← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 147 OF 247

Sashe 147

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

tafiyar shi ba, saboda yarinyar nan mai kama da shi ta tsaya mashi aranshi. Akan idon Benazir motar dr shureim ta fuce daga gidan, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da du ar da kanta asa, damuwa ce cunkushe a cikin zuciyarta, ga dai yarta Allah ya nuna mata da ranta da lafiyarta kuma tayi farin ciki mara misaltuwa sai dai bata jin zata samun sukuni da kwanciyar hankali in har taj bai yafe mata ba, har yanzu tana son mijinta kuma bata jin zata iya rayuwa da wani a namiji a duniyar nan in ba shi ba, zurfin tunani ta shiga da ace tun farko da ya aureta sunyi zaman lafiya zai iya yi mata uziri amma Yanzu koda yaji cewa Asiri akai mata ta gudu tasan bazai ta6a yarda ba saboda yasan wacece ita Cikin karyayyar murya ta furta"Halina ne Yaja min, Ni na ja ma kaina..." batai aune ba taji safkar hawaye kan kuncin ta, da sauri ta sanya tafin hannu ta share wallar, kafin ta juya ta nufi hanyar koma wa sitting room din tana ta an waige waige cike da sa ran zata ga 6ullowar taj sai dai har ta shiga babu shi babu alamar shi... __________Ummin America Futowa tay daga bedroom din ta jikinta sanye da bubu gown ta material, tay rolling akanta, flat shoes ne a kafarta, matsawa tay gaban handrail ta dafa tana kallon downstairs, A falo ta hango su gaba ayan su banda mutun uku, kowan nan su yana azaune kan rug sun ha a kai suna rubutu a cikin notebooks din su, Sajeed ne kadai ya zauna kan sofa da alama shi ke koya masu rubutun. Zura hannayenta tay acikin aljihun rigarta, ta nufi stairs cikin nutsuwa take taka matakalar ta sauko down ta nufe su babu wanda Ya lura da ita a cikin su har sai da tay masu gyaran murya tukunna suka dago da kai suka kalle ta har suna ha a baki gurin furta"Aunty Ummi zo ki ga Rubutun mu, Ki za6i nawa yafi kyau" kusan atare suke mike tare da kewayeta kowa Ya mi a mata notebook din shi. in kar6a tay gudun kada ta ha a rigima kallo aya da tai ma rubutun su sai da taji gaban ta ya fa i ganin wani jagwalgwalo, a fakaice ta kalli sajeed karaf suka ha a ido da juna da sauri Ya kumshe dariya yai mata alamar ta duba mana. "Aunty ummi nawa zaki fara dubawa, nafi su abun kirki" Jemimah ce ke rokon ta, kar6ar book din tay tare da duba rubutunta itace ke yin rubutu shigen na thailand ka rasa ta yadda take jagwalgwala shi "Aunty ummi in kin gama duba nata saura nawa" acewar Azeeza, Deeja tace"wlh na riga ki nawa zata duba" kamar zasu sanya mata rigima. Jinjina kai ta yi"Jemimah Kinyi ari ki dage kin ji, idan kika maida hankali har kyauta zanyi maki" uban tsalle ta daka na murna hada yi ma Azeeza gwalo ta kar6i notebook dinta tana ta murna "Muga naki azeeza' mika mata tay aranta ta ayyana tab lallai wlh da a school suka rubuta Iya shegen nan, jakkin duka zasu ci' amma a fili sai ta an murmusa tace"kema kinyi kokari, Ki ara himma" dadine Ya lullu6e azeeza ta kar6i book dinta ta juya ta nufi jemimah. Saurari Littafin >>>>Kurkukun addara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ora. aya bayan aya saida ummi ta duba notebooks din Har wara Naufal Ya iya rubuta ba laifi tayi mamaki har saida ta tambaye shi ya akai yafi su iyawa, Da hannu ya nuna mata Sajeed"kullum A aki kafin mu kwanta bacci, Shi yake koya min rubutu da karatu..." jinjina kai tay"Sajeed sannu da kokari, amma yakamata suma sauran ka dage da koya masu kamar yadda kake koya ma naufal" amsa mata yai da toh. Deeja sai ha e rai take don ba'a yabi nata ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"rubutun ma bazan ara yi ba" ta fa a tana kokarin keta littafin da sauri Haris Ya ru e hannunta"wayace maki rubutun baiyi kyau ba, ay naki yafi na kowa" kwa6e fuska tay tare da kallon Aunty Ummi tana faman zum6ura baki tace"amma ayni baki yabi nawa ba ko" yar dariya ummi tay"oh wai saboda ni zaki keta littafin, toh kiyi hakuri mantawa nayi amma naki yafi na kowa" washe baki tay har taji dadi.. "Ni rubutun ma yai kyau ko kar yayi ba damuwa ta bace, indai ba za'a hanani cin abinci ba" ta fa a tana hura hanci, gaba aya suka sanya dariya, girgiza kai Ummi tay"Allah ya shiryeki foodie, ke dai indai zaki samu abinci baki da sauran damuwa" aga mata gira tay. Sarah da ta gama ha e rai wurga notebook dinta tay kan sofa ta juya zata tafi "Hey! Where are you going?' muryar ummi ce ta katse mata hanzarin ta, yamutsa fuska tay"nagaji da rubutunne zanje na kwanta" murmushi ummi tay"nasan me kike ma fushi don ban yabi rubutunki ba ko" girgiza kai tay"a'a kawai nagaji ne" daga yanayinta ummi ta fahimci zatai rawar kawai dama tana lura da ita, ta iya raina abu in baiyi mata ba. "Okey, kije ki kwanta ki huta, da anjima, da kaina zan koya maku rubutun" "Okay, thanks" ta fa a tare da juyawa ta nufi dakin su tana tafiya kamar zata balle tsabar tsawon ta har yanzu bata da iba. "Kuma idan kun gaji ku aje karatun, kwakwalwa tana bu atar hutu, amma fa dole ku dage ilmi yana da matu ar amfani, you have to endure and persist before you succeed." ta6e baki parvin tay"Allah aunty ummi da kin daina wahalar da kanki gurin yi mana bayani, bamu gane komai.." sakin baki tay sototo tana kallon parvin abun ban haushi abun dariya Rubina tace"nima Allah bani ganewa, Nifa nafison in kwanta inyi bacci ko inci abinci" kallon ta ummi tay Hibba tace"dama girki kika koya mana, da yafi, kin ga sai mu dinga girka abun da ran mu yake so" Harara ta an watsa mata"hauka nake in kai ku kitchen da sunan zan koya maku girki? A haka? Ku fara samun ilmin kafin in yi tunanin koya maku girkin" Hannah tace"wai komai saida ilmi, to a jika abamu musha sai mu haddace" tuntsirewa ummi tay da dariya, Sajeed dake sauraron su baisan sa'adda ya fashe da dariya ba "Aunty ummi dama kin daina wahalar da kanki gurin yi masu bayani, ba zasu fahince ki ba, har yanzu da sauran su" acewar Sajeed, tsagaitawa tay da yin dariya cike da nishadi tace"wani lokacin kamar masu hankali, wani lokacin kuma wlh kamar in hada ku da tsumagiya inta jibga" dariya sukayi gaba dayan su "Ina Unaisah da Batool? Banga gifcinsu ba, ko suna adaki ne"? Hawwa tace"basa nan tun dazu muka je neman Unaisah don ta bamu notebooks dinmu mu yi karatu bamu ganta ba kuma bata a toilet sai dai muka auko books din" "Kun duba ko'ina baku gan su ba? Ko dai sun je dakin Danish ne"? Haris Yace danish Yana atare da chief suna karatu bana tunanin sun je dakinsa" "To Ina suka je ne"? Ta fada tana kallon su Yasmin tace"kila sun fita waje ko dai muje mu nemo su"! Shiru ummi tay bata amsa ba tunani tay ko dai sun shiga bangaren daddyn unaisah ne"? Da sauri ta zaro wayarta daga aljihu ta lalubo contact din unaisah ta kira layinta tana ta kira ba'a picking har ta katse almost 3 times Yanke shawarar kiran taj tay har wayar ta are ringing ba'a aga ba "Nafi tunanin suna acikin gidan nan, ku tayani neman su" amsa mata su kai toh, da gudu wasu suka nufi bangaren hagu wasu dama Suka fara bin sako da lungu suna neman su. _________________________ Bayan dr shureim ya isa gidan, a hanzarce Ya fito daga motar Ya nufi Cikin main falo Yana ta sauri saboda Hankalinsa Ya tashi Da halin da Zeenatu take a ciki Ya kosa Ya ganta ko hankalinsa ya kwanta har ya kusa fita daga falon muryar Tani ta katse mashi hanzarin shi. "Shureim har an dawo" dakatawa yai tare da kallonta"Tani na same ku lafiya" da fara'a tace"lafiyalou, " "Ina mutanan gidan"? "Hajiya layla tana a aki, zeenatu kuma bata jin dadi amma na kira daddynta awaya na fa a mashi, Yanzu haka ya turo family doc din su Yana a akin Yana duba lafiyarta..." tun kafin Ta are maganar dr shureim Ya furta"Ya Salam! Mami tasan bata da lafiya"? Girgiza kai Tani tay"dana je fa a mata na iske tana bacci shiyasa ban tadata ba" Hankalin shi atashe Yayi saurin nufar upstairs, azafafe Yake taka stairs din harya haura second floor, Yana isa gaban ofar akin yajiyo wata Murya irin ta giggan tantira daga cikin akin "Don't waste My time, idan baki bani ha in kai ba, zan kira daddyn naki awaya in fada mashi," shesshekar kukan zeenatu yajiyo tana fadin"ni wlh banso, ka kyaleni, ka kyaleni nace banaso" zuciya da sake sake ta raya mashi wani mugun abunne ke shirin faruwa, gabanshi na faduwa Ya ture ofar akin da hannu kai tsaye idanun shi suka sauka akan jibgegen katon nan Ya haye kan gadonta yayi mata rumfa da gabjejen kirjin shi ta ma ure kanta jikin headboard, jikinta sai kakarwa yake yatsun hannunta dana kafafuwanta sai kerma suke, ta rufe kirjinta da tafukanta, Yar rigar wanka ce a jikinta da bata wuci gwiwar kafarta ba, sumar kanta duk ta rufe fukarta....wani irin kishi ne Ya rufe dr shureim baisan sa'adda yai kukan kura daga inda yake yai wani waran taku Ya dam i kafar dr mark A firgice Zeenatu ta ware idanunta akan fuskarshi la66anta sai kerma suke. Dr mark ko ajikin shi, Fuskarshi a murtuke ba annuri Ya dubi Dr shureim da ya ruke kafar shi. A gadarance yace"malam Lafiya ka ru e min afa" ya fa a yana bin shi da wani kaskantaccen kallo Rai a6ace dr shureim yace"uban me kake yi akan gadon ta"? ta6e baki dr mark yai tare da nuna mashi Syringe in hannun shi"Ubanta ne Ya kira ni don in duba lafiyar yar sa, ko kana da Ja ne"
Chapter 147 · 0% Book details