Sashe 215
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe aya. "Ina sauraronki! Fa amin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta an yi tana haki kamar wadda tasha gudu. Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta an kur6a. Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari.. *bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a arshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a asa rabin jikinta a cikin toilet Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci aya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata ha i da yi mata magiya akan ta bude amma ta i saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar walla. "Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta. yar ta iya tattara arfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta. A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba aya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da arta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta. Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, mi a hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko arya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta arfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana arin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya arfinta na arshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba aya gangar jikinta ta dawo cikin toilet in kanta ya daki floor, A zabure ta mi e ta watsa a guje ta nufi ofa sai dai me? Kafin ta arasa iiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ara ta yi da arfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun arfa jikinshi sanye da ba en kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfa iya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ona ka da ayar Allah..., bata are maganar ba ya aura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya dam e shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma arin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa ka ai bala'e ne tsaf zai ona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi, Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata ra i take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet in ta dinga bugunta da yar ta samu ofar ta bu e sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya ebeta gaba aya ta yanke jiki ta fa i yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi. Hankalin Anila dana Taj ba aramin tashi ya yi ba, Sun yi matu ar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir. "Kin taba fa a ma wani?" aga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban fa a masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba. Cike da al'ajabi yake an jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka fa a yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta fa a masa akan Benazir. Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su. agowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya bu aci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?" Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi" a mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana... "Naga baku sha fruit din ba," Ya an tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi.. "Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai" "Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi .. "Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya "Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba... "Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!" "Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ata ba, saboda ni na yi wahalar na udarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara. "Sau nawa kina yun urin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?" Bai are maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata." Murmushin gefen fuska ya an saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na aga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana agawa ....." Bai are maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da mi ewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka ha a ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta fa a har hawaye sun zubo kan fuskarta, Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?" "Calm down your mind, Unaisah ta ji sau i yanzu, bari na kirata ku gaisa." Ya fa a tare da aukar wayarsa yana arin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta! Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata aure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, afafunta na sanye da highhill masu an banzan tsini.... Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta. "Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya..... Da index finger inta ta nuna Benazir, "Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?" Rai a matu ar 6ace ta fa a da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci. "Ki amsa min tambayata??" Ta fa a tana zare mata gray eyes dinta... Tsabar ru u da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji.... "Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min." Ta fa a tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin unar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?" Yawu Aneelerh ta ha iya utt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..." Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta fa a