← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 119 OF 247

Sashe 119

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

tsawa kamar an cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato anin shi Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu. Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka aga ba...." bai are maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya dur ushe kan gwiwowinsa. Kallon sauran gate officers din yayi wa anda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bau an mutunne, bahago mai wuyar sha'ani. Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa. kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana.... "Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza, bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai....... Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta "Sannu da dawowa mommy, ya aiki"? Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu, "Sannu da dawo Aunty, ya aiki? "Lafiyalou shureim ya mai jikin"? "Mai jiki Alhamdulillah, taji sau i sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta... da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba. Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya ha e fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi." Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza arasa shiga ciki.... "Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya mi e agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"? Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta. dakyar ya iya bu e baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya dam i gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim. Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba. "Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi fa a! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.." bata are maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje watsawa tayi da gudu ta nufi upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta bu e baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya aga hannu zai ebe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi, ji kake tasss! Waro ido waje hajiya Saratu tayi, zuciyarta ta hasala, Idanunta sun ka a jawur batasan sa'adda hawaye suka wanke fuskarta. Dr shureim dake atsaye hannunsa dafe da kuncinsa, tsabar radadin marin da yaji har wasu taurari masu wutsiya ya gani suna gilmawa a cikin idanun shi, zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshin shi, cikin karyayyar murya ya dubi Alhaji musa Ya furta"ni kadai yakamata ka hukunta saboda ni nayi maka laifi, saboda na auki zeeenatu na fita da ita, kuma ni ne nayi karyar cewa da saninka, saboda ni a tunanina zeenatu yar uwatace ina da right din da zanyi iko da ita.." ya fada yana kallon cikin idon Uncle din nasa. "Duk akan Zeenatu kake tada jijiyoyin wuya? Meyasa? Kawai saboda na fita da ita munje asibiti duba yar uwarta! Wai duk kullan nan na menene? Ya jefa mashi tambayar, gaba aya ya daure Alhaji musa da mamakin shi "Uncle yakamata ka sani, mu fa ba makafi bane, duk wani motsinka akan yadda kake tafiyar da rayuwar Zeenatu muna lura, Wallahi abinda ka aikata yau ya sa na fara kokwanto! sannan inaso ka sani don munayi maka biyayya ba hakan yana nufin muna jin tsoronka ba, ni bana tsoron kowa sai mahallici na......" waro idanu waje Alhaji Musa yayi jin furucin shureim, yayi mamakin yadda ya iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi magana batare da jin shakkar shi ba, Hajiya Sarah taji dadin martanin da Shureim ya mayar masa. gaba aya kalaman dr Shureim a kunnan Alhaji Ubaid dake a la6e yana sauraron su, yaga komai daya faru akan idonshi, har hawaye saida ya zubar saboda yaji zafin kalaman da alhaji musa ya jefi shureim da su, sannan baiji dadin marin da yayi mashi ba, yaji takaici kamar ya binne kan shi. Yasan bazai iya yin komai ba shiyasa ya hana kan shi zuwa wurin su. "Idan ka cigaba da yanke hukunci cikin fushi, wallahi zakayi danasani"! Kamar sakarai haka Alhaji musa Yabi shureim da ido wato ta ko'ina ya daure shi da mamaki, Ya kasa furta kalma, ga wani gumi dake tsastsafo mashi... "Shureim ka yi hakuri dan Allah!.." hajiya sarah ta fa a idanunta cike tab da kwalla,"kada ki damu Aunty", A fusace Ya haura kafa ya nufi room din shi, girgiza kai hajiya sarah tayi rai a6ace ta nufi dakin ta. Lokaci aya Alhaji musa yaji jiri na niyar ibar shi, da sauri ya zauna kan sofa, ya dafe kanshi dake sarah mashi da hannu biyu" _________________________________ Lokacin da motocin su Baba Obie suka araso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka auko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu dur usa asa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare aya abila aya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi da yar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya ji e su.Pravin kuwa Yana ru e da qugu ya ha a uban gumi duk da sanyin A.c in dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da an kanoma... Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ru e saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu wararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare aya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat aya? alla Medical team din sun auki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun aure kai lafiyarta qalou....'! Babu irin kokarin da
Chapter 119 · 0% Book details