Sashe 83
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ta kunna kai ciki, Tunkafin Dr shureim Yayi parking Aneelerh ta fito da sauri ta nufi motar su tsabar son takai garesu har tuntube takusa yi, kafin ta araso Benazir tai saurin fitowa da gudun gaske ta nufi Aneelerh suka rungume juna kamar za su koma mutun aya, Fuskar Dr shureim auke da murmushi ya fito tare da zagayawa other side in motar Ya bu e ma Zeenatu, fitowa tay daga ciki ta soma bin ko'ina na gidan da kallo kafin ta sauke idanunta kan su Benazir dake a rungume da juna, "Yaya Shureim wannan itace awar Aunty Benazir in?" aga mata kai yai alamar eh, Tsawon mintuna kafin suka raba jikin su daga na juna, fuskokin su sharkaf da hawaye saboda kukan da suka sha, Cikin shesshekar kuka Benazir tace"A.. Aneelerh! Ashe da rabon zamu ara ganawa da junan mu? Itama Aneelern da muryar kuka tace "Benazir kinga yadda kika koma? Nayi maraicin ganinki, nayi kewarki aminiyata sosae, wlh bakiji dadin da nake ji ba..." da yar suke magana saboda kukan da suke yi har lokacin, Zeenatu sarkin tausayi har ta fara matsar walla, shi kanshi Dr shureim dauriya ce kawai Yake Yi, amma ba aramin tausayi suka bashi ba, bazai ta6a manta sha uwar da ke atsakaninsu ba, Fitowa Zahra tayi daga gidan karaf idanunta suka sauka akan su Dr shureim da Zeenatu Har saida taji gabanta Ya fa i ganin irin kyawun mutumin da kamalarsa da yar ta janye idanunta daga kansu ta mayar da dubanta ga su Aneelerh, Murmushi Zarah ta saki saboda taji da in ganin aminnan atare, "Ki daina kuka bana son ganin hawayen ki," Aneelerh ce tai maganar idanunta jawur Benazir tace "Idan kinaso In daina kema ki daina, taya bazanyi kuka ba Aneelerh? Nayi babban rashin da har abada bazan Iya ta6a yafewa kaina ba, laifina ne gani nake kamar nice silar da zumuncinmu ya tarwatse..." da sauri Aneelerh ta sanya hannu ta toshe mata bakinta "ki daina aurawa kanki laifi, saboda bayin kanki bane tafiyar da kikai, kema bada son ranki aka raba ki da danginki damu kanmu ba...." lallashinta taci gaba da yi Zeenatu har ta fara gajiya da tsayuwa dama ita bata saba da wahala ba, Tana faman jan ajiyar zuciya ta juya ta dubi su Shureim cikin sanyin murya tace"Aneelerh ga Yaya Shureim da Zeenatu iyar Uncle ina" da sauri Aneelerh ta nufe su fuskarta da fara'a ta gaishe da Yaya shureim "sannunku da zuwa Yaya shureim ku shigo daga ciki" tay maganar tare da hugging in Zeenatu tace "Yan mata sannunki kuyi ha uri mun barku atsaye" Kamar bata son ha a ido da shureim saboda girman shi da take gani, tun fil azal tana matu ar jin nauyinshi kuma tana girmama shi, "Yawwa anaeelerh mun same ku lafiya", "Lafiyalou Yayanmu" tay maganar tare da ru o hannun Zeenatu suka yi gaba Shureim Yabi bayansu tare da Benazir da sauri Zahra ta koma falo tana jiran su shigo don su gaisa, Lokacin da suka shigo falon Mami da Ummi suna atsaye suna jiran shigowarsu don su tarbesu, koda Benazir tayi arba da Mami wani irin nauyinta da kunyarta ne suka kamata, Mami kuwa fara'a tasaki da sauri ta janyo Benazir ta rungumeta tana an bubbuga bayanta "marhabun lale ata, tsawon lokaci munyi kewar rashin ki" lokaci aya Benazir taji hawaye sun sake wanke mata fuska Muryarta da shessheka ta furta"Ma..mi " sam takasa arasa maganar, "na fahimce ki basai kinyi min bayani ba, Aneelerh ta sanar dani komai, ki kwantar da hankalinki ba kuka yakamata kiyi ba, godiya yakamata mu yiwa Allah daya dawo mana dake cikin oshin lafiya" Mamin ta fa a tare da raba jikinsu ta sa tafin hannunta tana share mata hawaye Kafin ta ago ta dubi Dr shureim wanda tun da ya shigo ya sunnar da kanshi asa saboda nauyin Mami da yaji gani yake kamar har yanzu tabon da yai ma kansa zaisa su guje shi, yar ya motsa labbansa zai gaishe da ita Mami tayi saurin katseshi da cewa "Allah sarki Shureim kaine ka koma haka? Gaba aya kun canzamin, Shureim Ka yada zumunci iri iri Ka guje mu ka koma Egypt ban ta6a zaton zakai mana haka ba" Cikin sanyin murya yace"Mami ay min afuwa nima bada son raina ba nayi nesa daku, zaman asar ne Ya gagareni saboda abun da Ya faru, amma wallahi ko bayan da na tafi kuna araina..." bai are maganar ba Mami ta katse shi da cewa "bakomai Shureim, duk abun da Ya faru mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa Ya guje ma addararsa ba, naji dadin ganin ku cikin koshin lafiya sosae..." "Ku mu zauna" ta fa a tare da nuna masu sofas, Bayan kowa Ya zauna Ummi da Zahra suka yi masu barka da zuwa "Muyiwa Annabi salati" acewar Mami gaba aya suka yi atare kafin daga bisani Mami ta dubi Zeenatu dake ta faman zare blue eyes inta, gaba daya tarasa sukuni saboda bata saba shiga mutane ba kamar tana jin tsoron su, "Tabarakallahu ahsanul khaliqin, ata wacece wannan bakuyi min bayani ba, gata dai masha Allah daga gani ba jinsin asar mu bane" murmushi Zeenatu tayi, Ummi tace"kin riga ni fa a, tun da suka shigo ta tsole min ido, kamar in sace ta" dariya sukai cikin raha, "Sunanta Zeenatu, iyar Uncle ina ce" waro idanu Mami tayi ha i da jinjina kai, "Masha Allah, sannu Zeenatu" amsa mata tay da "yawwa" "Dan Allah ki saki jikinki, ki auka kamar kina agidanku ne, don na fahimci kamar kin takura" Murmushi Zeenatu tayi har dimples dinta suka lotsa, "Ina su Maminku ina fata duk suna lafiya" cikin kulawa tayi Maganar tana kallon benazir" "Suna nan lafiya, sunce mu gaishe daku, taso mu zo tare amma tace sai zuwa na gaba", Murmushi Mami tayi "Allah Ya kawo ta Lafiya in ma batazo ba ni na fidda lokaci inje gidan naku" Shiru sukayi na wani lokaci, kowa da abunda Yake sa awa aranshi, Benazir ta osa su ke6e da Aneelerh don su ara jajantama junansu. Fitowa daga kitchen Ana tayi hannunta auke da tray na kayan abincin da suka shirya masu har zata gifta ta an dakata tare da kallon ba in nasu karaf idanunta suka sauka akan fuskar benazir, tsabar ki ima da ganin Benazir iris Ya rage ta saki kayan abincin hannunta Jikinta Ya hau bari da sauri takai abincin Dining ta nufo su, gaba aya ta zube kan carpet tana ambaton sunan Benazir, Kusan atare suka ago suna kallonta duk tabi ta ru e muryarta na rawa take fa in "Aunty Benazir! Kece? Ko dai makuwa nayi ne?" Hawaye ne suka ciko idon benazir bakomai Ya fa o mata aranta ba face Irin azabtarwar da tayi ma yar'uwar Ana mai aikin gidanta Janet taci azaba a hannunta in tai mata laifi hada duka take ha a mat Cike da jin kunyar Ana tace"Ni ce Ana, ba makuwa kikai ba, fatan na same ki lafiya? Ina yar uwarki janet" Matse walla Ana tayi "Allah Sarki Aunty Benazir Ina nan lafiyalou, Janet tana a Jos tare da Esther ni ka ai ce anan, Aunty Benazir Ina kika shiga tsawon lokaci bamu ji uriyarki ba..." Kafin benazir ta bata amsa Aneelerh tayi saurin tarar numfashinta da cewa "Ana kije ki arasa shirya masu abincin, zanyi maki bayanin komai" ta fa i hakanne saboda bata son ana tayi maganar 6acewar su Angel gudun kada Benazir taji hankalinta Ya tashi, "Kada ki damu, zuwa anjima kafin mu tafi zan nemeki..." amsawa Ana tayi da toh, Jiki asanyaye ta mi e tana tafiya tana waiwayon su Benazir tana mamakin Matashiyar da suka zo da ita, aranta ta ayyana watakil itace Yar uncle insu da taji ance zasu zo da ita...har sai da ta shige kitchen tukunna ta daina kallon su, ewa Aneelerh tayi tare da kallon Benazir tace "mu shiga daga ciki", Mami tace "kuyi me? Ba zaki bari su ci abinci ba, salon ki cika ta da surutu" "Ba da ewa zamu yi ba Yanzu zamu fito" Ummi tace"ke ko an da e ba'a ha u ba, tana son su an ke6e ne ay firar yaushe rabo", ewa Benazir tayi suka nufi bedroom inta hannunsu cikin na juna, "Shureim ya'yanka nawa Yanzu" sunnar dakai asa yai jin tambayar da Mami tayi masa, Dariya tayi "dan Allah kada kace min bakai aureba" Cike da jin kunyarta Yace "banyi ba Mami, amma nakusa in sha Allah" tayi mamakin jin maganarsa gashi har ya fara manyanta baiyi aureba koda Yake komai sai Allah Ya nufa, "Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" amsa mata su kai da ameen, Shigowa Ana tayi "Mami na gama shirya abincin" Mami tace"toh, ku tashi mu arasa Ciki" Dr Shureim Yace"Alhamdulillah, bana Jin yunwa sai dai ko Zeenatu in zata ci" e kafa a Zeenatu tayi "nima bana jin yunwar ay naci abinci agida" yadda tai maganar yaso basu dariya har sun gane shagwa6a66iyace uri zukuyi ku tashi muje, Nasan baza'a rasa space a cikin ku ba ko ruwan zumunci ne ku sha" lalla6a su Ummi tayi har dai suka mi e suka bi su Mami zuwa dining.. A 6angarensu Benazir bayan sun shiga aki da Aneelerh, cike da zumu i suka zauna daga gefen gado Sai faman bin juna da kallo suke yi kamar yau suka fada ha "Kinga yadda kika canza? Kin ara girma kinyi kyau abunki, bani labari bayan kin tafi ina kika fa Numfasawa tay kafin tace"Wani bawan Allah ne Ya taimaki Rayuwata, Mutumin kirki, an family in Obinna nasan ba zaki rasa saninsa ba, sunan shi Zaki Mubarak Obinna A asar Canada Yake..." gaba aya Benazir ta bata labarin Yadda suka ha u da zaki a Abuja bayan ta gudu daga jos da yadda harya taimaketa suka bar kasar atare.. Jinjina kai Aneelerh tayi har cikin ranta taji dadi da rayuwar benazir bata wula anta ba, "Koma wanene Yayi miki wannan aika aikar in sha Allah sai yaga sakayya, tun agidan duniya, anso a cutar da rayuwarki, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane cikin ikonsa kin fa a hannu nagari", "Ni inda nagode ma Allah, ban tafi da tsohon ciki na ba, da bansan a Ina zan haife shi ba, ba rabon ata tasha wahala wlh banyi zaton