← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 130 OF 247

Sashe 130

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata le en asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...." Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba aya tabi ta ru Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi an adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....." Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"! hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika iya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya auko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma aga mata hankali, bata ta6a jin fa uwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita. Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa sukuni wani irin tsorone Ya kamata babban tashin hankalinta kada hajjaty tayi silar kassara rayuwarta kamar yadda ta kassara rayuwar marwa ya ilahi abin ya aga hankalin ta, ba ita ta runtsa ba adaren jiya har saida pravin ya dawo ya fara mata fa a akan rashin dawowarta da wuri, baiwar Allah saboda tsoro ta kasa mayar mashi da martani saima ta rungumeshi ta ame shi hakan ba karamin daure mashi kai yayi ba, yaja hannunta suka zauna gefen gadon ya tambayeta meke damunta cikin sanyin murya tace mashi bata jin dadin zuciyarta tsoro take ji saboda abun da ya faru da marwa shiyasa taki dawowa gidan.. murmushi pravin yasaki har cikin ranshi yaji dadin tsoratar da tayi saboda shi agurinshi damace ya samu da zai dinga juyata son ranshi, tun da ya gano lagwon ta, a daren ranar sai da ya biya bukatar shi da ita, son ranshi ta sakar mashi jiki yayi abunda yakeso dama ya kwana biyu bata bashi hakkin shi ba. Bayan ta dawo daga duniyar tunanin ta mi e tana zagaye akin tana tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin dole ta auki mataki! Ta tsani hajjaty fiye da yadda ta tsani mutuwarta __________________________________ Lokacin da Benazir ta farka daga bacci, da wata irin kasala ta bu e idanunta wadanda suka ka a jawur muryarta na rawa ta fara ambaton sunan Angel mikewa zaune tayi kan gadon, hannunta aya dafe dakanta, ga wata faduwar gaba da take ji "Babyna! Where are you? Mami Ina Angel dina? Bata nan ne? dakyar ta iya saukowa daga kan gadon tayi mi a ha i da yin hamma kafin ta fara baza ido tana neman Unaisah, ita kadai ce adakin, hajiya layla taje office din dr jazz domin amsa kiran da yayi mata. "Angel! Angel! Can't you hear me calling you? Where are you?" Da karfi tayi maganar tare da nufar kofar toilet ta kwankwasa"pls idan kina ciki, Ki amsa min babyna kinji..." ta fada tare da kanga kunnanta jikin kofar, shiru taji ba a amsa mata ba, da alama babu mutun aciki, hakan yasa tay pushing door din ta shiga ciki tana bin ko'ina da kallo kwata kwata bata ga kowa ba, ji tayi kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu, gaba aya tabi ta rude dama saida ranta ya bata cewar ba lallai ta ganta ba Fitowa tayi daga toilet din, ta nufi bed dinta, ta zukunna tana le en karkashin gadon don taga ko anan ta buya Adai dai lokaci hajiya layla ta shigo dakin hannun ta ruke da takardar sallama kaitsaye idonta suka sauka akan benazir. rass taji gabanta Ya fa i ganin yadda tabi ta ru e tana ambaton sunan babynta, tuni taji hawaye sun ciko idonta sam takasa karasa shiga ciki saboda fargaban amsar da zata ba benazir idan ta tambayeta Ina babynta, batasan ya zatayi da ita ba, ga tsananin tausayinta da take ji. "Mommy"! Muryar dr shurieim ce ta katse mata zancen zucin ta, a an firgice ta juya baya tana kallonsu, a jere suka nufo ta su uku ne, Shureim da Alhaji ubaid tare da hajiya sarah fuskokinsu dauke da murmushi, dakyar ta ha iye damuwarta ta nufe su tana fara'a suka rungume juna ita da hajiya sarah bayan sun raba jikinsu, shureim Ya matsa kusa da mommynsu Ya rungumeta tare da manna mata kiss gefen fuskarta. "Sannun ku da zuwa" hajiya sarah tace"ay min afwa wlh banji dadi ba, jiya banzo na duba jikin benazir ba, ban kuma kira naji ya kuke ba" murmushi hajiya layla tay"kai haba ba komai wlh, ay kinama kokarin zuwa dubata, wlh kada kiji komai benazir tana cikin koshin lafiya.." tai maganar tare da kallon Alhaji ubaid dake kallonta, harara ta an watsa mashi afakaice saboda taji haushin rashin kiransu da baiyi ba jiya, cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri jiya bana jin dadin jikina ne shiyasa ban kira ba, naso ma inzo dubaku" ta6e baki tayi"ay kwara da kukazo gaba ayanku, ga Benazir can tana neman yarta, kuma yarinya masu ita sun dauki abunsu, dama likita ne ya bada maganin bacci aka bata tasha kafin aka rabata da yarinyar yanzu gata can ta hargitsa dakin tana neman yarta" Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Dr shureim yace"baiwar Allah, na tausaya mata, wlh dama saida naji fargaban zuwan ranar nan, gashi sun shaku da yarinyar" Alhaji ubaid yace"yanzu ya zamuyi jama'a? ay ni nayi zaton ma zamu taras da su ashe har sun tafi, gaskiya banji dadi ba, ban ta6a haduwa da yarinyar ba balle inmata godiya ita da iyayenta da sukai mana halacci.." Hajiya layla tace"wannan duk mai saukine tunda aneelah tasan gidan iyayenta, wata rana saimuje muyi masu godiya, yanzu dai muji da maganar benazir! Menene mafita"! Hajiya sarah tace"ni nama rasa ta cewa wlh, amma ni aganina, abun da yakamata shine mu lalla6ata mu fada mata cewa daddyn yarinyar yazo ya dauke ta sun tafi mall, da anjima zai dawo da ita, saboda mu samu mu bar hospital in da ita, in ba haka ba dakyar zata amince ta bi mu" gaba daya sunyi amanna da maganar hajiya sarah, atare suka nufi dakin, suna shiga suka isketa zaune gefen gado duk ta yamutse gashin kanta kamar na mahaukaci, ga fuskarta sharkaf da ruwan hawaye. Atare suka hada baki gurin yi mata sallama, da sauri ta mi e tana kallonsu, muryarta na rawa ta furta"mami! Ya shureim! Daddy! aunty Sarah! Ina babyna? Tana ina? Na duba ko'ina banganta ba! Dan Allah ku fadamin waya daukar min babyna? Wlh in har ba'a dawo min da itaba, zuciyata zata buga in mutu kowa ya huta"! kusan atare suka ha iyi yawu kowa yasha jinin jikinshi, dakyar hajiya Sarah tayi karfin halin furta"haba Benazir? Meyasa zaki daga hankalinki akan yarki? Waya isa Ya rabaki da ita? Ki kwantar da hankalinki, Yarinyar nan takice halak malak.."bubbuga kafafunta tayi saika rantse da Allah batasan me take ba, bayan da hankalinta tsabar pretending ne "Ni kawai ku fadamin tana Ina? Meyasa banganta ba"? "Benazir, daddynta ne ya dauke ta, sunje mall zasuyi maki siyayya da anjima zai dawo da ita gida..." cike da fargaba hajiya layla tayi maganar, shiru tayi jimm na an wani lokaci kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya fuskarta ayamutse tace"mami dagaske Taj yazo nan? Shi ya dauki Angel dina"? Murmushi suka sakar mata, dr shureim yace"kwarai kuwa dagaske shiyazo ya dauketa.." "Amma bai tambayeni ba? Ko ya daina sona? Ta fada tana zare masu eyes dinta Alhaji ubaid yace"ya tambayeki mana, ay saboda ke sukaje yin siyayyar, yana son ya faranta miki rai.." wani irin tsallan murna ta daka tana dariya. kallon kallo su hajiya layla suka jefawa junansu hankalinsu atashe, wato akwai gwarama idan suka koma gida taji shiru taj baizo mata da yarta ba. "Mommy zamu jiraku a mota" dr shureim ya fada tare da kallon daddynsu atare suka fuce, Badajimawa ba, saiga su sun fito tare da benazir har ta canza kayan jikinta ta maida kayan da aka kawota asibitin da su, a backseat na motar dr shureim ta zauna, yana agaba tare da alhaji ubaid, Hajiya layla kuma a motar hajiya sarah ta zauna, a jere motocin suka fuce daga asibitin. Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily
Chapter 130 · 0% Book details