Sashe 68
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
fruit, bayan ta ajiye masu fuskarta da fara'a ta gaishe sa su,a mutunce suka amsa mata "Idan kin shiga ciki, Ki sanar da mutanan gidan su prime minister sun sauka lafiya yanzu ya kirani awaya ya fadamin nasan ba lallai suji ba" Murmushi tayi"in sha Allah zan sanar da su" ta fada tare da mikewa ta fuce daga garden "Kana sonta ne? Naga kana kallon ta" muryar chief ce Ta ratsa kunnansa da sauri ya kau da idonsa daga kallon bayan hajjaty ya wurga masa hararar zolaya"dan Allah ka daina wannan maganar, kawai daga na kalle ta? Ta6e baki owais yayi batare dayace komai ba, Ya dauki Tea pot Ya tsiyaya masu a cups, atare suka zauna suna sha gwanin ban sha'awa ___________________________________BossBature A6angaren Aneelerh wunin ranar da farin ciki tayi shi, babu wanda baisan da zancen bayyanar benazir ba, Harta su mami da abie sai da ta sanar da su, sunji dadi har addu'a sukai mata akan Allah ya ara tsareta daga sharrin wadanda sukai mata kurciya da kuma fatan Allah Yasa suma su Taj su bayyana kamar yadda benazir ta dawo. Tun bayan da ta kammala sallar la'asar ta du ufa tana kallon hotunan benazir da ta tura mata awaya, kamar yau tafara ganin ta, gaba daya zumudin son ganinta takeyi, akwai abubuwa da dama da take son taji daga gare ta, tana son tasan meya faru da ita bayan guduwarta? Sannan A wani hannu ta fa a? Murmushi tasaki yayin da take yin zooming fuskar benazir tayi haske jawur ta ara jiki ta zama big mama.. "Ya Allah kamar Yadda Ka nuna min benazir da ranta da lafiyarta Ya Allah ka nuna min su Uzair haka, har Yanzu ban fidda rai da su ba, saboda Inaji araina suna araye, Ya Allah ka tsare min mijina da dan uwansa da angel dina aduk inda suke, Ya Allah Idan sun riga mu gidan gaskiya kaji ansu ka gafarta masu alfarmar annabi muhammd SAW......" muryarta na rawa ta are maganar saboda kukan daya ciyota..... "Aunty Aneelerh" muryar zahrace ta katse mata kukan nata, da sauri ta sanya tafin hannu ta share hawayen don batason zahra taga kukan ta, hakan zai iya sanyata damuwa, murmushi ta kakaro akan fuskarta ta dago ta kalli zahra dake shigowa. "Na'am Sisterna" "Auntyna Ina ara tayaki Murna, Aunty benazir ta bayyana saura Angel dinmu in sha Allah itama zamu ganta, Ni nasan yau dakyar zaki iya runtsawa saboda zumudin haduwa da Aunty benazir" cike da nishadi zahra tayi maganar, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana dubanta. "Nagode zahra, ki cigaba da tayani addu'a Allah Ya bayyana su uzair, bana jin zan ma Iya bacci adaren yau, in sha Allah zanyi nafilfili akan su..." ta fada tana an yamutsa fuskarta dake a kunshe da damuwa. "Lokacin da yayan benazir Ya fada min cewa kurciya akai mata har ta gudu tabar gida, wallahi bakomai ya fado min araina ba face 6acewar su taj, farat aya aka neme su aka rasa, a tsakar dare, zahra baki tunanin suma kurciyar akayi ma su"? Idanunta Jawur ta jefa mata tambayar, shiru zahra tayi jimm alamar tana nazari kafin ta an jinjina kai tace"nima nayi tunanin hakan, zai iya yiwuwa, amma kada mu dogara akan hakan tunda bamu da tabbaci" "Kin fadi gaskiya zahra" Shiru suka danyi na wani lokaci.. "Zahra, dazu muna cikin yin magana bamu arasa ba abie Ya kira ni..." murmushi zahra tayi "Ni ma sham na shafa'a...." labari ta fara bata na dinner din hateem tun daga farko har karshe ta dire mata. Bakomai ne Ya tsaya ma Aneelerh arai ba face yarinyar da zahra ta bata labarin sun ha u har sunyi hotuna. "Ki nuna min hoton in gani" zumbur zahra ta mike tana fadin inna lillahi na manta wayar a hannun baby junaid tun azu tana a wurinsa, Allah Yasa bai yi min barna ba" da sauri ta fuce daga dakin ta shiga neman baby junaid itace har dakin ummi da mamie duk baya a ciki, har falo bata gan shi ba, da sauri ta nufi dakin abie nan ma babu shi ta dawo ta shiga dakin uncle still ba junaid Sai da ta gama shan wahalar nemansa har zata juya ta koma daki ta jiyo sautin muryarsa a kitchen shi da Ana suna magana. "Kinga wannan itace Angel dina aunty zahra ce ta dauko min hotonta" Adai dai lokacin zahra ta shiga kitchen din kafin Ana Ta kar6i wayar don taga hoton Angel din motsin shigowar zahra ya firgitar da junaid aru e Ya saki wayar ta kife kan floor, wani irin bugu zuciyar zahra tayi ba ita ba hatta Ana hankalin ta, sai da Ya tashi idanunsa azare suke kallon junaid wanda tuni yasha jinin jikin shi. Muryarsa na rawa ya furta"aunty zahra bani bane, Ana ne ta kada miki waya...' yana magana yana girgiza kansa duk yabi ya rude, Jikinta na tsuma Ta nufi wayar ta dauko ta tare da juyo da ita, gaba aya screen dinta ya tsastsage fatsa fatsa baka Iya ganin komai..... Kamar ta fasa ihu haka Taji tsabar bacin rai, a fadace tace"junaid hankalinka Ya kwanta ko? Ka fasa min waya! daga abun arziki na baka ita don ka kalli hotuna" ta fada tana zare masa ido fuskarta adaure tuni Ya ara firgita. "Sister zahra kiyi hakuri shima bada son ransa hakan ta faru ba, kada ki tsorata shi" Ana ce ta fada cikin kwantar da murya. Bata tsaya sauraronta ba, Ta ruko wuyan rigar junaid"don kaga ina maka wasa da dariya ko? Shiyasa har ka samu kwarin gwiwar fasa min phone, muje daki yau saika yaba ma aya zakinta an rainin wayau, dallah jibarka ko kunya babu" la66ansa ya fara ta6ewa alamar zaiyi kuka"kar na kuskura naga hawaye a idonka, wayar wuta zan sa maka" shiru yayi can kuma ya fara mata magiya"bazan ara ba aunty zahra, dan Allah kada ki buge ni, na tufa Allah" kiris Ya rage ta fashe da dariya ganin yadda Ya tsorata kamar ta ta6a bugunsa Alhalin tun da ya taso babu wanda Ya ta6a bugunsa Janshi tayi har zuwa bedroom dinta, Ta zaro wayar charger a jikin socket, kafin ta dawo gare shi da gudu ya fuce waje yana kuka, biyo shi tayi aguje tana kwala masa kira. Bai nufi ko'ina ba sai dakin mommynsa Yana shiga Ya fa a kan laps dinta Ya ameta yana fadin"mommy kice ma aunty zahra kada ta bugeni, bana so..." duk yabi ya dabarbace, a rude Aneelerh ke kallon bayansa Jikinsa sai kerma yakeyi"fadamin kaida wanene"? "Aunty kibarni da babyn nan, Allah Yau sai yaji ajikinsa, Har ni zai fasa ma screen din waya? daga abun arziki na bashi aronta don ya kalli hoton Unaisah shine zai fasa min phone" "Amma banji dadi ba junaid, meyasa zakai mata haka? Ka kyauta abun da kaima aunty zahra"? Ba tare daya dago dakansa ba yace"tayi hakuri bajan ara ba, mommy ki siya mata wata wayar cikin kudina da nake tarawa a wurin ki" dariya sukayi gaba dayansu jin abun da Yace. "Aunty aneelerh yanzu ya zanyi? Ni takaicina hotunan da baki gani ba" Mika mata hannu Aneelerh tayi muga wayar da sauri ta bata, duddubawa tayi kafin tace"zanyi magana da mahboob yakai maki ita wurin gyara, kada ki damu idan an dawo da ita sai ki nuna min hotunan" ajiyar zuciya zahra tadan sauke"shikenan amma duk da haka saina tsala masa wayar nan" ta fada tare da yunkurawa zata zane bayansa fashewa yayi da kuka yana fadin"aunty zahra kada ki bugeni, Allah Yana sama Yana kallon ki..." dariya zahra tayi"kasan da hakan shine ka fasa min wayar"? Muryarsa da shesshekar kuka Yace"ay mommy zata canza maki wata cikin kudina" tuntsirewa tayi da dariya cike da zolaya tace"ban ta6a sanin kai matsoraci bane sai yau, ay ko daga yanzu tun da na gano lagwonka, da zarar kamin rashin ji zan zane maka baya da wayar cazana" ma e mata kafa a yai, ba tare daya tanka mata *HAJIYA ADAMA A hankali tai parking motarta, fitowa tai cikin shiga ta lace, ta yafa mayafi kan kafadarta, fuskarta manne da farin glass, Shopping bags ta auko a back seat na motar, kafin ta Nufi cikin gidan tana gab da zata shiga bedroom din su ta tsinkayi Muryar Uncle abdallah yana waya "Kayi hakuri nasan ba haka mukai dakai ba, na saba alkawari amma ka dubi halin da nake aciki, lokaci aya na rasa ana bayan haka na rasa an yayana tare da yarsa, na rasa yayana da kakata kai kadaine zaka Iya taimakona a halin da nake a ciki, wlh ni zan iya maida maka adadin kudin dana kar6a a wurin ka saboda ka dawo mun da su indai suna araye na wammace na are rayuwata a talauci akan inci gaba da ganin damuwarta akan rashin haihuwa..." Muryarsa amarairaice yayi maganar kamar zaiyiwa mutun da suke yin wayar sujjada tsabar yadda yake lalla6a shi yana yi masa magiya Cak Ya tsaya da yin maganar ba tare daya arasa ta ba, sakamakon kamshin turaren hajiya adama da hancinsa ya sha o masa, a hankali Yai rejecting call din yana kokarin dai daita nutsuwar shi "Ba halin ki bane Yi min la6e,"! Taji Ya fa i fuskarshi ba fara'a Bata tanka mashi ba, har sai da ta arasa gaban gado ta daura shopping bags din kafin ta juyo ta dube shi da alamun rudani akan fuskarta "Gaskiya ka fa a ba halina bane, amma wannan wayar da kayi yanzu ta aure min kaina, dear wani kudi ne naji kana fadin zaka mayar adawo maka dasu idan suna araye!? Har kake fadin ka wammace ka are rayuwarka a talauci akan ganin damuwana na rashin haihuwa? Su wanene kake yin magana akan su? da wani irin kallon tuhuma take duban shi. Hannu Yasa ya an shafa keyar shi, daga ganin fuskarsa babu kwanciyar Hankali, tsufansa Ya ara bayyana musamman fuskarsa duk tayi tamoji tamoji. Maimakon Ya bata amsar tambayarta sai cewa yai"Har Kin kammala siyayyar? Dame dame kika siyo mana ne" A waske Ya fa a tare da nufar Shopping bags din da ta ajiye kan gado, Ya bu e Yana dudduba kayan ciki. Kamar sakarya Haka Ya barta a tsaye Tana kallon Ikon Allah. "Hajiyata, Yunwa nake ji, pls Ki