← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 57 OF 247

Sashe 57

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

kayanta su tafi, bin bayan ta Alhaji ubaid yayi kamar zai rufeta da bugu sai fa a yake yi mata, Ko kallo bata isheshi ba, trolley din kayanta ta auko Ta fara kwashe kayanta dake a cikin closet tana jerawa a akwatin. Dawowa dr shureim yayi a an rude yake kallon dining din ganin babu kowa, da sauri Ya nufi dakin Benazir Yana shiga ya sameta, zu unne gefen gadon ta tana kuka, ga trolley din kayanta da ta gama ha awa. a ru e ya furta Benazir? Lafiya? Meya faru naga hawaye akan fuskarki"? Jiki asanyaye ta mike tare da kallon shi, fuskarta tayi jawur da ita. "Yaya shureim bayan kaje amsa kira, mommy ta fara fa a akan ita bazata cigaba da zama gidan nan ba, shine tace min inzo in hada kayana mu tafi, ni kuma bana son tafiya saboda ban cimma burina ba, na ganin na ha u da Aneelerh...." Share mata hawayen ta ya somayi da hannayensa cikin sigar lallashi Yace"kiyi hakuri ki daina zubar da hawayen ki, bana so kina sanya damuwa aranki, amma ni kaina na goyi bayan ku tafi benazir! Ko dan saboda abunda ke faruwa dake agidan nan, Ina jin tsoron na rasa ki, kwata kwata hankalina bai kwanta da zamanki ba' "Yaya shureim idan na tafi tayaya zan ha u da Aneelerh"? Harya bu e baki zaiyi magana, kwatsam Wayarsa ta fara ringing, a hanzarce Ya duba sunan mai kiran nashi, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, arude benazir tace yaya shureim lafiya naga kana murmushi" "Alhamdulillah, Kiran da muke ta jira ne sai yau Allah Ya nufa zamu gana da su, kar6i kuyi magana, abban Aneelerh ne Yake Kiranki...." Yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin picking call din kamar zata zauce tsabar murna Muryarta da zumu i ta furta"Assalamu alaikum Abie Ina kwana...." Kafin ta are maganar unexpected Muryar Aneelerh ta ratsa kunnanta da wani sauti mai karfi ta furta"BENAZIR!! Mafarki nake ko gaske"? Fashewa da kuka benazir tayi jin muryar aminiyarta da kunnuwanta sukai maraicin ji na tsawon shekaru. Cikin shesshekar kuka tace"Wallahi nice Aneelerh, nice benazir din da kika sani..." Kafin ta are maganar, Itama Aneelerh ta fashe da matsanancin kuka tana fadin"Benazir baki kyauta ma kanki ba! Meyasa? Meyasa? Meyasa kika gudu na tsawon shekaru? Idan wani abu ke damunki ba zaki fa a mana ba? Kinsan irin kunci da radadin da muka ji bayan tafiyarki? Kin kama hanya kin gudu kin bar jinjira acikin kwamin wanka, Da ranki da lafiyarki baki ta6a kira kinji awani hali Yarki take a ciki ba, wai dan Allah meyasa kikayi haka benazir meyasa.....?" kasa arasa maganar tayi saboda kukan da ya sar e makoshin ta. Tsananin tausayin su ne Ya kama dr shureim, tun dazu yana atsaye yana kallon Banazir kuma yana sauraran komai da suke tattaunawa. "Dan Allah Aneleerh Ki nutsu inyi maki bayani..." Aneelerh bata bari tayi mata bayanin ba rai a6ace tace"me zaki fa a min benazir? Ni meyasa ma kika kirani ne? lokacin da yakamata ki kira baki kira ba sai yanzu da lokaci ya kure...." hankali atashe benazir ta ke sauraron ta idanunta sun ka a jawur da su la66anta na kerma ta furta"meyasa kikace haka"? uff taji Aneelerh ta kashe kiran, hawaye na sintiri ta dago tana kallon shureim wanda tuni jikin shi ya gama yin sanyi. "Yaya shureim ta kashe kiran, dama nasani ba lallai ta kula ni ba..." tsananin tausayinta ne Ya kama shi, hannu yasa ya kar6i wayar, Ya sake Kiran Aneelerh ta agowa. Text message Ya tura mata _Aneelerh ki aga kiran, Ba benazir bace yayanta dr shureim ne Ina son Yin magana dake_ A 6angaren Aneelerh, Jiki amace ta sulale kan carpet ta zauna dirshan sai kuka takeyi, bakomai take tunawa ba face Angel da tajuddeen, Taji takaicin yadda Benazir tayi watsi da rayuwarsu gashi Yanzu ita benazir din ta dawo su kuma sun 6ata babu su a doron duniya Muryar Angel ta soma tariyowa kalaman da saba fada mata tuntana yar anuwarta _Aunty aneelerh wai meyasa Mommyna bataso na? gani yar kyakkyawa dani kowa rububina yakeyi amma ita, bata damu dani ba, shine ma ta haifeni ta bar ni acikin kwamin ka, idan bata sona to meyasa ta haife ni ay da ta sani ta kashe ni acikin ta_ arar shigowar sakon ne Ya fargar da ita daga zurfin tunanin da ta shiga, zuciyartace ta dinga tunzurata akan kada ta duba wayar ta yale ta kawai, saboda ta bata haushi, Taji zafin abunda tayi. Wayar sai ringing takeyi taki dubawa, kasa jurewa tayi, saboda ita kanta tayi kewar aminiyartata, bazata taba mantawa da awancensu ba, duk da taci wahalar banezir saboda rashin jin maganarta. Yatsun hannunta na kerma ta ru o wayar ta duba sakon, bayan ta gama karantawa, a kagare ta soma kokarin bin kiran don taji me dr shureim zai fa a mata, aranta tana mai mamakin bayyanarsu lokaci aya. Video Call ta kirasu don ta ara tabbar da cewa su dinne, bayan sunyi picking call din kallon kallon suka soma jefawa junansu, kowa yasha kuka, hakika sunyi mamakin canzawar da sukayi, duk sun fara manyanta... Cikin sanyin murya ta furta"ya shureim! Dama kana nan"! Jinjina mata kai yai alamar eh, kafin Ya soma magana cikin nutsastsiyar muryar shi. "Aneelerh, inaso ki nutsu ki saurari abun da zan fada maki" amsa mashi tayi da toh, saboda tana ganin girma dr shureim. "Abun da Ya faru da banezir bayin kanta bane, mu kanmu bamu san da hakan ba sai lokacin da ta dawo, bata a cikin hayyacinta gaba aya alamomin da muka gani ajikinta ya tabbatar mana da cewa Kurciya akayi mata, shiyasa ta gudu tabar yarinyarta batare data tuntu6i kowa nata ba......" atsanake shureim ya fayyace mata komai, Ita kanta benazir din batasan da abun da suke zargin anyi mata ba sai yanzu da taji abakin dr shureim, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, aneelerh kuwa jikinta yagama mutuwa, cikin tashin hankali take ambaton inna lillahi wa'inna ilahirraji'un. Dr shureim Yace"hakuri zamuyi da abunda Ya riga ya faru, bana so muna tuna ba....." nasiha ya cigaba dayi masu har saida Yaga hankalin su Ya kwanta, kafin Ya bar wayar a hannun benazir Ya basu wuri don su gana da junansu Kamar yau ce rana ta farko da suka fara ha uwa, sai bin kansu suke yi da kallon kurulla, Allah ne ka ai Yasan irin kewar juna da su ka yi. "Benazir bansan yadda zan misalta maki farin cikin da nake a ciki ba, Allah shine shaidata, Naji dadin ganinki da ranki da lafiyarki" Cikin sanyin murya tace"nima haka Aneeleerh, ashe da rabon zamu gana bayan tsawon lokaci"? Ta fada tana matse kwallar da ta cike idununta. "Aneelerh, Ina Yarinyata dana bari? Ina mijina Yake? Mommy ta fada min basa kasar nan amma ni ban yarda da maganarta ba, dan Allah ki fada min gaskiya, saboda nasan ke kadaice zaki fada min" Fuskar Aneelerhh auke da matsananciyar damuwa take kallon benazir dama sai da tayi fargaban tambayar da zatai mata, tuni taji zafafan hawaye sun cika mata idanunta. "Aneelerh kinyi shiru baki ce komai ba? Pls ki yi min magana wlh ji nake kamar zan zauce saboda agarar da nayi na son ganin su ..." ta fa a tana dubanta "Kada ki ji komai, Ki fa amin kawai ko da ace sun mutune zan rungumi addara..." cikin karfin hali ta fa a, tun da tafara maganar Aneeleeh ke kallonta gwanin ban tausayi. bata jin zata Iya sanar da ita a yanzu, ko dan gudun kada zuciyarta ta buga, wara ta kwantar mata da hankalin ta. aro murmushi tayi akan fuskarta "Abun da mami ta fa a maki gaskiya ne, suna nan cikin koshin lafiya, sun yi tafiya zuwa south korea inda Uncle dinsa abdalla ke zaune, amma ina ji araina sun kusa dawowa" Tsabar farin ciki yasa banezir sakin dariya har fararen hakoranta suka bayyana, Aneelerh dake kallonta tsantsar tausayintane Ya ara kamata. "Dan Allah Aneelerh idan kina da hotonta ki turomin inason ganinta, Idan ma kina da number taj din ki bani sai muyi magana da shi, wlh na agara da son ganin su" Murmushi Aneelerh tayi"kada ki damu zan tura maki da hotonta har ma dana yaro na, sai dai bani da layin taj bansan da wanne yake amfani acan kasar ba" Da mamaki tace"Aneeleerh dagaske kin haihu? Ya'yan ki nawa yanzu"? "Shi kadai Allah Ya bani, baki ganshi ba, kyakkyawa kamar Angel dinki.." Muryarta na rawa tace"Allah sarki, Aneeleeh, na tayaki murna, Ina mijin ki ko shima hada shi suka tafi korean"? "Atare suka tafi" murmushi benazir tayi kafin ta kuma cewa"ki bani labarin Yarinyata, inason jin kuruciyarta, Ina fata dai bata dauko halina ba.." dariya aneelerh tayi da zolaya tace"like mother like daughter, Har tafi ki rashin ji magana," waro idanu banazir tayi hada sanye hannu ta dafe kanta aya"indai kuwa hakane nasan ba lallai ta yi min da sauki ba, watakil ma ta tsane ni, bata son ganina" ta fada tamkar zata fashe da kuka "Ki ma daina wannan tunanin, taya a zai i jinin uwarsa, ay bata da abu mafi soyuwa da yawuce mahaifiyarta, ni nasan Angel bazata ta6a gudunki ba" kwantar mata da hankali taci gaba dayi, har ta bata labarin unaisah, taci dariya wani wurin kuma ta matse kwalla. "Allah sarki tajudden na barshi da dawainiyar yarinya, abunda yakamata ace ni nayi bansamu damar yi ba..." in a cool voice tayi maganar," shiru suka danyi na wani lokaci kafin Aneelerh tace"Har yau babu labarin Aisha! Baiwar Allah taga rayuwa, gaba daya addarace ke bibiyar rayuwarmu lokaci aya awancenmu ya tarwatse nayi takaicin rasa farin cikin amintarmu' hawayen dake taruwa acikin idanunta tuni sun fara wanke fuskarta.... Shiru banezir tayi zuciyarta cike fal da jimamin halin da suka tsinci rayuwarsu. "Inaso nazo gidanku Aneelerh, ki kirani da layinki, sai inyi saving contact naki" amsa mata tayi da toh, sunjima suna waya kafin sukayi sallama da junansu.. Meya faru bayan Ummi Ta fuce daga dakin su Unaisah? Da gudu ta nufi dakinta, tana shiga ta bude toilet ta tsaya agaban Sink tana kwarara amai, idanunta sun kada jawur da su, shatun jijiyoyin goshinta sun fito rudu rudu kamar zasu fasa fatarta, tayi kuka tamkar ranta zai
Chapter 57 · 0% Book details