Sashe 141
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
jikin naki"? "Naji sauki sosai" shiru sukayi fargaban shi kada tace yakaita gurin azeezaty ya san halinta in rigimarta ta motsa. "Lafiya? Naga kamar kinyi shirin zuwa anguwa,"? Murmushi ta sakar mashi "Eh, gidan su anila nake son zuwa, jiya munyi waya da ita, ta fadamun yaronta baida lafiya, ashe shiyasa bata kira ta yi min ya jiki ba.." tun da tafara magana shureim ke kallonta gani yake kamar karya ta shirga mashi don ta samu yakaita gidan. Ganin irin kallon da ya ke yi mata ne yasa tai saurin furta"wallahi dagaske nakeyi maka, bari in kira maka anilan ku yi magana" tay maganar tare da kai hannu ta bu e purse dinta, ta curo wayar ta kira layin anila tana fara ringing, ta mi a mashi fuskarta dauke da murmushi. "Assalamu alaikum, Anila barka da safiya"! On the other hand tace"ya shureim ina kwana ka tashi lafiya? Ya jikin benazir din? Wlh junaid ba lafiya shiyasa ban samu na kira naji ya ku ke ba ashe ma har an sallame ta" ajiyar zuciya ya dan sauke. "Lafiyalou anila, Benazir taji sauki, itace ma ta kira min ke, tace tana so tazo duba junaid, ubangiji Allah ya bashi lafiya, in sha Allah yanzu zamu zo" "Allah Ya kawo ku lafiya, ngde" sallama sukayi ya mika ma Benazir wayar "Ki bari sai anjima muje, yayi wuri yanzu" girgiza kai tay ha i da aure fuskarta"ya shureim itafa ta nuna tana son inje yanzu" "Naji, amma dan Allah idan mu ka je gidan, kada ki yi mata maganar yarinyar nan Azeezaty, nasan hada hakan yasa kike zumudin zuwa gidansu, kiyi hakuri Benazir yarinyar nan ba yarki bace idan kika sa hakuri in sha Allah kema zaki ga taki yar.." dukar dakai kasa tay, idanunta suka ciko da kwalla. "Kiyi hakuri idan maganata batayi maki dadi ba" girgiza kai tay'na fahimce ka, in sha Allah bazanyi mata maganarta ba, ay na hakura tuntuni" ajiyar zuciya ya sauke "haka nakeson ji, Kin fada masu mommy zaki fita" girgiza kai tay"a'a yanzu in zamu tafi sai mu gaya masu" amsa mata yai da toh Kafin ya juya ya shiga ciki ya auko carkey dinsa Ya fito suka jera atare suka nufi dining room, mutanan gidan duk suna azaune suna yin breakfast, mutumin ya ha e fuska sai shan kamshi yake kamar iska tana mashi wari, abincin ma da aji da izza yake cin shi tamkar baya son tauna shi.. A fakaice hajiya layla take aika mashi harara kamar zata rufe shi da bugu, shi dai Alhaji ubaid ya nutsu Yana cin abin cin shi, yayin da zeenatu take fuskantar mommyn ta, sam takasa cin abincin ruwan lemu kawai take ta aikin durawa cikin ta, hankalinta da tunaninta suna akan Azeezaty, jiya har mafarkinta tayi, bata da burin daya wuce su ha u da ita, don ta tambayeta wacece Unaizah mai kama da ita Takun tafiyar su shureim ne yaja hankulansu ga duban su, Bayan sun karaso cikin girmamawa suka gaishe da su kowa ya amsa masu banda Alhaji musa hakan bai dame su ba, sun riga sun dan halinshi mami ta dube su"ina zuwa haka shureim"? "Zamuje gidansu anila ne, yaronta baya jin dadi" hajiya sarah tace"Allah sarki, itace kawar benazir wadda suke zuwa asibiti dubata ko"? Benazir ta amsa mata da eh"Allah ya bashi lafiya" mami tace"ay da kun fada min tun dazu dana shirya mun tafi atare, amma idan kun isa gidan ku kirani dan Allah" suka amsa mata da toh, Alhaji ubaid yace"ku gaishe min da mutanan gidan, ace ma anila inayi mata yamai jiki, Allah ya bashi lafiya, idan na samu lokaci zan shigo gidan" ya amsa mashi toh. "Ya shureim zan biku dan Allah" zeenatu ce tayi maganar, har zata mi e Alhaji musa ya jefa ta da wani kallo tuni tasha jinin jikin ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah daddy ka bari su tafi dani, mommy kice ya shureim ya tafi dani inaso in bi su" atsawace Alhaji musa ya furta"karki kuskura ki ara magana! " a tsorace taja baki tayi shiru, idanunta akan fuskar shureim dake kallon ta, wani irin tausayinta ne ya kama shi, yana so su tafi da ita sai dai yasan daddynta bazai barta ba. "Musa ka barsu su tafi da ita tunda tana son zuwa..." Alhaji ubaid ne yai maganar, Banza yayi da shi tamkar baiji abunda yace ba, hakan ya sosa zuciyar Alhaji ubaid musamman layla ranta ya 6aci, harara ta galla mashi akan idonshi, ita day hajiya sarah tayi shiru batace komai ba. "Shureim ku tafi, Allah ya tsare hanya.." ta fada tare da yi masu alamar su je, ruko hannun Benazir yayi suka kama hanyar fita daga falon yana jiyo sautin shesshekar kukan zeenatu, har waiwayowa yayi sai kallon shi takeyi duk sai yaji ba dadi amma idan ya tuna abunda alhaji musa ya fada mashi sai yaji kwara zamanta agidan duk da shi baiga amfanin hakan ba saboda yayi imanin cewa Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake. Har suka shiga mota, bai daina tunanin zeenatu ba, ta tsaya mashi aranshi yana jin tausayin rayuwarta Tsawon mintina kafin suka karaso anguwarsu anila, motarsu ta na shigowa layin gidan suka hango anila atsaye cikin shiga ta abaya fara ta goya baby junaid abayanta, hannunta ru e da wayarta.. Tunkafin su karaso ta aga masu hannu alamar su tsayar da motar, agabanta yayi parking, ta nufi backseat ta bu e ta shiga ta zauna kafin ta warware goyan junaid ta kwantar da shi kan kirjin ta. Dr shureum yayi zaton gidan zasu shiga har zai tada mota benazir ta ru e hannun shi ya dubeta da mamaki"ba ciki zamu shiga ba, Anila ki fa a masa inda zamuje" Cikin sanyin murya tace"ya shureim obie estate zaka kaimu" aru e yake kallonsu da mamaki yace "Bangane ba, me zakuyi acan? Anila fada mun ina fata dai ba gidan iyayen yarinyar nan zakuje ba"? "Ya shureim muje kawai, zamuyi maka bayani daga baya, wani abune mai mahimmanci zai kai mu can" bai musa masu ba, yayi reverse ya mi i hanyar fita daga unguwar "Anila ya jikin junaid din! Ko dai shima duk plan dinku ne"? Murmushi suka saki, Anila tace"a'a ba plan bane, dagaske baida lafiya, amma jikin nashi da sau i.." "Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin. Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen. Tags Kurkukun Kaddara YOU MAY LIKE THESE POSTS [14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite Home Kurkukun Kaddara Kurkukun addara Takun arshe chapter 43 Complete by Boss Bature Novels Elite Admin September 05, 2024 Sponsored Link Takun arshe DAGA AL ALAMIN BOSS BATURE Bayan ta samu ta lalla6a junaid ya koma bacci, tun da motarsu ta haura kan titi suke ta satar kallon juna tsakaninta da Benazir ta cikin mirror din motar kamar wasu munafukai, kwata kwata hankalin dr shureim baya akansu ya tattara nutsuwarsa akan driving din da yakeyi, hakanan ranshi ya raya mashi ya dubi fuskar Benazir, ta wutsiyar idanun shi ya ke kallon ta adaidai lokaci sun kura ma juna ido ita da Anila da alamun rashin gaskiya atattare da su, duk dagowar da zaiyi sai ya kama su suna kallon juna ta mirror, gyaran murya yayi masu da sauri suka dube shi. "Ban yarda daku ba! Ku fa amin gaskiya meke faruwa ne? Meyasa kuke satar kallon juna ta mirror? Ina fa lura da duk wani motsinku acikin motar nan, kamar baku da gaskiya, ku ji tsoron Allah ku sanar dani abun da kuke boye min"! Shiru su ka yi suna ta an kame kame an rasa me bude baki ya bashi amsa duk sun sha jinin jikin su. "Da ku nake magana? Me zamuje yi a obie estate? In har baku fadamin ba zan dakata da yin driving din..." fuskar shi adaure yayi maganar batare daya kalle su ba, kallon juna suka sake yi ta mirror, kafin su yanke shawara da junan su dr shureim ya yi parking din motar a gefen titi Ya kashe ta tare da jingina kanshi jikin headrest. "In har ba zaku fadamin abunda kuke boye min ba, to kuwa zamu kwana anan ne.." yawu Anila ta hadiya tare da kallon benazir da hankalinta ya gama tashi, Cike da fargaba benazir tace"yaya shureim..dama ummm gidan su Azeezaty zamu je..." Dakyar ta are maganar ganin ya juyo dakai ya kalle ta tuni ya hade rai, annurin fuskarshi ya gushe rai a6ace yace"meyasa baki jin magana ta? Har nasiha nayi maki nace ki yi hakuri tun da yar nan ba taki bace ki hakura mana, ni dama tun da naga take takenku raina ya bani gidan su yarinyar nan zaku je, to wlh bada ni ba, da nasan gidan su azeezaty zamuje da ban biye maku ba." kallon juna sukayi hankalin su atashe damuwa ce arara akan fuskokin su. Juyawa yai tare da kallon Anila cikin sanyin murya yace"haba anila! Meyasa zaki biye mata? Ni nasan bada son ranki ba, itace ta matsa maki, Benazir bata da hakuri ta fiye kafiya da naci, ba irin lallashin da ban yi mata ba akan ta hakura da yarinyar nan amma ta i jin maganata" kifa kai Benazir tayi jikin seat din da take azaune ta fashe da kuka tana fadin"yaya shureim na hakura da ita, nasan ba yata bace na yarda da hakan, Anila tayi min bayanin komai dangane da ita kuma na fahimce ta...." ta are maganar tana shesshekar kuka, kafin yayi magana Aneelerh ta riga shi cewa"ka yi hakuri yaya shureim ban nemi shawararku ba nayi gamon kaina, saboda ina tausayin halin da Benazir take a ciki" ta fada tana kallon fuskar shi"shekaran jiya ta kirani awaya take fa a min ita fa tun a asibiti ta fahimci yarinyar nan ba yarta bace kun ce mata taj ya dauketa sunje mall shiru basu dawo ba kun hana tasan gaskiya kun boye mata saboda baku san 6acin ranta, ni kuma abunda nayi tunani duk daran dadewa dole Benazir tasan gaskiya tun da gashi harta kirani awaya ta fadamin tagane ba yarta bace shiyasa kawai na fa a mata gaskiyar zance,