Sashe 159
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
jikin ta. Kifa kanta tayi kan gwiwowinta tunawa da nasihar da mahaifinta ke yawan yi mata. "Ke kadai Allah Ya bani mamana, tun kina aramarki bani da burin daya wuce in inganta rayuwarki ki zama hafizar alkur'ani mai ilimin addini da zamani saboda inyi alfahari dake sannan ki zama abun kwatantace, Alhamdulillah cikin ikon Allah sai gashi kin cika min burina ko'ina zancenki ake duk in na shiga cikin jama'a sun dinga yabonki suna fadin ata malama ce hafiza mai cikar kamala da kamun kai ga kyautatama al'umma da son taimako, kowa yabon ki yakeyi, burin kowace mace tayi koyi da Aishatu bintu imam malik mace aya tamkar da dubu, Ummi nasihar da zan maki ko bayan ba raina kiji tsoron Allah, kada ki canza daga yadda nasanki, abun da zaki min wanda zaki biyani shi ne Ki karemun martabana da kimata a idon duniya, kada kiyi abun da zai zubda min mutuncina Aishana" Rushewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, a duk lokacin da ta tuna nasihar mahaifinta zuciyarta ba aramar karaya ta ke yi ba, tana jin tsanar rayuwar data aukarwa kanta, tana mai danasanin abun da yayi silar rabuwarta da mahaifinta, saboda bata da abu mafi soyuwa da ya wuce shi a duniyar nan, kai duk wani gata da ya zata samu agurin ubanta ta samu ninkin baninkin sa. tana jin ra in karya al awarin mahaifinta da ta yi na kare mashi martabarsa. kifa kanta tayi jikin pillow, ita kadai baiwar Allah babu mai lallashin ta. Ba halin ta bane, ba laifin ta ba ne, tana da ilmi tasan zina ba kyau ta kuma san hukuncin wanda ke aikatata amma meyasa takasa dainawa ko da tayi nufin ta tuba ta koma ga Allah? Tasha yun urin yin hakan amma aduk lokacin da big boss ya bu ace ta bata iya bijire ma shi. Ta yi kuka tamkar ranta zai fita kamar ar dambe ta dun ule hannayenta ta dinga bugun mattress kamar zatai hauka ta tsani abunda take aikatawa bata so ta mutu batare da yafiyar mahaifinta ba, kuma batason ta mutu tana aikata sabon Allah tana matukar jin tsoron makomarta. Ringing in wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta, fuskarta sharkaf da hawaye ta janyo wayar daga kan drawer ta duba sunan me kiranta. Maji da ina shine sunan daya bayyana akan screen din, kasa picking call din tayi saboda fushin da zuciyarta ke yi. Text message ne ya shigo on the top of the screen din wayar, cikin zuciya ta soma karanta abunda ya rubuta mata _"ummi, na tafi ba tare da nayi maki sallama ba, ki yi hakuri da hakan nasan zaki tashi da kewana, anyi min kiran gaggawane, ba dan nagaji da jin umin jikin ki ba, bazan iya misalta da in da kika jiyar dani ba, kin bani cikakkiyar gamsuwa da zan iya aukar kwanaki ban nemi matana ba, bazan iya biyanki ba Ummi, ki fadamin me zanyi maki don in faranta maki"_ Runtse idanunta tayi gam, siraran hawaye suka dinga shararowa kan kuncin ta.. "Ya Allah Ka cire min jarabar son bawan nan naka, Ina neman tsari da shi...." bata kare maganar ba kwatsam taji dirar motoci acikin gidan, a firgice ta jefar da wayar ta fa a kan mattress ta duro daga kan gadon, tafin hannunta a tallabe da bargon ta fa a toilet taja ofa ta datse, tana faman zare idanunta, sam ta manta da su Batool tasan bai wuci sune suka dawo gidan ba, abunda take jima fargaba kada wani ya shigo akinta tasan in har suka ga gadonta sai sun zargi wani abu saboda ya 6aci ba ka an ba. Cikin Takun sauri Chief Ya fa o Falon Ya nufi upstairs, agurguje taj da big guy suka biyo bayan shi, kwata kwata babu kwanciyar hankali akan fuskokin su damuwace arara saboda jami'an da suka tura su nemo Danish kusan awanni har yanzu ba wani labari, har tracking layin sa sukai a karshe suka gano location din da wayar take agida yabar ta baije da ita head quarter din ba, wannan dalilin ne yasa suka yanke shawarar su dawo gidan, watakil su gan shi. bai nufi ko'ina ba sai bedroom din Danish Yana isa bakin kofar yayi knocking in ta cike da fargaban kada su ki ganin shi. Jin shiru ba'a bu e kofar bane yasa shi tureta da hannun shi ya fa a ciki Yana haki saboda gudun daya sha, bazai iya tuna when last yayi irin shi ba. da matsanancin faduwar gaba yake bin dakin da kallo wayam babu kowa adakin dafe kan shi yayi da hannu aya idanunshi sun ka a jawur babban tashin hankalin shi Ina Danish yaje? ya zai yi da yan uwan shi? Me zai fada ma Uncle hateem idan ya kira yana son yin magana da shi"? "baya aciki ko"? muryar boss ce ta katse mashi zancen zucin shi Big guy duk ya rasa kuzarin shi Ya daura ma kanshi alhakin 6atan Danish saboda shi ne silar daya ja har ya yi zuciya Ya tafi, sai yanzu ya ke danasanin bata mashi rai da yayi ganin yadda ya aga hankalin chief Owais. "Taj bansan ya zanyi ba, baya nan, ya tafi, ya zanyi da raina, bana so na rasa yaron nan wallahi danasan abun da zai faru zuwan mu headquarter da ban tursasa mashi akan yabi mu ba..." dakyar yake magana saboda damuwar data cika zuciyar shi. jikinsu yayi mugun yin sanyi. Cikin raunin jiki ya dubi big guy"Omar, kaga abunda kaja min ko? Idan har yaron nan bai dawo gida nan ba, bazan yafe maka ba..." gaba aya ya rikice masu. "Sir kayi hakuri, na kar6i laifina, kuma nayi danasanin 6ata mashi rai da nayi, bada son raina ba ya 6ata min rai ne amma nayi maka alkawarin zanje in nemo shi duk in da ya shiga agarin nan..." yana fa an hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi azu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matu ar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi. Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba aya ya rasa warin gwiwar shi. "Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi" Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi "Ina sauran Yaran? Sun shigo?" bai are maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, aya bayan aya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su. "Sun shigo," "Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu" "Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba" Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan. "Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki" Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh. Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici. kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su. Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta. Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu "Unaisah! " dakyar ta bu e idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi "Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai aci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne" "Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su. Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi. "Allah Ya kare mana shi