← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 189 OF 247

Sashe 189

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

in namanta ya gama zagwanyewa. A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Ya i kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin akinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ara tashi ganin har dare yayi _______ BLACK NIGHT _______ arfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun addara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun addara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya kara e ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda ki an ke tashi.. takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya addamar da gidan kurkukun addara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna okinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ara arfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu le a muga meke wakana adaren Black Night aya bayan aya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ure kuri adakansa, arshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne. Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na asar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban san o dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye. A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu aton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da ba i a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai yami in ya kallesu sau aya bazai sake marmarin kallon su ba. Tawagar matsafan kurkukun addara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu ba e har asa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar warangwal. Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini. Gaba ayansu sun hallara a tsakar kurkukun, wansu da watar su ko'ina ka kalla sune birjik. Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun sa o da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya arfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su. Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka da e suna she e ayar su. Surutunsu Ya kara e ko'ina, da wani irin Yare mara da in Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nisha Daga kan ground floor in gurin wani ha en red carpet ne aka shimfi a tun daga fadar mai girma Elder har zuwa arshen bango inda aka awata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an awatasu da kayan ado. Daga can gefe aya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne auke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu ha arin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table in, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman awisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan ma walashe. Yayin da maka an suke ta yan ki e-ki e da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe ha ora suna kallon su.. Gaba aya sun agara a fara shagalin, fitowar Elders ka ai suke Jira.. Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba ayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ari. Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya fa a yana bin su da kallo.. "Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin ga ar makaho bace, ananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sau i ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su etare ba, mune masu arfin iko, da izinin mu komai ke wakana, in muka so Da kalma aya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!" Gaba aya suka tuntsire da dariyar sha iyanci, bayan sun tsagaita da yin dariyar Elder Ya dubi wanda yayi maganar Jan Le6e, "Na ji da in bayanin ka.." Ya fa a tare da maida dubanshi kan Elder din dake zaune gefen Jan Le6e ya ce, "Mutumina Jan wuya, Ko akwai labari? Ko kuwa sai mun sha mun bugu don nasan halinka da miskilanci kafi sakin baki idan ka hau kan network..." Cike da sha iyanci ya furta, "Musamman in akwai mata da giya anan linzamina yake kwancewa..." Dariya suka saka gaba aya.... "Baka da matsala mutumina, yau ranarmu ce, saika za6a ka darje," asaitacciyar dariya jan wuyan ya saki. "Jan kunne na ji ka yi shiru baka ce komai ba"? Ya fa a Yana duban shi. Muskutawa ya yi ya gyara zaman shi, "Elder, Ni bani da abun cewa, Hankalina Ba a kwance Yake ba, ban ta6a tsintar kaina a yanayi na jin fa uwar gaba irin na yau ba..." gaba aya suka maida hankali kan shi. Da kakkausar Murya wani mai zafin rai a cikinsu wanda suke kira jan harshe Ya ce, "Wannan wani irin zancen banza ne? Ka kuwa san me hakan Yake nufi? Fa uwar Gaban Elder yana nufin mummunar addara zata Iya afka mana, tun wuri Ka dakatar da zuciyarka, ba'asan Elder da raunin zuciya ba..." Yana are maganar Jan Wuya Ya ce, "Ka gafarce ni, kaima kayi kuskure a maganarka Jan harshe, Elders sunfi arfin mummunar addara, ita kanta addarar tsoron mu take ji, shiyasa bata ta6a gigin afka mana ba..." Da gadara suke magana. (Duniya budurwar wawa, Wanda Ya 6ace Ya 6ace.....) "Jan wuya, kai in na dabanne, namijin duniya, wanda bai ta6a karaya ba, ina son warin gwiwarka mutumina..." Ya fa a tare da yi masa alamar jinjina da babban yatsansa, kafin Ya dubi Jan Kunne "Kai kuma, kada na kuskura na ara jin ka ambaci fa uwar gaba, nasan me ke damunka, da zarar kaga mata masu manyan mazaunai zaka wartsake..." Dariya suka saka gaba ayan su. Kafin wani ya ara furta kalma a cikinsu, Evil Giants masu irar samudawa har su Goma suka kewaye kofar shiga Fadar... aya cikinsu mai wata irin atuwar murya ne Ya ce, "Elders ba i sun hallara, lokacin shagali ya yi, zamu iya tafiya..." jinjina kai Elder yayi tare da mi ewa suma sauran Elders din suka Mi e cikin takun dattako suke tafiya akan jan carpet din da aka shimfi a masu, hannuwan su ru e da sandunan su na alfarma. Lokacin da suka 6ullo ta ground floor in maka an dake ki a suka ara kaimi gurin buga gangunan kamar zasu fasa su, ga wata dadda ar busar sarewa dake tashi, wani irin kirari suka fara yi masu suna kurantasu da hura masu kai har wani rausayawa suke yi alamar kirarin yana kai masu karo. Gaba aya Hankulan matsafan Ya dawo kan Elders, Taurari masu haskaka duniyar matsafa, kowa burinsa ya ga Elders, musamman sababbin matsafan da basu jima da shiga harkar ba, saboda wani irin farin jini ne da su, sun shahara a fadin duniya. Cikin girmamawa matsafan suke mi o gaisuwa kamar zasu dur usa masu saboda biyayya....bayan Sun arasa gurin da aka awata masu, kowan nan su ya zauna kan armchairs in da aka tanadar masu. aga hannu Elder ya yi cikin sauri masu buga gangar da masu raye rayen suka dakata ... Duk fa in girman gurin idan ya yi magana sai kowa Yaji shi kuma a hankali yake yin ta cikin nutsuwa. "Ina yi ma kowa barka da zuwa, ha a bazan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba na ganin kowannanku, abun alfahari ne a gareni, ace wa annan dubban mutanan saboda ni suka baro muhallinsu suka zo don su taya ni murnar zagayowar ranar dana Kafa GIDAN KURKUKUN ADDARA....." Ya an dakata Yana bin matsafan da kallo tun daga kan hawa na Uku har izuwa na farko, sun kasa kunne suna sauraron shi.. "A daren yau, muna taya juna murnar nasarorin da muka samu, bamu ta6a fa uwa ba, dukkan abunda muka sa gaba sai mun cimma shi, ina fata abokan harkar mu zaku tayamu murna." Sowa suka sanya da arfi suke amsa mashi da, "Yeho! Yeho!! yehoo!! a kai ya yi kafin ya aura da cewa, "Kamar yadda kuka zo domin mu kuka faranta mana, muma zamu faranta maku, wannan yasa muka tanadar maku shirye shiryen da muka saba
Chapter 189 · 0% Book details