Sashe 180
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
can zaune falo sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, Ni nasan bai wuci zancen tafiyarku bane Ya aga hankalin su..." ta fada fuskarta ayamutse. Muryarshi da damuwa ya furta"Ya sallam, Ummi pls ki yi ko arin kwantar masu da hankalin su" "Wallahi ba irin lallashin da banyi masu ba, amma duk abanza" "Ummi, ki zauna dasu, yanzu zamu shigo gidan In sha Allah" "Okay, Allah ya dawo daku lafiya" "Ameen" da ga haka Su ka yi sallama. Saukowa down tayi, har ta shigo falon ba su ankara ba. Sau uku tanayi masu sallama babu wanda Ya amsa mata saboda Hankalinsu baya atare da su. Binsu da kallo ta yi, daga wanda ya age kai sama, Sai wanda Ya langwa6ar da kan shi jikin Sofa, kowa dai da alkibilarsa da ya kalla Bakowane Yafi bata tausayi ba, face Unaisah, baiwar Allah ita kadai ce kwance Kan rug, yadda kasan tsumma, ta nanna e guri guda kamar kifin gwangwani ko motsi batasan yi. Kware murya tayi da karfi ta furta"wai bakwa ji nane"? A firgice suka zabura kowannan su Ya gyara zaman shi, kusan atare suka dube ta, In ka cire Unaisah wanda ko gizau batay ba, tana nan yadda take a kwance.. "Aunty ummi har kin bamu tsoro," hanna ce tay maganar. Haris Yace"wai har yanzu basu dawo ba"? "Aunty ummi, ko zaki kira mana su? Mun yi ma Unaisah magana tace wai batasan inda ta jefa wayar ta ba, kuma mun duba bamu ganta ba" acewar Batool.. Naufal yace"pls Aunty Ummi, nasan ba zaki rasa sanin ranar da zasu tafi ba, dan Allah ki fa a mana wlh munyi maki alkawarin ba zamu fa a masu mun sani ba" Bata tanka masu ba, wuri ta samu kan Sofa ta zauna, batare data kauda ido daga kallon su ba. Calmly tace"yanzu nayi waya da boss, Yace min suna akan hanyar su ta dawowa gida.." "Aunty ummi duk ba wannan ba, kawai ki fada mana ranar da zasu tafi, in ba haka ba hankalin mu bazai kwanta ba" acewar Naufal. "ku yarda dani, wlh nima bansan date din da zasu tafi ba, har tambayar boss nayi yace min basu fidda rana ba, kunsan yanayin aikinsu na jami'in sirri, kuskure kadai zai iya lalalata shirin su, yakamata mu fahimce su ko" ta fada cikin kulawa tana kallon su. Sarah tace"amma ay ba laifi bane in mun sani, zamu tayasu da addu'a ne kawai," Murmushi ummi ta anyi"in zaku tayasu da addu'a ay ba dole sai kun san ranar da zasu tafi ba, wannan baya daga cikin sharuddan yin addu'a" "Look aunty ummi, kin san komai, kawai kina boye mana ne" fuska a daure Sajeed Ya fa Yar dariya tayi"dama nasan zaiyi wuya ku yarda dani, in ma baku yarda ba toh kada Allah yasa ku yarda" ta fada tare da yi masu dakuwa da hannunta, tuntsirewa su Ka yi da dariya itama dariyar tayi "Kun fiye taurin kai Allah, haba mana, kusan karfe tara, Yakamata kuje ku kwanta, ga little sisters dinku nan sai gyangyadin bacci sukeyi nasan saboda ku yasa suka ki zuwa su kwanta bacci" ta fada tana nuna Azeeza da jemimah da hannunta sun manne ma juna sai gyangyadi su ke yi.. "Hmm aunty ummi kenan, Salon muje mu kwanta bacci, lokacin da zamu farka ace mana sun tafi ko? Da fa wayon mu" dariya tayi sosai maganar javed ta sanyata nishadi. Mikewa tayi ta nufi sofa din da su jemimah suke a zaune, ta dauki jemimah ta goya abayanta, kafin ta tada Azeeza tana layi ta mike kamar wadda tasha kwaya.. Ruko hannunta tayi, ta nufo bedroom dinsu dasu, sai da ta tabbatar sun kwanta bacci ta kashe masu switch din dakin tana kokarin fitowa unexpectedly Jiniyar motocin dake shigowa gidan ta kara e kunnuwan su. Kusan atare suka mimmi e tsaye suna jiran shugowar su, Unaisah ce ka ai bata motsa ba tana nan inda take akwance.. Cikin takun sauri suka fara shigowa falon, Chief ne agaba hannun shi ru e dana Danish daga bayan su Shiekah Imam Malik ne, Yayin da Boss da big guy hada ma Salsabeel su ke abiye dasu, mutun biyune babu kaki a jikin su, Danish da Salsabeel, black jean da white shirts ne a jikin su kala aya. Tun da Ummi taji Sallamar shiekh Imam malik, ta kasa fitowa daga dakin su Jemimah.. Kusan atare suka ci burki suna kallon su, sun yi mamakin ganin su a tsaitsaye curko curko suna ganin Danish jikinsu har 6ari yake garin saurin su karasa gare shi, daya bayan daya saida yayi huggin din su duk da agajiye yake har wani jiri jiri yake gani acikin idanun shi.. Atare suka hada baki gurin yi masu sannu da dawowa, kafin suka gaishe da shikeh imam malik cikin girmamawa.. "Sheikh, mun jima bamu ganka ba, kamanta damu" sajeed ne yai magana Tattausan murmushi shiekh imam Ya sakar masu"masha Allah na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya, Yan jikokina, ban manta daku ba, kuna araina, duk in zanyi addu'a saina sanyaku a ciki" murmushin farin ciki suka saki.. Gaba daya hankalin Taj baya akansu, Yar shi Yake nema Yaga babu ita a cikin su, baisan awani hali take ciki ba, ya yi kewarta ba kadan ba.. "Bismillah, mu shiga ciki" big guy ne ya fada tare da nuna masu hanya Kafin su karaso, da sauri Unaisah ta mike cike da rashin kwarin jiki ta zauna. Bayan sun karaso cikin falon Prisoners gaba daya suka zauna kan rug, su Chief suka zauna kan sofas din. Kwata kwata basu lura da ita ba, ganin daddynta ya mi e yana kokarin nufar dakinsu yasa tay karfin halin furta"sannu ku da dawowa, ya gajiyar aiki" atare suka dago suna kallon ta, haduwar idanunsu Cikin na jina yasa Danish yin saurin kawar da fuskarshi gefe daya saboda kallonta da yakeyi ba karamin karya mashi zuciya yakeyi ba, hakan da yayi ya sanyata jin wani iri a azuciyarta, gani take kamar fushi yake da ita.. "Unaisah Lafiyarki kuwa? Meke damunki"? Taj ne ya tambaya yana kallon ta.. Murmushi ta kakaro kan fuskarta"bakomai daddy, idan ma akwai abinda ke damuna, bai wuci zullumi da fargaban tafiyar ku bane" Jiki asanyaye Taj ya zauna gefenta, tare da ruko hannayenta acikin nashi. Hankalin Chief gaba daya yana akansu, shi kanshi Ta bashi tausayi ya lura da ramawar da tayi. "Pls ku bamu aron hankalin ku nan" big guy ne yai maganar, gaba daga suka dube shi, a lokacin Unaisah ta kwantar da kanta saman kafadar daddynta.. "Ina Auntyn naku take"? "Taje ta kwantarsu da su jemimah dakin su, har yanzu bata fito ba" "Okay, wani ya kira mana ita" Har mubeen Ya mi e zaije kiranta, sai gata ta fito komawa yai ya zauna.. Tana karasowa, cikin sanyin murya tayi masu bangajiyar aiki, kafin ta dubi sheikah Imam malik kallon juna sukayi ido cikin ido daga gani sunyi kewar ganin junansu Muryarta na dan rawa ta furta"ina wuni sheikh ya fama da jama'a.." tamkar bazai amsa mata ba, ya furta Lafiya..daga haka Ya kau da idanun shi gefe aya. "Bismillah, Ki zauna" big guy ne ya fada tare da nuna mata sofa, bayan ta zauna falon yayi tsit baka jin motsin komai kamar mutuwa ta gifta. Gyaran murya sheikh Imam Yayi tare da duban Chief yace"Owais, meke faru ne? naga kamar wani abu na damunku, daga ku har yaran babu mai walwala, ince dai ko lafiya"? Jinjina mashi kai chief yayi"kada ka damu, babu wani abu." ya fada tare da kallon Omar batare daya furta mashi komai ba, da ido ya fahimci me chief yake nu fi.. A tsanake ya fara labarta ma Sheikh Imam, dangane da shirye shiryen da suke yi nakai farmaki, sai dai ba komai ya fa a masa ba, ya dai ce mashi miyagun yan'ta'addane kuma matsafa ne masu hadarin gaske zasu je kaima farmakin a kurmin daji.. Sheikh Imam Malik Ya jinjina lamarin, tun da big guy ya fara zayyana mashi, Yake ta dan jinjina kan shi alamar ya girgiza da jin zancen. Chief Owais Ya daura da cewa"baba, alfarmar da muke nema agurinku, munaso ku ha a kai da manyan malamanmu na addini don ku yi mana addu'o'i, sannan zamu bada abun sadaka abawa mabukata da marayu suma su taya mu da addu'a." Numfasawa sheikh Imam yayi fuskar shi dauke da matsananciyar damuwa yace"Owais, Kunyi tunani mai kyau, tabbas tunkarar miyagun matsafa ba abune mai sauki ba, mutanene masu ha arin gaske, amma ta inda kuka fi su ku kun dogarane ga Allah ne, kuma kun yi imanin shi ne zai baku nasara akan su..." ya fada yana an jinjina kanshi "In sha Allah Owais, tun da har kuka nemi mu taya ku da addu'a zamuyi aiki tukuru, bi'iznillahi ba zasu ta6a cin galaba akan ku ba, saboda kyakkyawar niyar da kuke da ita na ganin kun kawar da masu aikata fasadi adoron kasa.." gaba daya sunji dadin furucin sheikh Imam malik "Zan iya sanin yaushe ne zakuyi tafiyar"? prisoners duk sun baza kunne suna jiran jin amsar da chief zai ba shi. "bamu fidda rana ba, amma a kowani lokaci zamu iya tafiya" "Okay, in sha Allah zuwa gobe da safe zan sanarwa yan uwana malamai yan team dinmu wadanda nayi imanin in har muka hada kai da su gurin yi maku addu'a babu wani mahalukin daya Isa Ya ci galaba akan ku, Sihirinsu bazai ta6a tasihiri a kanku ba, in ba wani iko na Allah ba....." Gaba aya sunji dadi maganar shiekh Malik, "Amma, malam, Danish har yanzu bai musulunta ba" gaba daya suka maida hankali akanta, sunnar da kanta kasa tay, ganin irin kallon da daddynta yayi mata. A hankali suka maida duban su ga Danish, wanda ya dafe goshinsa da tafin hannun shi Salsabeel Yace"kamar kin shiga zuciyata Unaisah, wlh tun dazu nake ta zucci zuccin inyi mashi maganar shi, gaba daya mun damu da rashin addininsa" Chief yace"nima abun na damuna, ataimaka mana sheikh, a karkato mana da hankalin shi Ya kar6i shahada, kafin lokacin da zamu tafi" Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, babu wanda baiyi magana ba, akan damuwar su na rashin addinin Danish In ka cire Big guy ko kadan bai sanya baki a maganar ba. "Danish, Har yanzu baka da ra'ayin kar6ar