← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 46 OF 247

Sashe 46

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

Aneelerh tana agidan iyayenta, abun da ya faranta ranshi, Yaron da yaji ta haifa masu, tunkafin ma yaganshi Yaji Ya kamu da kaunarsa, kaunar da yake yima uzair gaba daya ta koma akan yaron da bai ta6a ganinsa ba......' acikin labarin da muhsin ya fada masa abu ayane bai sanar da shi ba, rasuwar iyayensa gudun kada zuciyarsa ta buga, kwara idan ya samu nutsuwa ya sanar dashi daga bisani. A daren ranar kafin muhsin yabar dakin taj, Sai da taj ya garga esa akan kada ya sanar ma wani cewa yagansa saboda rayuwarsa tana acikin hatsari, idan mutanan da suka kashe uzair suka san da zaman shi tabbas zasu cigaba da bibiyarsa har sai sunga bayan shi. Cikin sanyin murya muhsin yace in sha Allah babu wanda zaiji zancen dawowarshi, zai rufa masa asiri yaci gaba da zama a gidansa har zuwa lokacin da Allah zai kawo mashi mafita.... Tsawon wata guda suna agidan muhsin, a cikin kwanakin da yayi baya iya runtsawa saboda damuwar rashin angel, duk daren Allah Sai yayi nafilfili saboda angel dinsa, duk ya fita hayyacinsa sam baya da koshin lafiya ciwon kafarsa tamkar ana fama masa shi abu ya i ci ya i cinyewa, muhsin yaso ya bi shi suje asibiti a duba lafiyarshi gudun kada ya rasa ranshi amma yaki yarda saboda bayason wani yaga fuskarshi, ya wammace idan ma mutuwarce ta dauke shi agidan muhsin zaifi mashi sau i akan wadannan azzaluman mutanan su kona shi. A daren wata rana ne, Yana cikin Yin nafilfilin dare, Yajiyo dirar motoci a cikin gidan muhsin, A firgice Ya mike daga kan darduma Gabansa na faduwa, baisan su wanene sukazo gidan muhsin ba, a irin wannan lokacin karfe kusan sha biyu na dare, zuciyarsa na bugawa ya nufi falon gidan don ganin su wanene, Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, ganin matasan samari masu jini ajika suna shigowa kowannansu sanye cikin shiga ta bakake kaya sun rufe fuskokinsu da facemask. Bakomai ne ya tsoratar da shi ba face tunawa da wadannan body guards din da suka budewa alhazawannan motocinsu, nan take ranshi ya bashi cewar sune, hakan na nufin muhsin Yaci amanarshi, bayan yayi mashi alkawarin zai rufa masa asiri shine yabi ta bayan fage ya tona masa asiri, zuciyarshi ajagule ya furta meyasa zaiyi min haka! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankalin shi danejo kada suce zasu ha a da ita su kashe... A lokacin zuciyarshi ta riga ta gama hasala, Jininsa akan akaifarsa yake, tunkararsu yayi muryarshi a fadace yace"kun biyo ni nan dinma donku kashe ni? Laifin me nayi maku ne? Da aci aransa ya furta maganar, kamar daga sama yaji muryar muhsin daga bayan shi yana fadin"taj, ka tsaya zanyi maka bayani" a sukwane ya juya ya kalle shi a fusace yace"wani irin bayani zakayi min muhsin? haka mukayi dakai? ka cuce ni muhsin, ba zan ta6a yafe maka ba, yanzu dakai za'a hada baki don akashe ni"? Hawaye cike tab da idanunsa yayi maganar, fitowa danejo da matar mushin sukayi daga dakin duk suka tsaya suna kallon su.... Matasan da suka tsaya abakin kofar falon sun har e hannayensu akan kirjinshi suna kallon shi, babu alamun zasuyi magana.. "Taj bazan ta6a cin amanarka ba, abun da ya faru da kai ba kai ka ai ya shafa ba, hada ni kaina saboda ina jinka tamkar an uwana na, wa annan matasan da kake gani, ba su zo da niyar su cutar dakai ba, sai don su taimaki rayuwarka, Idan ka basu hadin kai in sha Allah zakuyi nasarar nemo Angel dinka data 6ata, bayan haka zasu tayaka daukar fansa akan mutanan da suka kashe uzair" "Har yanzu ban fahimci inda zancenka ya dosa ba .." murmushi muhsin yayi kafin yaci gaba da cewa"su in jami'an hukumar ISOD ne, nasan ba zaka rasa sanin CHIEF OWAIS ba, an gidan Sharafudeen Obinna......" wani irin al'ajabi ne ya kama tajudden muryarshi na rawa ya maimaita sunan Chief Owais da tsantsar mamaki yace"muhsin dagaske kake min ko wasa? Tayaya akai ma su kasan da zamana" Kafin muhsin Ya bashi amsar tambayarshi, Chief owais Ya shigo bakin shi dauke da sallama cikin shiga ta kakin isod, da sauri matasan nan suka buga kafa tare da sara mashi, muhsin kamar zaiyi mashi sujjada tsabar yadda yake washe baki yana yi mashi sannu da zuwa yalla6ai, shi dai taj ya gaza yarda da abunda idanunsa suke gane mashi, kai ko a mafarki bai ta6a tsammanin zai ha u da chief owais ba, mutumin da a tv kadai yake iya ganinsa, sai gashi yau a zahiri Allah Ya nuna masa shi. Cike da qasaita, Chief Ya nuna masa sofa alamar Ya zauna" jiki na 6ari taj yaje ya zauna yana ta faman bin shi da kallo a lokacin shima ya zauna kan sofa din dake fuskantar ta shi. Cikin harshen turanci yace"nasan zaiyi wuya ace baka sanni ba, amma duk da haka zan gabatar maka da kaina, da farko sunana owais sharafudeen Obinna, chief na hukumar Isod...." ya fa a tare da an dakatawa yana dubansa, tun anan taj ya fahimci ba karamin mutunne bane mai ji da kansa. "Malam taj, kamar yadda kake mamakin ganina nima haka nake mamakin kasantuwana acikin rayuwarka, ko a mafarki ban ta6a tsammanin akwai ranar da zan hana idona bacci saboda damuwa da mutumin da bansan wanene shi ba...." kalaman chief owais sun girgiza shi matu a, har dai ya gaza jure wa yace"dan Allah ka fadamin meyasa ka damu dani bayan baka sanni ba" da bu ar bakinsa sai cewa yai" arka ce sila" waro idanu waje taj yayi da tsantsar mamaki yake binsa da kallo fuskarsa da rudani yace"meyasa kace haka"? Numfasawa yayi kafin ya soma magana muryarshi tamkar ana busa sarewa saboda dadin sauraranta.... A washe garin ranar dana dawo Nigeria daga U.S anyi min wani kira da ya tsaya min araina.... Fitowa yayi daga cikin bathroom waist dinsa daure da towel, yayin da dayan hannunsa ke a ruke da wani short towel yana tsane sumar kanshi, a gaban dressing mirror ya tsaya da niyar ya gyara jikin shi, wayarsa dake akan nightstand ta soma ringing, dakatawa yayi da tsane sumar kan da yakeyi a hankali ya nufi wayar ya dauko ta yana duba number din da aka kirasa da ita, yayi mamakin ganin bakuwar number, A matsayin shi na jami'in sirri komai nasu asirrince suke yin shi, harta phone number dinsa special ce, bakowa yasan shi da ita ba, sai mutun yakai yake samun damar mallakar ta, bai yi niyar picking call din ba saboda a ka'idarsa baya aga bakuwar number, ko kiransa akayi indai ba family dinsa bane to baya picking sai anfara neman iznin yin magana da shi...... Amma a lokaci sai zuciyarsa ta kwallafa rai akan son sanin wanene ke kiransa... Baisan sa'adda Ya danna answer call ba, ko da yai picking ya kara phone din a kunnansa shiru yayi baice komai ba tsabar miskilancinsa jira yake yaji wani isasshen ne ya kira shi batare da iznin shi ba. Lamarin ya daure masa kai jin anyi shiru ba'ayi mashi magana ba, ko wanene wannan mai karfin halin? Har zaiyi rejecting call din sai kuma Ya fasa calmly ya furta "who is on the line"? Sautin muryar karamar yarinya yaji ta ratsa kunnansa "Angel ce," Yayi mamakin jin muryar karamar yarinya, aransa ya ayyana ko yar wacece ta kirasa, "kinsan dawa kike magana"? "a'a," ta bashi amsa atakaice "Ur age"? "7yrs" voice in shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'? "Daddyna ne, ya tafi masallaci ni ka ai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya" Murmushin gefen fuska yadan saki har dimple dinsa ya lotsa, don ya fahimci ba'asan ta dauki wayar ba, tun daga kan muryarta ya gane irin yaran nan ne masu tsiwa "Can i call u video"? Da sauri tace eh, Nan take ya mayar da kiran Video call, da sauri ya sanya yatsan hannunsa ya rufe front camera din wayar saboda baison taga fuskarshi, baisan ko tarko aka ana masa da ita ba, lokacin da fuskar Angel ta bayyana akan faskeken screen din wayarsa wani irin bugu zuciyarsa tayi, bai yi tsammanin zai ganta kyakkyawa ba, fara sol ga manyan idanu launin gray dara dara da su, gaba aya ya kasa kyafta idanunsa daka kallon fuskar ta, a sukwane ya koma gefen gadon shi ya zauna yana ci gaba da kallon ta... "I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale masa ido, murmushi yasaki yana kallon ananun la66anta tausasan gaske launin pink, chief Ya shagala da kallonta, tamkar a mafarki yake bin fuskarta da kallon urulla kamar zai ha iyeta, A can 6angaran Angel taji shiru ba'ayi mata magana ba, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, batasan cewa shine ya toshe front camera din wayarsa don kada tagansa, da sauri yayi screenshort din fuskarta ba tare da sanin ta ba... Zuciyarsa ba aramin sosuwa tayi ba, ganin tayi rejecting call din, sam bai gaji da kallonta ba, da wata irin kasala ya kwantar da kansa bisa pillow, Ya bude hotonta yaci gaba da kallon fuskarta.... Baiyi tunanin kiran layin ba, haka ya wuni da tunaninta aranshi, tsawon kwana uku baya iya bacci batare daya kalli hoton fuskarta ba, sometimes a rungume da wayarsa yake kwana, sai da takaiga harta daddynsa da mommynsa sunsan da hoton yarinyar daya kwallafa rai akai, mahafinsa ne Ya bashi shawarar Ya nemo ta idan hakan zai kwantar masa da hankalinsa, Ya ji dadin shawarar daddynsa, maimakon ya tuntu6i layin tajuddeen kaitsaye su yi magana da shi, sai ya fara bincike ta hanyar amfani da phone number din da Angel ta kira da shi, anan ya sami bayanan taj hada shafukansa na social media da yake amfani da su wurin ya a aikinsu na an jarida, cikin sa'a ya gano address din gidan radion da taj yake aiki, bai samu damar zuwa joss ba saboda kiran gaggawa da akayi masa tafiya ce ta kama shi zai bar kasar ba don yaso ba. Gaba aya ya tattara komai ya damka a hannun Big guy, wanda ya kasance aya daga cikin na hannun damansa, amintattunsa, Ya fada masa komai dangane da yarinyar data
Chapter 46 · 0% Book details