← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 165 OF 247

Sashe 165

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

abun da za'aji kunya..." kallon juna su ka yi, duk sun kagara da su ga su wanene... Shigowa falon Taj yayi hannayen shi zube cikin aljihun jallabiyar shi, kwata kwata babu annuri akan fuskarshi kamar wanda aka fada ma sakon mutuwar shi. Kwata kwata basu lura da shi ba har saida Javed Ya ambaci sunan shi kafin hankalinsu yakai gare shi, Unaisah na ganin shi ta nufe shi da sauri donta fada mashi abun farin cikin daya faru na bayyanar Danish azatonta bai sani ba. tana karasowa Taj yayi saurin kauce mata kamar bai ganta ba, fuskarshi a ha e ya nufi su Naufal Ya mika masu hannu daya bayan daya ya yi musabaha da mazan kafin Ya maida hankali kan su sarah da fara'a yake amsa masu gaisuwar da su ke yi mashi. gaba aya ta gaza aga kafafunta saboda faduwar gaban da taji, hankalin ta ya tashi da ganin abun da daddynta yayi mata, kokwanto tayi anya ya ganta? Ko dai bai lura da ita bane? In ba haka meyasa zai shareta ya nufi yan uwanta? ta sanyawa ranta cewa bai ganta bane saboda bai ta6a mata hakan ba, cike da kwarin gwiwa ta nufe shi a lokacin yana tsaye, ta fada bayan shi ta rungume shi tana fadin"daddy ni baka ganni ba ne..." rai a an bace ya furta"unaisah ki sake ni, tun kafin na bata maki rai" ya fada tare da janye hannunta Ya jefar da shi gefe aya. e ta kalli fuskar shi, ya ha e rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne. Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su Duk da haka bata kawo komai aranta ba, ta kuma cewa"daddy, chief ya fada maka an ga danish a cikin toilet dinsa..." banza yayi da ita tamkar baiji maganar ba, hakan ba karamin aga mata hankali yai ba. komawa tayi cikin yan uwanta ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba. [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________ ..." bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi an uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun auke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"! A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu ha in kai.... A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi.. Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba" Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya" jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba aya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala. "Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am.. "What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"! murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba" murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba. "In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara" da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin fa in"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa" kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi "Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce. Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman ya i, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!. Chief ya aura da cewa"nayi alkawarin bazan ara takura ma Danish game da zancen kurkukun addara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun ha in kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...." yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi "Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun agara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu fa a masu" ya fa a yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ari" Dukar da kanshi asa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun ayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya. yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din" big guy yace"muna jiranka" mi ewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan. Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska. Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish. "Inason yin magana dakai" ya fa a tare da juyawa ya nufi upstairs sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun" amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana. "Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai wa anda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba. Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su" bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so" "Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..." duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.." bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane. Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare daya cika burin shi akan Unaisah ba gya a kai yai da alama ya kamo bakin zaren saukowa down yayi bai ganta a falon ba, kaitsaye ya wuce bedroom din su, yayi knocking almost 3
Chapter 165 · 0% Book details