Sashe 52
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
laga shi akanta. Ita kanta data kalli madubi sai da ta firgita da ganin wani sihirtaccen kyau daya bayy ana akan fuskarta, murmushi tadan saki har dimples dinta suka lotsa. "Daughter I'm waiting For You, Kin bar daddy awaje Yana ta jiranki" Muryar taj tajiyo daga waje yana magana, da sauri ta nufi kofar ta fito, waro idanu waje taj yai arude Ya furta"Tabarakallahu ahsanun khalikin! My Angel? Kinga kuwa kyan da kikayi kamar hurul aini" sunnar da kanta kasa tay, fuskarta sauke da murmushi Ruko hannunta yai a cikin nashi suka nufi dakin chief. Abakin kofar dakin suka dakata suna kallon juna Lokaci daya suka sakar ma juna murmushi a yai mata a kunnanta"ba'ay mashi rashin jin magana ba kamar daddy bane da aka raina" dariya tayi jin abun da yace. Sakin hannunta yai"ki kula min da kanki," amsa mashi tayi da toh, kamar karsu rabu yana tafiya yana waiwayonta itama sai kallon shi take yi aga murya tayi tare da cewa"daddy kada ka tafi ka jirani in fito" "Ba nesa zanyi ba, Zanje gidane bazan jima ba zan dawo" ta6e mashi baki tayi kamar zatayi kuka, hakan ba karamin nishadi ya sanya shi ba. Zuciyarta Cike fal da fargaban ha uwa dashi tay knocking kofar, Almost 3 times ba'a bude ba, harta fara tunanin ko dai bacci yakeyi ne ko baya a dakin har zata juya kofar ta soma zugewa a hankali ta bu e, kamshin turarensa ne Ya fara dakar mata hanci har saida ta dan lumashe idanunta. Kasa shiga tay saboda zullumin hada ido da shi, da kuma jin nauyn magana da shi. Sai da ta shafe kusan mintuna biyar, tana sa e sa e a zuciyarta ba tare da ta motsa ba, kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta kwatsam kofar ta soma kokarin rufe kanta, da sauri ta ratsa ta tsakankanin door din da karfi ta fa a dakin kamar wadda aka jeho, iris Ya rage ofar ta datse da jikinta, wannan gangancin nata ba karamin mamaki ya bashi ba, sai faman nishi take yi hadi da sauke ajiyar zuciya, sai da tagama yan kame kamen ta, kafin a hankali kamar maijin tsoronsa ta soma bin dakin da kallon, Lokacin da ta daura idanunta akan shi har saida gabanta Ya fadi ganin surar jikin shi, Har yanzu bai motsa daga kan gadon shi ba, kamar yadda Big guy ya barshi haka ta taras da shi sanye da rigar wanka, ya daura Apple laptop dinsa kan waist insa, Yayin da kanshi ke akan pillow ya dan lumshe idanunsa, tuni kamshin turarenta yakai mashi karo Yawu ta ha iya, a tunaninta baya ganin ta cikin sanda ta matsa daga gaban gadon tana faman zare gray eye dinta ta furta"ina kwana, ka tashi lafiya" magana takeyi hankalinta na akan kwantaccen sajen fuskarshi. "Lafiya" taji ya amsa mata da sanyin murya, tayi mamakin jin voice dinsa irin na danish. Shiru tayi tana faman wurwurga eye balls dinta, bata ta6a jin nauyin wani dan adam ba sai akan shi, kamar ma kunyar shi take ji Wasa takama yi da yatsun hannunta, batasan cewa yana kallonta ta cikin laptop dinsa ba. "Idan kingama tsayuwar zaki iya tafiya" sexy voice dinsa ce ta kuma ratsa kunnanta, muryarta da en ena tace"am.. um. wai Dama daddy ne yace inzo in yi maka godiya" Shiru yayi yana maimaita maganarta a zuciyarsa kafin ya furta"bake ki kayi niyar zuwa ba? Shiya tursasa maki kizo"? Dafe kai tay da hannu daya alamar ta kwafsa. "Mantawa nayi, ni nayi niyar zuwa inyi maka godiya". Ta6e pink lips dinsa yai na an wani lokaci kafin yace"ba'ay min godiya, duk wani abu da nayi nayine don Allah, ina fata kin fahimce ni" amsa mashi tayi da toh, shiru suka kuma yi, Ganin yaki sake tanka matane yasa tai kafin halin cewa"tun da bakason ay maka godiya, to ka fadamin wani abu da zan dinga yi maka tunda kaima ka kyautata mana duk da nasan bazan iya biyan ka ba" ta fa a tana cuke la66anta. A hankali ya dan ware reddish eyes dinsa, duk wani motsinta akan idonsa sai dai ita batasan Yana kallonta. "Will you do whatever I tell you?"da kwarin gwiwa ta amsa mashi Eh "Okey," ya furta tare da sauke Laptop dinsa gefe aya, a hanzarce ta juya mashi eya, Ganin zai mike kuma taga bathrobe ce a jikin shi, murmushin gefen fuska ya dan saki. Saukowa yai daga kan gadon Ya nufi walk-in closet dinsa, Jim ka an Ya fito sanye da thobe launin ruwan toka, tamkar a jikinsa aka dinka ta tsabar yadda ta bayyana surarsa. Kamar yadda yabarta haka ya same ta atsaye ta juya baya. Zama yai gefen gadon da alama bata san ya dawo ba. "Zaki Iya zuba min abinci"? an zaro idanunta tayi kafin ta amsa mashi da toh, juyawa tayi a hankali ta saci kallonsa Idanunsa na akan wayar hannunsa, taji dadin ganin hankalinsa baya akanta Cikin takun sanda ta karasa daga gaban table din. "Me kakeso nafara zuba maka" "Duk abun da yai maki" farfari tayi da idonta hada an gumtse baki alamar mamaki, sam batayi zaton zai kulata har haka ba, kallo aya da tai masa ta fahimci mutunne mai ji da kansa Coffee ta mika masa yasa hannu ya kar6a A hankali Yake kurbarsa, Angel sai faman satar kallon la66ansa take Yi, ba karamin rudarta yakeyi ba, ga kamshin turarensa dake ta kai mata hari. Komai ta zuba masa cinye shi yake yi, mutumin da bai cika cin abinci ba, amma yau har saida yaso ya wari cikin sa, ba tare daya ankare ba.. Bayan ta kammala serving nasa tace"ko akwai wani abun da zanyi maka? Ko in gyara maka bedroom din ka" "Idan kin ji zaki iya" ta6e baki tadanyi kafin tafara tunanin shiga toilet dinsa ta gyara masa shi, watakil kafin ta fito shi kuma Ya fita sai ta gyara dakin Juyawa tayi da sauri ta nufi toilet din, sai lokacin Ya dago Yana bin bayanta da kallo har sai da ta 6ace ma ganinsa tukunna ya kau da idonsa. ZAHRA udundune take kan darduma ta lullu6e jikinta da hijabi, tun bayan sallar asubahi bata farka daga bacci ba. Shigowa Dakin Aneelerh tayi, hannunta ru e dana baby junaid, sakin hannunta yai da gudu ya tunkari zahra Ya fa a jikinta yana fadin"aunty zahra Ina tsarabar da kika ce zakiyi min jiya! Shine ma baki tada ni daga bacci ba" Janyo shi Aneelerh tayi tana fadin"meye haka? Ba ka ga bacci take yi ba"? Zahra dake sauraronsu tayi shiru batare da ta motsa ba ashe idonta biyu. Da shagwa6a baby junaid yace"mommy ay itane tace zata min tsaraba, Ni ta tashi ta bani abuna kamin taci gaba da baccin..." bai kare maganar ba, ta rufe bakinsa da tafin hannunta. "Yi shiru kada ta farka, mu tafi zuwa anjima sai mu dawo" ma e mata kafa a yayi"nidai ba inda zani Allah, sai ta bani abuna" kwace hannunsa yai daga na Aneelerh Ya fada kan zahra yana kiciniyar tada ta daga bacci, duk yadda taso tayi pretending sai da takasa tana faman fitar da numfashi mai an huci ta sanya hannu ta janye junaid kafin ta mike zaune ta tu6e hijab din jikinta ta jefar da shi gefe Har saida gaban aneerlah Ya fadi ganin jirwayen hawaye akan fuskar zahra, idanunta sun kumbura suntum da su, da alama tasha kuka har ta gaji. Waro idanu waje baby junaid Yayi "mommy mun shiga uku, aunty zahra kuka tayi wani ya buge ta . " bai kare maganar ba, zahra tai saurin sanya hannu ta dan buge bakinsa"kada na kuskura nasake ji kayi magana," ta6e mata baki yai alamar zai yi kuka da sauri ta janyoshi tare da manna shi kan kirjinta, wani sabon kukan ne ta kuma fashewa da shi. Hankalin Aneelerh ba karamin tashi yayi ba, tuni yanayin fuskarta Ya canza, matsawo tayi kusa da zahra ta zauna, cikin sanyin murya tace"ni dama tun jiya da kika dawo gida hankalina bai kwanta da yanayin ki ba, saboda na lura da yadda kike kokarin danne damuwarki saboda kada mu gane! Meyasa zahra eyeh? Adan tsawace ta fada tana dubanta "Ki fadamin me ya faru dake ne? Waye ya ta6a min ke yanzun nan in aura amarar yin ya i da shi"! ta fa a babu wasa akan fuskarta, Cikin shesshekar kuka zahra tace"a.. Aunty Aneeleerh zayn! Na shiga uku! Hajiya saratu ta ha a ni da masifa, ashe lokacin da ta turamin sakon nan tace min in zabi daya daga cikinsu nayi kuskuran rubuta sunan zayn a maimakon zaid shine fa ta ha a ni dashi, aunty aneelerh baki ji kalaman daya furta min ba.........' a tsanake tafara bata labarin abun da ya faru jiya bayan da hajiya saratu ta kira ta. Fitowa tai daga hall din tana ta faman yan kalle kalle can ta hango hajiya saratu tsaye abakin motarta, Cikin girmamawa ta arasa daga gefen ta, bayan sun ara gaisawa zahra tace "mommy gani" murmushi hajiya saratu tasakar mata tare da ruko hannunta acikin nata"mu shiga ciki, inaga zaifi muyi magana a tsanake" ta fada tare da bu e murfin backseat, bayan sun shiga taja kofa ta rufe, Zahra sai faman bin cikin motar take da kallo, saboda haduwarta ga sanyi a.c dake ratsa fatar mutun Shiru sukayi babu mai magana, Hankalin hajiya saratu na akan wayar hannunta da take an daddanawa, "Zahra," ta ambaci sunanta, da sauri ta amsa da na'am "Ina fata kin nishadantu da dinner din nan," tana dan murmushi ta jinjina kanta tare da cewa"Eh mommy, Alhamdulillah, naji dadin gayyatana da kikayi, I can't thank you enough" Murmushin dattako hajiya saratu tayi"kada ki damu, kin cancanta ne, ni kaina najima ina mamakin yadda kika kwanta min araina, saboda ba kowa nake mu'amala da shi ba, ina da wuyar sha'ani zahra " ta fa a ba tare da ta ago da idonta dake akan screen in wayarta ba. Zahra sai faman sakin murmushi takeyi taji dadin maganar da hajiya saratu ta furta mata. "Kinsan meyasa na kira ki"! "A'a" "Idan ba zaki manta ba, Kwanakin baya na tura maki hoton twins dina, har nace idan na baki za6i wanne kike so acikin su, ashe kin bani amsa ban samu damar