Sashe 171
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
okinsu sai girmama su ake. Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table in saida suka cika shi da kayan abinci kala kala. Yau gaba ayansu su ka yi dinner a tare da ba in su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji da in karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun ha a ala a ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nisha i da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci ka an ka an kuma hankalin ta yafi karkata akan daddynta saboda shine damuwarta. Bayan sun kammala cin dinner in, wata sabuwar firar ce ta 6arke a tsakanin sojojin da su Chief har kusan arfe goma kafin Big guy ya raka su masaukin da za su zauna, duk yadda Unaisah taso ta gana da daddynta a daren ranar abun yaci tura tana ta jiran zuwan shi tasan ya saba duk in yana gidan dare yayi sai ya zo dakinsu yayi mata sallama kafin ya tafi amma yau taji shiru, koda ta fito bata iske kowa a falon ba, shima yayi tafiyar shi, da damuwa ta kwana a ranta. Gidan Kurkukun addara _____________________________ Meke faruwa a gidan kurkukun addara? Saboda gabatowar gagarumin shagalin da zasuyi na black Night, sun fara shirye-shiryen tarbar wannan dare mai daraja a gurin su, Yanzu sun dakata da yin duk wani mugun abu da suke yi a gidan kurkukun, hatta fursinonin su sun yi mamakin sauyin da suka gani, lafiyayyan abinci suke basu mai rai da lafiya har sau uku a rana, bayan haka sun tsaftace akunan prisoners din da makewayin su sun kuma canza masu sabbin Uniform. Duk da sauyin da suka samu, hakan bai saka su yin murna ba, saboda sun san da wata manufa a asa, wata wutar bala'en ce zata kunno kai, kamar ko sun sani dalilin dayasa suka sauya masu cimarsu daga ganye zuwa lafiyayyan abinci mai gina jiki, saboda albarkatun jikinsu su cicciko suyi iba fatarsu tayi kyau don su ji da in aikata fasi anci da su, a cikin abincin da ake kawo masu hada wata kwayar sihirin da suke saka masu a cikin dafaffen kwai, kamar sha ka fashe take aiki a jikin an adam walau mace ko namiji, cikin kankanin lokaci Yake ciko da duk wata ramar jikin su ya ha66aka jinin jikin su. Lallai Elders Sun shirya ma Black Night.. Yau gaba aya Sun fiddo da Prisoners din dake a kurkukun zuwa tsakar prison din, ko ina ka kalla sune birjik, sun jera layi, as usual jajayen uniform ne a jikin su, a yanzu babu masu black Uniform na an baiwa tun daga kan su Unaisah. alla fursinonin da suka rage agidan kurkukun addara zasu kai kimanin ari uku da hamsin, daga ciki harda jariran da suke raino. Yan matan suna asanye da short gown wadda bata wuci gwuiwarsu ba, mazan kuma riga da wando ne ajikin su, babu mai magana a cikinsu kamar gumaka sun ame a tsaye ko motsi basa yi, Iya wayar idanun su ce kadai take kyakkyaftawa sai numfashinsu dake fita. Bakomai ne yasa suka nutsu ba, fa ce Giants in dake a kewaye da su, Wasu irin gabza-gabza masu jini a jika. sun kasa sun tsare sai suntiri suke umarni kawai suke Jira su aiwatar. Cikin takun Izza Tsohuwa Inno ta nufo gurinsu hannun ta ru e da sanda, kamar kullum a cikin shiga ta red gown take, daga bayanta Giants in dake take mata baya ne, kan matakalar benan dake fuskantar prisoners in suka dakata da yin tafiya, ta tsaya tana bin su da antaccen kallo. har na tsawon mintuna batare data furta kalma ba, sai da ta mula ta sha iska kafin ta fara magana a a gadaran ce "Duk wanda na kira lamba in shi a cikin ku, Ya koma gefe aya" ta fa a tare da nuna masu inda zasu tsaya da sandar hannun ta.. "Prisoner no twelve, Thirteen, Fourteen...' duk wanda ta kira sunansa, Jikinsa na kerma yake fitowa daga cikin layi ya tsaya gefe aya, daga gani masu kyawun surar cikin su take za ulowa wa anda suka zama matured. Kusan fursinoni arba'in da takwas ta kira, mata sunfi yawa acikin su, saida ta kammala kiran lambobin wa anda ta zaba kafin ta furta prisoner no 100 shiru ba'a amsa mata ba, da alama ta manta aika aikar dasa giant yayi mata, tsawa ta daka masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?" Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi arfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ara ganin ta ba"! Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata. Giant in dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin bu iyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita akin fi a kamar yadda kika bani umarni, ban ara bi ta kanta ba" Murmushin gefen fuska ta saki, "If she dies, I will be sad because I want her to witness the black night, Even though I know even if she is alive, she will not be useful anymore." Cike da sha iyanci ta fa a kafin ta sake ce ma giant "Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita akin fi a ka tabbatar sun fe e sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar. "Bayan na kaita akin fi ar, ban ara komawa ba, saboda ba hurumina bane" Bata tsaya taji arshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya. bata nufi ko'ina ba sai dakin fi a, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici in dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta. Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta. Wani irin ululun ba in ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani haya in huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa.. A matu ar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya auke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo. da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta. _"Fa a da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yun urin yi min rashin a'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_ waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya arfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi _bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_ Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata. Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta fa o dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta dam i wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke fa a mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell! cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta arasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta auka gurin yin jinyarta ba, har inki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji. Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu. Kamar zasu yi dambe ita da Khala, saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da arfi kamar doki, da yar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa agowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin an uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas. Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar arama dake sai ba