Sashe 123
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya. Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta. "Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya aurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat aya ta nuna bata ganta ba. Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ru e ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta "Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan atuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nanna e cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta. "Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba. "Mami kinyi shiru..." murmushi ya e ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba. Ringing in wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun an kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta an firgita ka "Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta. "Babyna..." Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse. kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse. Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"? On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri" "Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani" Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan "Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..." "Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta" "Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun an jima suna waya kafin sukayi sallama. Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya bu e kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun Daya bayan aya ta fara karanta shi. _Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_ Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani aramin yarone ya auki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta... Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci aya taji gabanta ya an fa i ganin kamar nick name dinta wato Angel _My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_ Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi. "Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna "Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta wallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya" ta fa a tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba" Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu aya, sai yaji ta bashi tausayi. "Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"? "Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gya a kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin. ______________________________ Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta mi e kwata kwata babu kuzari kamar zata fa i kasa da sauri zahra ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta... Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah.... Bayan shigarsu dakin, Anila ta zame hannunta daga na zahra, ta zauna gefen gadon, wani iri gumi ne Ya wanke fuskarta, Numfashin ta da hucin zafi yake fita. tsananin tausayinta ne Ya kama zahra, cikin sanyin murya tace"Aunty Anila dan Allah ki daure ki tashi ki shiga toilet kiyi alwalar, idan muka kammala sallar sai muyi masu addu'a...." idanunta jawur ta kalli zahra, Cikin disasshiyar murya ta furta"Zahra ki barni kawai, Ni kadai nasan ra in da zuciya takeyi min! Zahra in har Ana bata dawomin da junaid ba, wallahi zaku iya rasa ni, saboda bazan iya rayuwa batare da yaron nan ba, zuciyata zata iya bugawa in mutu...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sar e makoshinta, fashewa da kuka zahra tayi"Aunty Anila ki daina wannan maganar! Bana jin dadi, Kina karya min zuciya ta! In sha Allah babu abunda zai faru dake, ba zaki mutu ba, kuma in sha Allah ba abunda zai faru da junaid, Zasu dawo cikin koshin lafiya..." lallashinta zahra ta ci gaba dayi dakyar ta samu ta shawo kan Anila, harta hakura ta mike ta shiga toilet yin alwala, bayan shigarta zahra ta nufi wardrobe din kayan Anila, don ta auko mata hijabi, bayan ta bude murfin ta zura hannu cikin jerin hijaban Aneelarh dake a jere ta ru aya tana kokarin janyota kwatsam! ba zato ba tsammani idanunta suka sauka akan an mutun dake kwance cikin shelve din wardrobe Ya kudundune kanshi atakure jikinshi duk ya sandare. Rass taji gaban ta ya fa i nan take ta saki hijabin dake ruke a hannunta ya fa asa ta runtse ido ta daddage ta fasa ara tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un jikinta ya fara kakarwa gaba daya tabi ta ru e takasa gane wanene ma ita dai kawai taga dan mutun kamar aljani, banko kofar toilet anila tayi da gudu ta fito jin sautin karar zahra, gabanta na faduwa ta furta"Zahra! Meye faru? Lafiya kike ihu? La66an zahra na kerma sam ta kasa magana sai nuna mata cikin wardrobe din takeyi da yatsan hannunta wanda ke ta kerma.. Adabarbarce ta furta"Aun...Aun... aunty Anila mutun! an mutun a ciki! ...." a matu ar ru e Anila ta nufi wardrobe din ta kai idonta inda zahra ke nuna mata lokaci aya ta waro idanunta waje da karfi ta furta"baby junaid..." sai lokaci zahra ta sake kallon shi dakyau taga fuskarshi sharkaf da gumi ya sandare kamar matacce duk ya takure kanshi a cikin shelve din da alama ya dade a ciki, wani abun daure kai towel ne aure a jikin shi daga gani har wanka anyi mashi. Allah kadai yasan meya faru da har ya 6oye kan shi cikin wardobe.. " A hanzarce Anila ta auko shi ta zauna kan floor tare da kwantar