← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 106 OF 247

Sashe 106

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

Wa anda suka kashe uzair zasu iya kashe ni idan sukaji ina raye!" cikin matsananciyar damuwa yayi mata maganar donta dauki abun serious...girgiza kai tayi"daddy bazan bari kowa ya sani ba, saboda bana so na rasa ka" "Koda wani ya nuna ya sanki ki ce bake bace, kinji"? aga mashi kai tayi... "Ko kinsan mutun kika ganshi kada ki tanka mashi ko ki nuna kin sanshi, tun da haryanzu bamu san wanene ya sadaukar dake ba!" Gefen fuskarta yashafa da hannun shi, ki fara shiri zuwa anjima da daddare zamu tafi" ta amsa mashi da toh, jan ta da fira ya farayi duk don ya faranta mata rai ko ta manta damuwar da take a ciki....... ______________________________ wuraren arfe biyar, A jere motocin su Alhaji musa suka kunno kai cikin asibitin, A parking space suka dakata, da sauri body guard din dake driving din sa ya fito ya bude mashi mota, gently ya fito, ya auki wankan shadda mai aukar ido, fuskarsa na sanye da mask, Iya idanunsa ne kadai zaka Iya gani, fitowa Alhaji ubaid Yayi daga motar, a tare suka nufi ciki, wani irin farin jini ne da shi duk inda ya gifta satar kallon shi ake, daga nurses har drs din kai harma da visitors. Duk da ya 6oye fuskarsa hakan bai hana wasu gane shi ba, cikin girmamawa likitoci ke gaishe da shi wasu kamar zasu durkusa asa, cikin isa Yake aga masu hannu batare daya furta magana ba.... Kafin su karasa ga medical room din, suka hango dr shureim tare da Aneelerh da zahra atsaye suna tattaunawa.... "Shureim"! Alhaji ubaid ne Ya kira sunan shi, kusan atare zahra da Aneelerh suka dago tare da kallon su...Rass Aneeleeh taji gabanta ya fa i ba ita ba hatta zahra saida taji wannan yanayin datayi tozali da Alhaji musa, Yayi matukar jan hankulansu... ura mashi ido Anila tayi, a lokacin dr shureim Ya karasa wurin su, kamar taso ta gane wanene, sai ta ga kamar uncle din benazir, bazata ta6a mantawa da an tahalikin nan ba, saboda kyautatawar da yayi masu tun da kuruciyarsu, kafin daga baya lokacin daya taka matsayi mai girma gaba aya suka daina jin duriyarshi. "Aunty Aneelerh wanene wannan"? "Kamar uncle din benazir, banga fuskar dakyau ba amma inaji araina shi ne. ." bata are maganar ba, su Alhaji ubaid suka karaso wurinsu, atare suka ha a baki wurin gaishe da su Alhaji ubaid ne kadai Ya amsa masu, da fara'a Yace"Aneelerh sannunku da kokari, Ya mai jikin"? Ita yake yi ma magana amma hankalin ta na akan Alhaji musa ya wani kau da ido kamar bai gan su ba. "Alhamdulillah daddy, Jikin nata da sauki ba kamar jiya ba" "Aneelerh ga Uncle musa ku gaisa ko baki gane shi ba..." dr shureim ne ya fa Murmushin yake ta saki"ina wuni..." asa asa da murya ya furta"lafiya..." zahra na gaishe shi ko kallo bata ishe shi ba, Ya wuce Ya nufi dakin Alhaji ubaid yabi bayan shi. jinjina kai zahra tayi aranta ta ayyana wannan wani irin mutunne? daga gani Yana da girman kai da izza. "Shureim ko dai Ya manta dani ne? Naga kamar bai gane ni ba, duk sai naji ba dadi..." Shiru shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin halin ko'in kulan da alhaji musa Ya nuna ma Aneelerh ba bayan ya santa farin sani... Murmushi ya anyi kafin Yace"bana tunanin ya ganeki" Ajiyar zuciya ta an sauke kafin suka cigaba da magana game da yarinyar da suke jiran zuwanta anjima... Lokacin da su Alhaji musa suka shiga dakin, Hajiya layla tana azaune kan prayer mat, hannunta ru e da cazbaha, kamshin turaren Alhaji musa ne Ya fara dakar hancinta kafin sallamarsu ta ja hankalin ta ga duban su, kamar taga wani mugun abu haka ta zabura ta mike tana kallon shi cike da mamakin ganin shi, saboda bata tsammanci zaizo ba tun da bai damu da benazir ba.... Tunda ya shigo idonshi na akan Benazir wadda ke kwance ta lumshe idanunta sai sambatu takeyi asa asa, kai tsaye ya nufi gaban gadon Ya zauna kan chair din dake fuskantarta "Sannu daughter, Ya jikin naki"? Ya fa a tare dakai hannu Ya shafa goshin ta, a firgice ta bude ido tana kallon shi, la66anta na kerma ta furta"Uncle! Daddy! ina babyna? Ina Angel dina, dan Allah ku nemo min taj ya kawo min babyna" Lumshe ido Alhaji musa yai kafin a hankali Ya furta"calm down your mind, zansa a nemo maki ita, but ki fara kwantar da hankalin ki" rurruke hannunshi tayi acikin nata"dan Allah ku kawo min ata da mijina, uncle ku taimaka min kada na mutu ban gansu ba...." tun shigowar shi bai dago Ya kalli hajiya layla ba, kamar babu ita adakin, wato yafi karfin yayi mata magana. Ita ko tayi tsaye tana kallon ikon Allah, sam batayi farin cikin zuwan shi ba, gani take kamar ba alkhairi ne Ya kawo shi ba... Gyaran murya Alhaji ubaid yayi mata "Layla ya jikin nata"? "Da sauki, mun samu taci abinci har wanka na taimaka mata tayi" "Ya ake ciki game da yarinyar da Aneelerh zata kawo"? "Sai zuwa dare zata zo asibitin" "Allah Ya kawota lafiya, amma iyayenta ba su nemi komai ba"? "Sai dai sunzo zamuji" ajiyar zuciya yadan sauke "Ba kiga musa ba ne? Naga baku gaisa ba" ya fada tare da nuna shi da hannu... Harara ta watsa mashi kafin tace"ay shi yakamata ya fara yi min magana bani ba, sai kace dai Nina tursasa mashi yazo asibitin"? gaba daya maganganun da suke tattaunawa akan kunnansa ko ajikinsa. Sun an jima kafin ya mi e Alhaji ubaid Yabi bayansa suka fito daga dakin Sai da suka fara zuwa office din likitan dake kula da ita don jin karin bayani dangane da lafiyarta, kafin suka fuce daga asibitin. _________________________________ Wunin ranar Danish bai le o ko kofar dakin sa ba, babu wanda Yasan halin da yake a ciki, kamar yadda ita ma ta killace kanta adaki, wuni tayi kudundune cikin bargo lokacin sallah ka ai ke tada ta, tuni zazza6i ya lullu6eta jikin ta har kerma yakeyi kamar zatai hauka saboda azabar ra in da zuciyarta keyi mata, tayi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, danish ya dasa mata tsanar shi a zuciyarta, ko sunan shi bata son ambato, hauka tadinga tana bubbuga mattress da hannayenta kamar yar dambe duk ta hargitse dakin a karshe ta fashe da kuka tana fadin"ka karya min zuciya my man, na tsane ka! Bana son ka! Bana son ganin ka! Ban ta6a tsammanin zaka iya cutar da rayuwata ba! Meyasa kayi min haka? ..." tajima tana haukanta ita kadai kamar zata zauce. Wuraren arfe takwas na dare, taj ya kirata awaya yace ta shirya ta same su a parking spot, jiki na rawa na shiga toilet, dama a kagare take data bar gidan kodan ta nisanta da shi, watakil ta samu relief din radadin da heart dinta keyi mata. Bayan ta fito shaf shaf ta shirya cikin abaya, ta dauko kaya kala uku ta cusa a backpack dinta, ta goya jakar abayanta, ta zura takalmanta kafin ta dauki wayarta, babu wanda Yasan da zancen tafiyarta, harta fuce daga gidan..... Cikin sauri take tafiya kamar zatayi tuntu6e, a parking space ta hango daddynta tsaye, ya sanya face mask a fuskarshi Kallo aya yayi mata ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa atattare da ita Baisan ya zaiyi da ita ba, taki fada masa damuwarta, bu e mata murfin motar yayi, wani sanyayyan kamshin turarene Ya daki hancinta, nan take ta gane kamshin wanene da sauri ta dago ta kalli daddyn nata Murmushi ya sakar mata kafin yace"ki shiga mana" "Wanene a ciki"? Ta jafe mashi tambayar "Chief ne, tare da shi zamu tafi" jim ta anyi kafin ta kutsa kai ciki, har saida gabanta ya dan fadi lokacin da ta sauke idonta a kanshi, yana daga zaune ya auki wankan shadda blue sky tayi bala'en yi mashi kyau, laptop dinsa ce akan laps dinsa, ya dan lumshe idanunshi.... Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin wani irin sanyi acikin zuciyarta. Sai da ta zauna gefen shi kafin ta samu kwarin gwiwar yi mashi sallama tare da gaishe da shi... Calmly ya amsa mata... Nutsuwa tayi idon akan glass din motar da bai karasa rufewa ba, tana iya hangen filin gidan.... "Zamu Iya tafiya" chief ne Ya fa a, security din dake zaune a driver seat Ya tada motar, A hankali Ya fara driving dinsu, motarsu big guy tana abiye da bayansu su biyu aciki tare da daddynta, sai motar jami'ansu dake abiye da su.... Lokacin da motocin suka haura kan titi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta, ta lumshe idanunta, bakomai take tariyowa ba face abunda Ya faru tsakanin ta da danish, tayi fatan ace mafarkine ba gaske ba..........bata san sa'adda hawaye suka gangaro takan kuncin ta ba, kwata kwata ta manta da chief acikin motar, Ranta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta bu e idanunta wa anda suka ka a jawur, karaf idanunsu suka shiga cikin na juna..... Daga ita har shi sun kasa sarrafa kansu, wani irin kallo suke bin juna da shi mai wuyar fassaruwa amshin turarenshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba..." Tsananin tausayinta ne Ya kama shi, har yau yana mai mamakin kananun shekarunta da kuma irin wahalhalun rayuwar da ta fuskanta, shi tunda yataso rayuwarsa baisan menene wahala ko rashi ba. "I don't want to see your tears..." DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE *Mu ha u Jibi, Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440* Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS Previous Post Next Post GET IN TOUCH SUBSCRIBE US OPINION FACEBOOK COMMENTS CATEGORIES Africa Al'adu Alkamawa Article Blogger Tips Economy Education Entertainment Gist Gyaran-Jiki Health (13) Jikar Iya (11) Kimiya Kiwon Lafiya (54) Kukan Zuci Kwalliya Labaru (23) Lifestyle Ma'aurata News (300) Nigeria Noma Opinion Picture Politics (15) Profile Ramadan Ramadan Tafsair Siyasa Sports (72) Tarihi Technology Tips Video YouTube Zain Abeed Zamantakewa Novels Elite Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be
Chapter 106 · 0% Book details