Sashe 10
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
mutunci, zamu rama ne" ta fa a tana dariya, baby junaid kuwa Ya aure fuska, Kumatunshi sunyi jawur da su, da alama kuka Yake so yayi. Atare suka nufi cikin gidan, tana agaba mahboob Yana abayanta Bayan shigarsu Falo, Suka taras da mami da Ummi zaune suna kallo a plasma tv din falo, Cikin girmamawa suka gaishe da su. "Sannun ku da dawowa, Ya gajiyar aiki"? Cikin Kulawa mami tayi maganar, atare suka hada baki wurin cewa"yawwa mami" Ummi dake kallon Baby junaid tace"to fa, Me akayi masa ne naga yana aure fuska" Mahboob Na dariya Yace"wallahi Ummi Rigimarshi ce ta motsa, Kinsan Halin shi. Zahra tace"bawani nan, shine Ya i zuwa aukarshi da wuri, Yabar shi a school yana ta jira" "Gaskiya mahboob Baka kyauta mana ba, saboda Allah, Haka akeyi? Sai kabar mana Yaro ga Yunwa" Ummi ce ta fa a tana satar kallon baby junaid duk don ta nuna mashi taji Haushi. "Ay mashi uziri mana, hakanan dai Mahboob bazai i zuwa aukar baby junaid ba sai dai idan wani uzirinne Ya ru e shi" mami na fadan hakan Mahboob Yace"ay har bayani nayi ma zahran, motana ne Ya samu matsala sai da nakaita gyara, in sha Allah Hakan ma bazata ara faruwa ba zan dinga zuwa ina dauko shi akan lokaci" Ummi tace"haka Yakamata" "Zonan babyn mommynsa" acewar Ummi ta fada tana mi a mashi hannu, ma e mata kafa a yayi alamar bazaije ba, Saima Ya ara ame Zahra, mami na dariya tace"In banda abunki sai kace bakisan halinsa ba idan Yana fushi Yafi bu atar jin umin mommynsa," "Ina auntyn tawa take"? "Tana a kitchen" Maimaita kalmar kitchen Zahra tayi, aranta ta furta me kuma Aunty Aneelerh take yi a kicin"? Batayi asa a gwiwa ba, Ta nufi kitchen din Mahboob Har Ya zauna kan sofa, sai kuma Ya mi e Yabi bayan zahra. Tunkafin su arasa kitchen din suka hango Aneelerh ta ha a uban gumi a kitchen tana girki, Ita kadai. Sam bata Ji alamar shigowarsu ba, ta zage damtse sai motsa miya take Yi "Aunty Aneelerh"? atare suka ha a baki wurin kiran sunanta, da sauri Ta rufe soup pot din, Ta juyo tana fuskantarsu, kafin ta aura idanunta akan Baby Junaid, Murmushi ta sakar masu "Sannunku da dawowa," "Yawww, Auntyna, Yau ke kike Aiki akitchen Ina Ana"? Zahra ce ta jefa mata tambayar, Mahboob Yace"Allah yasa dai lafiya" Girgiza kai tayi cikin sanyin murya ta soma magana"ba lafiya...." gaba aya ta labarta masu abunda Ya faru zuwansu dakin Ana tare da su mami, Hankalinsu Ba aramin tashi yayi ba, Musamman Mahboob. "Bansan Ya zanyi ba, Ta i fa a mana abun da ke damunta, Ni tsorona kada wani abu Ya faru da ita" fuskarta da tsantsar damuwa ta furta maganar "Nima hankalin bai kwanta da ita ba, dafarko nayi tsammanin Damuwar halin da an uwanta suke aciki ne ke damunta, ashe ba haka bane, daga gareta ne" Acewar Mahboob. Kafin Zahra ta furta magana baby Junaid Ya fashe da kuka, Dama ranshi a6ace Yake, da sauri Aneelerh Ta mi a hannu ta kar6e shi cikin sigar lallashi take jijjiga shi tana fadin"Am sorry My baby boy, kayi hakuri nasan nice na 6ata maka rai,' muryarshi da shesshe ar kuka Yace"wayyo Allah mommy, Kuna ta surutu Kin i kulani, baki missing ina ba" dariya zahra da mahboob su ka yi, hakan Ba aramin 6ata mashi rai yai ba, Hada Jifar Su da harara Shafa sumar kanshi tayi"Na kar6i laifina, ay min afwa... " zumbura mata baki yayi, Zahra tace"aunty Aneelerh, Ki tafi dashi aki Ni zan arasa girkin, Inyaso da anjima Sai mu arasa tattaunawa" "Keda kika dawo daga aiki a gajiye kuma kike neman in bar maki girki, a'a gaskiya Ki bari na arasa ai ba ni kadai nake yi ba, Tare da Ummi muke Yi, bata jima da komawa falo ba.. " Kafin Ta are maganar, Mahboob Yace"tun da tace zatayi kibar mata kawai, Nima saina tayata, baby junaid yana bu atar kulawarki, Kije Ki lallashe shi" Murmushi tasaki Tana kallonsu, Har cikin ranta take jin tsantsar kaunar Yan uwanta, Ha in kansu Na burgeta, fatanta Allah Ya dawwamar da farin ciki arayuwarsu, Hakika suna kyautata mata. "Nagode, zahra, Mahboob, Allah Ya barmu mun ku," Amsa mata su ka yi da ameen "Zan shiga ciki, pls zahra Ki dafa mashi indomie" amsa mata tayi da toh, Bayan fitar Aneeleeh daga kitchen din, Mahboob Ya ajiye food basket din Junaid, Yabi bayan aneelerh hannun shi ruke da backpack din Baby junaid, Bayan Ya ajiye mashi adaki, Ya fito Ya nufi nashi room din, shaf shaf Yayi wanka Ya sanya gajeran wando da ar singlet, Kafin Ya nufi kitchen don Ya taya zahra girki kamar wani mace, atare suka cigaba da kula da girkin, suna tattauna fira dangane da matsalar Ana. "Amma kai a tunaninka meke damunta"? "Sister Ni kaina nakasa gane wani tunani zanyi dangane da matsalar Ana, sai dai kawai mubita da addu'a, Allah ya yaye mata abunda ke damunta,' "Ni aganina, Mu kar6i Contact din an uwanta , mu tuntu6esu may be sunsan meke damunta, tunda sunfi kusa da ita" "Nima nayi tunanin hakan, Yanzu dai mu jira, zuwa lokacin da su Abie zasu dawo gidan, nasan zasu Kirata su tambayeta," "Hmm kana ganin zata Iya fa a masu gaskiya? Bayan Aunty Aneeleeh tace tare da su mamie suka je dakin nata amma ta i fada masu, ai ni aganina idanma akwai wanda Ya dace ta fadamawa baiwuci su mami dinba" Jinjina kai Mahboob Yayi"kin fadi gaskiya," "Ni abunma Ya fara bani tsoro, da naji aunty aneeleeh tace Ana ta dinga kwala masu ihu tana fadin su fita subar mata dakinta, Anya mahboob bata da matsalar kwalwa? Mahboob Yace"Bana tunanin hakan, wata'kil Aljanune suka shige ta, mu cigaba da tayata addu'a Allah Ya kawo mata saukin abunda ke damunta" "In sha Allah zamuyi mata" Daga haka basu ara magana ba, sun maida hankali akan Girkin da suke Yi. Fitowa Aneelerh tayi daga Bathroom, Bayanta goye da baby junaid, tayi mashi wanka, sai faman hade mata fuska Yake Yi, Riga da wando ta Dauko ta zura mashi ajikinshi, ta feshe shi da turare, zama tayi gefen gadonta,ta aura shi saman laps dinta, hannunta aya dafe ta shi,tarasa meke yi mata da i, Ita dai Hankalinta bai kwanta da halin da Ana take aciki ba, Ji take aranta kamar wani abunne Zai faru, zuciyarta batayi mata da i, sam ta manta da baby junaid Tayi zurfi a tunaninta, Har Ya fara lumshe ido zaiyi bacci, Muryar Zahra ta fargar da su, hannunta biyu ru e da plate din indomie, Sai tiriri Take Yi, daga saman indomie din ta shimfi a mashi Soyayyan kwai, Mahboob Yana abiye da bayanta, Hannun shi ru e da mugs biyu na kakkauran Tea. "Sannunku da kokari, nasanya ku aiki ko hutawa ba ku yi ba" "Pls ki daina fadin hakan, Mu yakamata mu Yi maki sannu, anbarki da girki a kitchen, Su mami suna a falo fira tai dadi" Mahboob Ne yai maganar Asaman Table zahra ta daura plate din, Mahboob Ma ya sauke nashi mugs din, atare suka fuce daga dakin. Baby junaid tunda yayi tozali da indomi Ya soma sakin murmushin murna, Har wani lashe le6ensa Yake Yi "Mommy da zafi, kuma ni Yunwa nake ji Allah" ashagwa6e Yayi maganar "calm down Your Mind my baby boy, Ni zan baka da hannuna, kasan dai mommy bazata bar baby junaid dinta Yaji zafi ba ko"? aga mata kai yai alamar" "Yawwa my boy" ta fa a tare dakai hannu ta dauki fork, ta soma nanna o taliyar tana hura mashi da baki idan ta huce saita tura mashi abaki, kusan atare suka cinye indomie din dakwai, Kafin suka sha tea din su. "Kada kayi bacci, Yanzu za'a fara kiran sallar magrib," aga mata kai yai alamar toh, Janshi ta soma yi da fira duk dan kada yayi bacci. Bayan Kammala sallar Magbrib, A lokacin Abie da Uncle an Iya sun shigo gidan, babu wanda Ya tuntu6esu da maganar Ana, sun bari ne sai sun huce gajiyar da suka kwaso ,Har saida suka kammala cin abincinsu, Tukunna Ummi ta sanar da su Halin da ake ciki, babu 6ata lokaci, Abie Yasa suka hallara A falon gidan gaba ayansu, Ana ce ka ai ke babu acikin su. Aneelerh da zahra da Mahboob suna zazzaune kan Carpet, A lokacin baby junaid Ya jima da yin bacci, Yana can kwance saman gado. Abie da Uncle an Iya suna a zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Abie Yana sanye da farar jallabiya ya manna farin glass a idanunsa, Yayin da Uncle an Iya yake asanye da Riga Yar shara ta farin Yadi, daga ciki ya sanya gajeran wando ba Su Mamie da Ummi suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun biyu, dukansu Hijabai ne a jikin su. tamkar mutuwa ta gifta babu mai magana acikinsu, Har na tsawon mintuna kafin daga bisani Uncle an Iya yayi masu gyaran murya, suka ago suna duban shi, da hannu Ya nuna Mahboob "Je ka kira ta" Amsawa mahboob Yayi da toh, ya mi e ya nufi bedroom din Ana, abakin ofar Ya tsaya tare da kai hannu yayi knocking kofar kusan sau uku bata bu e ba, Har ya fara tunanin ko bacci tayi ne sai kuma Yajiyo mutsu mutsunta ta cikin akin. A hankali ta turo ofar akin, tare da le o da kanta, Ko da mahboob yai tozali da fuskarta sai da gabanshi ya fa i ganin yadda ta kumbura suntum, idanuwanta sun ka a jawur, daga gani kukan take cikin yi In a calm voice Ya furta"ina fata ban katse maki baccin ki ba" Muryarta adisashe tace"ban kaiga Yin baccin ba," Jinjina kai yayi"Uncle ne yace in kira ki, su na a falo shi da su mamie da abie" Shiru tayi jimmm kamar bazata motsa ba, har saida ya maimaita mata maganar tukunna tace Toh, ka jirani mu tafi atare" "Okey" Maida ofa tayi ta rufe ta, badajimawa ba sai gata ta fito sanye da doguwar riga, ta yafa mayafi akanta, Jin ta ru o hannun shi acikin nata ne yasa shi saurin kallonta, sam hankalinta ba akwance Yake ba, bai yi yun urin raba hannun shi daga