← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 202 OF 247

Sashe 202

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

acikin ranta "Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta" Lokaci aya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta..... Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"? ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga... Lokaci aya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba *Bayan Wani Lokaci* *OIH* Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su. A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun ka a jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta. Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital) gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta. Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya.. Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya. Hankalin su Ya tashi matu a sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba. (Get well Soon Unaisah Angel) *DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE *Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440* [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ~<><><><><><><><><><><><><><><> ~__________________________________~ gajiya tafari yi da tsayuwa charging kwata kwata baya sauri, zama tayi gefen gadon su ta dan fara gyangyadi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba da ita. A hankali ya ke saukowa down ya zuba hannayensa Cikin aljihun wondon baccin sa, sam ya kasa runtsawa saboda tunanin a wani hali Unaisah take a ciki? Ta yi bacci ko idonta biyu? Ya damu sosai akan ciwonta, direct ya nufi bedroom dinsu Yana gab da zai shiga ya jiyo shesshekan kukan ta kasa kasa. Almost 3 times yana kwa a sallama shiru tare da knocking door din, ba'a amsa mashi ba Har zai juya sai kuma ya kasa jurewa saboda baya son damuwarta ga kuma kukan da ya ji ta na yi. A hankali ya tura kofar akin Ya shiga da sallama abakin shi, babu wadataccen haske a dakin sai na bedside lamp da suka bari a kunne, Batool ya hango a kwance kan gadonsu tana ta sharar baccin ta ita kadai abun ta. Wurga eye balls dinsa yai saitin inda yake jiyo shesshekar kukanta, wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi ganinta a cikin prayer corner tana a zaune kan prayer mat, jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ruke da prayer beads tana lazami, yayin da idanunta ke akan qur'anic stand din data bu tabbas tajiyo kamshin turaren Chief sai dai bata kawo aranta cewa shine ba kuma kwata kwata ba ta ji motsin shigowar mutum ba saboda tayi nisa a cikin ibadarta. Unaisah ta yi Namijin kokari ba lafiya gare ta ba, amma saboda ta nema masa rahama gurin Allah yasa ta hana idonta bacci ta tsaya tsayin daka don ganin tayi masa addu'a dama alkawari ta daukar masa zata raba daren ta biyu rabi ta yi bacci rabi ta yi addu'a, samun masoyi mai sonka tsakani da Allah da zai iya yi maka addu'a batare da sanin ka ba zaiyi wuya a duniyar nan. Hakika ta burge shi sosai, Har ya zagayo ta gabanta bata lura da shi ba, saboda ta an lumshe idanunta, dogayen eye lashes din ta sun ji u da ruwan hawayenta. Kyakkyawar fuskarta ta 6aci da hawayen ta, aga hannayenta tayi sama Cikin harshen larabci ta fara karanta addu'o'i duk akan Danish dinta. Lumshe idanun shi yai a hankali ya sake bude su kan fuskarta, ya jinjinama irin kaunar da take ma Danish yayi fatan ace shi ya samu soyayyarta, saboda samun mace tagari irin ta zaiyi wuya a fadin duniyar nan, yarinyar da zata iya tashi in the middle of the Night tayi nafilfili don ta yi maka addu'a Omg A hankali Ya zukunna ta gefen ta, Ya zuba mata lumsassun idanun shi masu auke da bacci. Bakomai yake kallo ba fa ce eye lashes dinta da soft lips dinta dake kerma sun jiku da hawayen ta sometime har tongue take zurowa ta lashe su baisan ya akai ya tsinci kan shi da kallon ta ba. A hankali ya mayar da eye balls dinsa kan kwantaccen gashin forehead dinta dark brown ya nannade gwanin ban sha'awa kai komai nata abun ban sha'awa ne. Kasa yi mata magana yai cos yai tunanin she may feel uncomfortable if she sees him in front of her. Slowly ya mi e tare da juyawa ya nufi hanyar fucewa daga dakin Kamar daga sama yajiyo muryarta a cikin kunnan shi"Wanene" dan dakatawa yai ba tare da ya juya ba, Zumbur ta mike gabanta na faduwa cos tajiyo motsin tafiyar shi. waro idanu waje tay lokacin da tay arba da faffadan bayan shi, wlh sai taga kamar Danish ne yanayin tsayuwarsa banbancin Danish yafi sa tsayi da kuma doguwar sumar kai, uwa uba launin fatarsu ba daya ba. "Wanene"? Ta ara fa a cike da fargaba, gudun kada ya tsoratar da ita yasa shi juyowa a hankali suka fuskanci juna tana ganin chief tay saurin share hawayen ta saboda ya hanata kuka, tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin a cikin dakinsu, arude ta furta"barka da dare" ya fahimci rudani dake akan fuskarta hakan yasa shi cewa"I'm sorry na shigo dakin ku batare da izninku ba, na fito ina zagayawane najiyo shesshekar kukanki, Hankali ya tashi sau uku ina yin sallama ba'a amsa min ba, har knocking nayi shiru shiyasa na yanke shawarar shigowa ciki amma ba halina bane" Cikin sanyin murya ta furta"na fahimce ka, kuma nagode da kulawarka agare ni, ka damu dani sosai" Sam taki bari su hada ido tun kallon farko da tay mashi ta kawar da idanun ta. "Kin manta sharaddun da dr ya gindaya maki? I thought I would find you sleeping, although you are doing good thing, but you should continue resting until you've fully recovered, ban hana ki masa addu'a ba, zaki iya yi masa addu'a aduk lokacin da kikai sallah, amma yanzu dare ne Unaisah" with respect ta amsa mashi da toh. Shiru suka anyi na wani lokaci, takun tafiyarsa taji da sauri ta dago matsowa yai dab da ita.. Ta sadda kanta kasa tana dan jin faduwar gaba. In a cool voice yace"a ranar da mu ka kwana a sansanin mu, Danish ya nemi in yi masa alkawarin ko bayan ransa In kula da rayuwarki data mahaifinki da yan uwanki, and I vowed to fulfill his request" jin wannan maganar yasata kusa fashewa da kuka jikinta ya kama kerma. "Ban fada maki don in fama maki raunin dake a cikin zuciyarki ba, sai don inaso ki taimakamin Unaisah, Ki bani hadinkai gurin ganin na cika masa alkawarinsa, in har kika bani dama duk da ina shiga busy saboda aiki zan yi kokarin ware mana lokacin da zamu dinga ganawa da juna, in sha Allah I'll support you in overcoming the pain that's troubling you." dakyar ya are maganin ganin yadda hawaye ke yar tseral kan kuncinta aranta ta ayyana wata irin kauna Danish yakeyi mata? Ya Ilahi, Shi damuwar shi wanda zai kula da rayuwarsu in baya nan wayyo Allah hakika tayi babban rashi arayuwar ta. batai aune ba taji safkar yatsun chief kan fuskarta gently ya soma share mata hawayen ta. Muryarsa tamkar ta me yin ra a ya furta"If you give me a chance, I will replace him, despite knowing I may never fully replace him in your heart" ya an dakata yana mayar da numfashi, ta nutsu tana sauraron shi. "Na riga shi sanin ki amma ya riga ni haduwa dake, nasan da ace tun lokacin na
Chapter 202 · 0% Book details