Sashe 47
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 6 min read
kirasa a wayar sannan yace mashi yana son yaje har can joss din Ya bincika mashi inda suke rayuwa, saboda yana son sanin komai dangane da ita........ Atakaice big guy shine mutumin da ya siya ma angel piano da kayan zane, a ranar da sukaje kasuwa da su taj ta sanya masu rigima sai ansiya mata su gashi basu da kudi, ashe shine ke bi biyarsu duk wani motsinsu akan idanunsa, chief shine ya bada umarnin komai suke bukata yayi masu shi sannan bayaso su san cewa shine yake bibiyarsu har zuwa lokacin da zai dawo kasar. Duk wani abu da unaisah tayi sai big guy ya turama Cheif ta wayarshi, hakan ba karamin dadi yake yi mashi ba .... Kafin chief ya dawo Nigeria wannan tsautsayin ya ritsa da su tajuddeen wanda yayi silar 6acewarsu, hankalin big guy ba karamin tashi yayi ba, lokacin da labarin ya riske shi, har sai da yaji fargaban sanar da chief saboda yasan yadda ya walla fa rai akan kaunar yarinyar, gashi saura kwanaki kalilan ya rage mashi ya shigo nigeria, Yaci burin haduwa da ita tare da mahaifinta, Allah bai nufa ba . ... Dakyar Big guy ya sanar da shi abunda ke faruwa na 6acewarsu, tsabar tashin hankalin daya fuskanta na jin mummunan labarin har zazza6i sai da yayi, duk da haka bai karaya ba, yabar komai nashi, ya dawo nigeria bai sauka a abuja ba, kaitsaye ya sauka a joss, big guy ne yaje tarbo su a airport, tare da jami'ansu dayazo da su... A katafaren gidan da big guy din yake da zama suka sauka, dama chief ne ya biya kudin gidan a lokacin daya tura shi neman gidan su Angel. Kwana uku da zaman su agidan kafin suka fara nasu binciken, basu tsaya bata lokaci ba suka nemi alfarmar Inspector General of CID da ya damka masu case din su tajudeen a hannun su, tuni suka amince masu saboda sunsan hukumarsu ta musammance, duk wasu bayanai nasu tajudeen saida suka tura ma chief hada makullan gidajensu da suka kar6a. Muhsin yana aya daga cikin wadanda jami'an isod suka tuntu6a har gida suka kai mashi ziyara don jin cewa shi ayane daga cikin aminnan tajuddeen bayan sunyi mashi tambayoyi ya amsa masu wanda ya sani sai kuma sukace mashi ko bayan tafiyarsu idan yaji uriyar tajudeen ko abokinsa uzair yayi gaggawar sanar da su, saboda sunsan zasu iya tuntubarsa tun da shi amininsu ne, contact dinsu suka bashi kafin sukayi mashi sallama kun ji yadda akai har muhsin ya samu damar sanar da jami'an isod zancen zuwan tajuddeen ba tare da shi taj din Ya sani ba, saboda ya fahimci baya son kowa yasan da zamansa, shiyasa bai sanar da shi dangane da jami'an isod dake nemansa ba... Bayan chief owais ya kammala bashi labarin, saukko yayi daga kan sofa din Ya zube saman gwiwowinsa hawaye nata sintiri akan fuskarshi cikin sanyin murya yace"dama angel itace silar da kasan da zamana"? Muryarsa na rawa ya furta maganar, baisan sa'adda ya fashe da kuka ba, dama zuciyarsa a raunace take, "Allah sarki angel, ashe da rabon wata rana rashin jin ki ya yi min amfani...." kasa karasa maganar yayi, Da sauri chief ya ruko hannunsa acikin nashi, cikin sanyin murya yace"ka yi hakuri, ni banzo don na fama maka raunin dake acikin zuciyarka ba, nazo ne don na tallafi rayuwarka, idan har ka bani hadin kai nayi maka alkawarin zan yi iyakar bakin kokarina don ganin na baka kariya, na kuma tallafa maka da duk abunda nake da shi, Allah shine Ya hadani dakai ta silar yarka, Ina jinta tamkar kanwata, muhsin Ya sanar dani komai dangane da abun da ya faru dakai wanda yai silar bacewarku, in sha Allah mutanan da suka yi maku wannan aika aikar sai sunyi danasanin kasantuwarsu a doron duniyarnan......." kwantar masa da hankali chief ya cigaba da yi har saida yaga ya fara samun nutsuwa tukunna yace mashi zai jira ya yanke shawara...." ai tunkafin ya karasa maganar taj yace mashi ya amince, zai basu hadin kai, babu wata shawara da zaiyi, saboda shi bashi da mafita kwara su tallafa masa ya nemo yarsa..... Sunji dadin yadda taj ya amince masu batare da 6ata lokaci ba chief, Yace mashi su fara shiri zasu tafi abuja tare da shi, saboda Yana so ya sama masa muhallin da zai zauna akusa dashi sannan yace zai sama masa gurbi a hukumar su ta Isod bayan ya kar6i training dinsu, bayan tafiyarsu tajudeen abuja, rayuwarshi ta sauya, chief owais ya gatanta shi, a cikin gidansa ya ware masa part aya, inda zai zauna tare da danejo bayan haka ya bashi kyautar mota, cin su da suturarsu gaba aya shine yake daukar nauyin su, Kafin taj Ya fara kar6ar training din Isod sai da yafara auran danejo saboda yana son su ara kusanci da juna, bayason tayi kewar rashin wani nata. Big guy shi ne mutumin da ya shiga gidan Uzair, aranar da Aneelerh taje gidan har ya auke mata baby junaid, bayan haka sune jami'an sirrin da suka kaita gidansu har su ka yi mata tambayoyi da suka shafi 6acewar su Angel. Sauke numfashi yayi bayan ya gama basu labarin cikin sanyin murya yace _"Kunji yadda akai na tsira daga hannun mutanan da suka so rabani da rayuwana, hakika cheif yayi min halaccin da bazan ta6a mantawa ba, ya kyautata min, ya faranta min a lokacin da gwiwata ta sage na fidda rai da rayuwar duniyar nan, badan Allah ya addarar haduwata dashi ba, da yanzu bansan awani hali zan tsinci kaina ba"_ *Daga Al alamin Boss Bature *Littafin kurkukun addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*Buy bestselling books online 3196407426 First bank Bature Hafsat Muhammad, *bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268* Sponsored Post Tags Kurkukun Kaddara YOU MIGHT LIKE POST A COMMENT Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu. Previous Post Next Post GET IN TOUCH Facebook twitter YouTube Instagram Whatsapp SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content. Novels Elite SUBSCRIBE Posts Comments Links Post a Job LATEST POSTS ADVERT Novels Elite Copyright 2024 Novels Elite | All Rights Reserved DMCA.com Protection Status Disclaimer | Privacy Policy | Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home Kurkukun Kaddara Kurkukun Kaddara Takun Karshe Page 17 Complete Novels Elite Admin June 09, 2024 Sponsored Link Novels Elite English _ *~ BOSSLADIESWRITERS