Sashe 235
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne ta shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu fa a, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya aure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji Gaba aya suka bita da kallo yayin da take arasa saukowa daga kan stairs in ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta. cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"! Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir. Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."? Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita. Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta. Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."! Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwa aita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana arasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka ha a kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su. "Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya fa a yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna. Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi. Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi .. Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba. Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ara girma ya kuma ara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da. Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya fa a idanunsa cike tab da kwalla. "Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu. Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers" Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji "Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla. Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?" Gabansu ne Ya fa i rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta. Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba. "Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...." bata are maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aru e ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru. "Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla. Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata.. "Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"? Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani. Gaba daya maganganun Aisha sun ru a Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan aya, ya rasa gane inda suka dosa. Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan