← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 89 OF 247

Sashe 89

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

dinner din...." gyara zama zahra tayi gaba daya ta kwashe abun da Ya faru ta sanar da mami Lamarin yayi mugun daurewa mami kai Aneelerh ta ara da cewa"yanzu haka can estate din zamuje, don mu tabbatar da abun da muke hasashe akan Yarinyar..." jinjina kai mami tayi ita kanta ta goyi bayan suje saboda kamannin Yarinyar dana Angel sun 6aci, bugu da ari da taji cewa Yaran tsintattune watakil su dace "Aneelerh zaiyi wuya ace yarinyar nan ba ita bace, amma dai kuje kawai, Allah Yasa adace" "Ameen mami, ki tayamu da addu'a Allah Yasa mu samu ganin ta cikin sau i, saboda estate din nasu ba karamin tsarone da shi ba, In har ba wani daga cikin Ahlin su Ya gayyace ka ba to basu bari bakuwar fuska ya shiga....." "Ita zahra ba suna mutunci da mutanan gidan ba"? Acewar mami Zahra tace"hajiya saratu ce, nasan indai na tuntu6eta zata taimaka mana, duk da nasan mawuyacin abune tun da yaran a hannun chief owais suke da zama, Ba lallai su bari mu gan su ba..... Shiru mami tayi kafin tace"to me zai hana ku kira an jaridan nan shima badaga family dinsu Yake ba kuma ay yasan da zancen 6acewar yarinyar tun da har bayanan an tura masa....." "Har kiran layinsa nayi kwata kwata baya shiga, watakil ko Ya shiga wurin aiki ne..." Mami ta gya a kai"shikenan Kuje kawai sai ku kira hajiya saratun, sannan dan Allah idan ba abaku damar shiga ba kada ku takura kanku ku dawo gida kawai inyaso sai ayiwa an iya magana tun da shi ya saba hulda da yan siyasa watakil ku samu hanyar shiga ta wurinsa..... Amsa mata sukai da toh, Kafin su mi e mami tay hanzarin dakatar da su"ku jira mahboob Ya shigo gidan, kwara kuje da namiji" Zama sukai har saida Mahboob Ya dawo Mami ta sanar da shi komai, ay tun da yaji zancen Unaisah ya gaza samun nutsuwarsa dama yajima da burin su gano yarinyar ba dan komai ba sai don jarin da Yake tunanin zai samu da ita shi uban son banza.... Lokacin da Motarsu ta shararo kan titin obie estate Aneelerh ta jinjinama haduwar wurin kasancewar yau ne na farko da suka fara zuwa, bata gama shan mamakin daular ba sai da Mahboob Yayi parking a gaban tankameman gate din estate din, hankalin su ba karamin tashi yai ba ganin Jami'an dake tsaron shi, sojoji da Jami'an Isod Babu wanda Yayi gigin fitowa daga cikin motar, Mahboob Yace"mun kawo kanmu, zahra ni fa tsoron tunkararsu nake Yi Allah, Sai dai wani daga cikin ku Ya arasa driving din... Yar dariya zahra tayi"bansan Iya shege mahboob dalla ka arasa mana sai kace ba namiji ba"? "Indai saina tunkari wadannan masu fuskar shanun zan zama namiji to wlh na kwammace ku kirani da sunan hajara...." dariya suka sanya gaba ayansu.... Mahboob Fa Ya dage akan bazai karasa da su ba...." Kwatsam biyu daga cikin sojojin suka tunkaro motarsu hannayensu ruke da bindigogi tuni zufa ta fara wanke fuskar mahboob ganin Yana kokarin tada motar Yasa zahra yin saurin cafke hannunsa"haba mahboob meye haka? Wai dama haka kake da shegen tsoro? Harara Ya galla mata"nifa ba tsoronsu nake ji ba, tashin hankali ne ke banso ..." da yar Ya are maganar ganin har sojojin sun araso gare su Kwankwasa window glass din motar, aya daga cikin su Yayi da kakkausar murya Ya furta"Put down the glass!" Aneelerh ce tayi karfin halin sauke glass din windown Ya zukunno da kansa Yana binsu da kallo idanunsa jawur "Su wanene ku kuma daga Ina? Murya na rawa zahra tace"wurin Hajiya saratu muka zo...." "Okey, Ku kirata awaya don ba'a sanar damu zuwanku ba" jiki na kerma ta amsa mashi da toh, da sauri zahra ta kira Layin hajiya saratu, kusan sau takwas baya shiga, Hankalinsu ba karamin tashi Yayi ba "Bari na ara kiran ziyad watakil shi Ya aga" aneeelrh ta fada yatsun hannunta na kerma ta curo waya ta kira layin ziyad tana ringin baya picking, hankalinsu duk Ya tashi asa asa da murya Aneelerh tace"mun shiga uku zahra shima bai aga ba yanzu ya zamuyi"? Mahboob da ya gama tsorata Yace"mu koma gida kawai shine mafita in ba haka ba wlh wannan mai fuskar shanun tsaf zai Iya bombing motar mu... cikin muryar ra a yai magana Zahra tace"wait bari na kira zayn duk da nasan mayucin abune yayi picking..." koda Ta kira layin zayn sau uku baiyi picking ba, A kira na hu u ne Ya aga muryarsa kamar ta mashayin giya ya furta "Waye"? Ko sallamarta bai amsa ba Cike da jin shakkarsa ta furta"zahra ce" "Wace zahra"? Sarai fa Ya gane muryarta har saving layinta Yana da shi awaya "Am..zahra wadda mommynka ta ha a ka da ita, a wurin dinner din prime minister "Okey nagane, lafiya kika kira"? "Munzo estate dinkune an hana mu shiga, sojojin sunce dole sai an basu izni kafin su bari mu shiga Kafin ta kare maganar Zayn yace"kina hauka ne? Ki rasa wa zaki kira saini? Oh tun yanzu raini Ya fara shiga tsakanina dake! Uban me ma Ya kawo ku estate din? Hatta su Aneelerh sai da sukajiyo masifar da yake zazzaga mata "Dan Allah ka taimaka mana, bamu da wata mafita ne shiyasa na kira ka, wani abu ne mai mahimmanci Ya kawo mu...." kamar zata sanya kuka "Look, Ku koma inda ku ka fito tun da baku da wani ala a damu" Yana are maganar Ya katse kiran, Tashin sense gasu dai agaban estate an hana su shigaa "Yanzu menene mafita? acewar Aneelerh "Aunty aneelerh mu hakura kawai tun da kowa yaki aga kiranmu Inyaso ko zuwa gobe sai mu dawo in ba haka ba wahala zamu sha.." Gurgiza kai aneerlerh tayi"bana jin zan iya komawa gida, sai dai ku tafi kubarni, Ni kawai zanje na roke su su barmu mu shiga ta fada tare da bude car door din Ta fuce da sauri zahra da mahboob suka bi bayanta Babu irin magiyar da aneelerh batay masu ba, amma suka dage akan dole sai an basu izni, a karshe ma wani fusatacce daga cikin su Ya tsawatar masu akan su koma inda suka fito Rai a6ace Aneelerh ta dawo jikin motar ta tsaya fuskarta har ta fara zubda gumi, mahboob da zahra sai rokonta suke akan su hakura su tafi gida, amma ta kafe akan ba inda zataje, su kansu sunyi mamakin taurin kan aneelerh abun da bata ta6a yi ba...... Har mami zahra ta kira tayi mata bayanin halin da suke a ciki, tace su ba aneelerh waya su yi magana bayan ta kar6a mami tace tay hakuri su dawo gida kawai inyaso sai ayi ma uncle dan iya magana.." ta amsa mata da toh bayan sunyi sallama da mami, su zahra har sun fara sauke ajiyar zuciya a tunanin su zata koma akarshe sai cewa tayi"ita fa kawai ta amsa ma mami ne, amma fa ba inda zataje sai taga abun da ya turewa buzu na i..." kamar su daura hannu akai suyi ihu haka suka ji, sojojin dake zirga zirga sai kallonsu sukeyi su kansu sunyi mamakin taurin kan matar da basu san wacece ita ba, don ma Taci albarkacin Kyan dake gareta ay da tuni sunyi masu korar kare daga Layin. babban abun da Yafi damunta dayasa har ta kafe akan sai sun shiga halin Da benazir ta shiga jiya Ya aga hankalinta da ciwon abun ta kwana jiya tasan mawucin abune in wani abu bai faru da ita ba, wanda yasa har bata neme ta ba kuma in ta kira bata samu Su zahra har sun gaji da tsayuwa tsawon awanni uku har karfe 1 na rana ta buga, kamar zasu sanya mata kuka fuskokin kowannansu sun Yi jawur Kiran wayane Ya shigo layin Aneelerh a hanzarce ta duba screen ganin sunan benazir ya bayyana ne Yasa tai gaggawar aga kiran hadi da kara wayar a kunne Muryarta har rawa take wurin furta"benazir ina kika shiga inata kira baya shiga...." cak ta tsaya da maganar jin muryar Dr shureim "Aneelerh ba ita bace Shureim ne Ina fata kun tashi lafiya..." tun daga kan yanayin sautin muryarsa ta fuskanci babu lafiya Gabanta na fa uwa tace"yaya shurem ina benazir din, tun Jiya bayan kun tafi nake ta jaraba kiran layin ta don inji ko kun isa gida lafiya amma ba'a aga wa... "Aneeelerh! Kunyi magana jiya da benazir akan mijinta ..." Murya na rawa tace"eh.. munyi" "Meyasa kika fa a mata abun da ya faru da su..." "Yaya shureim wallahi banyi niyar sanar da ita ba, itace ta matsamin..." gaba daya ta fa a masa maganar da sukai da benazir har rikicewar da tayi "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..." shine abun da taji Ya furta... Su zahra dake kallon fuskar aneelerh Hankulansu duk sun tashi tunkafin ma suji me suke magana akai "yaya shureim wani abu Ya faru ne..." Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer Privacy Policy Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 27 Complete
Chapter 89 · 0% Book details