar yanci Danish, inaso kayi farin ciki kafin kabar duniya, Hakkin ka da aka tauye maka na rayuwa shi nakeso ka samu Danish dan Allah ka tafi, kabarni kawai, ka koma wurin su Unaisah ni basai na rayu ba, rayuwarku tafi mahimmanci agareni nasan zaku ha a gwiwa don ganin kun kawo arshen elders...." magiya ya dinga yi masa akan ya tafi ya yale shi amma ya iya har saida ta kaiga Ya daka mashi tsawa a fa ace Yace"Ka tafi ka yaleni!! nace maka ka tafi! ka tafi !kabarni kawai..." Cikin sanyin murya Danish yake fa in "bazan tafi ba salsabeel, Idan kaga na bar wurin nan to na kubutar da kai ne..." Gaba aya sun Harzu a, fa a ne ya kaure atsakanin su kamar zasu bugi juna, kwatsam a lokacin da basuyi tsammani ba, sautin tarin Deeja Ya cika kunnuwansu, kamar an dasa masu aya suka dakata dayin sa'in sar da suke yi, kusan atare suka kai idanunsu ga duban inda take a kwance da tsantsar al'ajabi, babu wanda yayi zaton akwai me rai acikinsu, da sauri Danish Ya nufe ta Yana dubanta, idanunta a runtse take sambatu cikin fitar hayyaci take ambaton sunan haris da Angel tana fa in "ku taimaki rayuwata kuna ganin za'a cutar dani........" kallon juna sukayi shida salsabeel, kafin Ya mayar