Sashe 25
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
gaba aya ta kundumo saman tiles kanta ya daku, Harta zabura zata mike da niyar ta watsa a guje taji ya dam afarta aya, ta arfi ya janyota kamar iyar roba ya dawo da ita saman gadon, runtse idanunta tayi da sauri tana ambaton La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin. Dogayen yatsun hannayensa dake kerma ya aura saman wuyanta, ya sha eta sosai tamkar zai tsinka wuyan, radadin azabane ya ziyarce ta, ta kware baki ta fasa wata irin ara mai sautin gaske, sai faman kiciniyar kwace kanta take yi amma ta kasa saboda arfin dake gare shi tamkar zaki a haka ma don bai da koshin lafiya da tuni yajima da kashe ta cikin rashin sani. Radadin da tajine yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske Adai dai Lokacin Ummi ta fito daga room din ta, don taje ta fara shiryasu ganin lokacin dinner din Ya kusa Cika Har ta nufi stairs zata hau, kunnuwan ta suka soma jiyo mata Gunji gunjin kukan unaisah, Lokaci aya taji gabanta yai mugun fa uwa, tsabar rudanine akan fuskanta, fasa sauka tayi cikin takun sauri take bin hanyar da take jiyo sautin kukan cike da was wasin kodai kunnuwanta ne suke jiyo mata badai dai ba A hanzarce takarasa Bakin kofar, ta soma bubbugata tamkar zata 6alleta, muryarta da sauti mai karfi take ambaton sunanta"Unaisah!! Unaisa!! Unaisah" Kofar tamkar an datse ta da key taki bu ewa ta rufe gam, kware murya ummi tayi tana ambaton ba kowa ne akusa? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un unaisah idan kinaji na ki yi min magana! Meke faruwa dake ne'?_ Ta fa a jiki na tsuma ta zura hannu aya ta dauko wayarta daga cikin aljihun skirt dinta. Layin boss man ta danna ma kira bugu biyu yayi picking ko sallama babu tace"yalla6ai kazo gida an samu matsala, na fito daga daki na na ji yo sautin muryar unaisah a dakin danish tana kuka na tashin hankali, nayi kokarin bu e kofar ta datse..." Muryarshi a ru e Ya furta"Chief bai dawo ba"? Yarfa hannu ummi tayi "bansani ba, yanzu na fito daga daki.... bai bari ta are maganar Ba, Yayi rejecting kiran ranta ne ya 6ata cewar zai zo, tsayawa tayi abakin kofar Idanun ta sun ka a jawur ta tsorata dajin ihun unaisah, lokaci daya taji shuru babu ihun nata nan fa hankalinta ya kara tashi tadinga buga kofar da hannu da kafa Tana Ambaton"Unaisah dan Allah Kiyi min magana? Danish Ya farkane? Me yake yi maki? Meyasa kike kuka, Nashiga ukuna, Unaisah kada ki bari Ya cutar dake, Kiyi kokarin kare kanki! Unaisah kina jina? Naji kinyi shiru inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." hawaye har sun fara wanke fuskar ummi saboda ta gama gigita Zuciya da sake sake gani take kamar Danish Ya kashe ta ne shiyasa tajiyo shirunta. Kamar an jeho shi Ya fa o falon A fujajen, wuyan jallabiyar shi ma akarkace take sam baya a hayyacinsa, da gudu Ya falfala Ya haye up inda ummi take atsaye tana faman buge bugen ofa, yana karasawa Ya daddage da iya karfin shi na karshe Ya bangaje ta da kafadarsa nan take kofar Ta zuge kanta da gudun gaske, Tsabar saurin su shiga suga meke wakana har suna bangaje juna shi da ummin america, duk wannan budurin da ake sauran yan uwan su basu san meke faruwa ba. Shigar su keda wuya, suka taras da abun da ya daure musu kai, Yana azaune bakin gadon Ya du ar da kanshi kasa, Sumar kanshi Ta lullu6e fuskar Unaisah wadda kanta yake abisa cinyoyinsa' basa iya ganin fuskarta sai an kafafuwanta, cike da fargaba da karyewar zuciya boss Ya furta Sunan shi"Danish! Unaisa meya faru ne? Ka yi mata wani abu ne? Ha a sun yi mamakin farkawarsa babu wanda yayi tsammanin zai tashi a cikin an kwanakin nan. Adabarbarce ya kare maganar, tamkar yayi magana da bango babu alamun danish zai saurare su duk sun bi sun rude mutun kamar Ifritun aljani gashi ya damki yarinya a hannun shi Cikin shesshe ar kuka Ummi take rokonshi akan Ya saketa, kada ya kashe masu ita.....' Karfin Hali taj yayi da sauri Ya nufi gefen gadon inda su ke a zaune Ya mi a hannayenshi biyu da niyar ya kawar da ita, Dam ar hannunsa Danish yayi tare da dagowa yana faman lumshe idanun shi tamkar na wanda yasha giya, muryar shi da kasala Ya furta"ina bukatar ruwan da zan yayyafa mata" kusan atare ummi da Taj suka sauke ajiyar zuciya, saboda sunyi tsammanin baya ahayyacinsa ne. juyawa ummi tayi da sauri ta fita daga dakin sai gata ta dawo hannunta ru e da robar ruwan da ta auko a fridge ta mi a ma taj, shi kuma Ya kar6a ya Mi a ma danish, a hankali Ya sanya hannu ya kar6a bayan ya cire murfin ya tarfa hannunsa dake an kerma Ya ebi ruwan ya watsa mata akan fuskarta, lokaci aya ta zabura zata fara buge buge da sauri boss Ya dam i hannunta, tare da dago da ita ya zaunar. Wani jiri jiri take gani a idanunta, hannu tasa ta dafe makoshinta tana fadin ruwa ruwa zan sha. Kwafa mata ruwan yayi abaki ta rurruke robar duka ta shanye shi, ta dago da luhu luhu idanunta wadanda suka kada jawur da su Sam ta manta a ina take zaune, gani take kamar amafarki lamarin Ya afku, Kwata kwata bata lura da danish ba, wanda ke a gefenta kuma shi ya bata ruwan da ta sha. "Unaisah, are you okey? Ina fata bai ta6a lafiyar jikin ki ba"! Cikin kulawa ummi keyi mata magana Kallon ummi tayi murya na an rawa ta furta"nayi mafarki danish Ya farka, Har Ya sha e min wuyana" ta fa a tana shafa wuyanta "Ba mafarki ki ka yi ba, dagaske ne Ya faru, danish Ya farka sai dai baya a hayyacinsa ne lokacin daya sha e ki" boss ne ya bata amsa, da wani irin Hanzari ta dubi danish da ke gefen ta, idanunsa suna a lumshe numfashin sa na fita a hankali. Lokaci aya ta fashe da matsanancin kukan farin ciki, ta kamo yatsun hannayensa acikin nata, Muryarta cikin shesshe ar kuka take fadin"My man...kana lafiya? jinjina mata kai ya danyi alamar eh. "Alhamdulillah Ya Allah, Alhamdulillah..." sakin hannunsa tayi ta sauko daga kan gadon ta zube saman gwiwowinta tare dakai goshi kasa tayi sujjada tana mai nuna godiyarta ga Allah. Murmushi taj ya soma saki yana kallon danish, Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e shi mara misaltuwa Yaji dadin farfadowar nan tashi, Har ya fara tunanin haduwar shi da Prime minister. Har yanzu Danish babu fara'a akan fuskar shi, jefi jefi Ya ke kallon su da lumsassun idanunsa, ganin lokaci na shirin kure masu yasa ummi ruko hannun unaisah tace su tafi su fara shiryawa, kamar karta baro dakin tana tafiya tana waiwayon danish gani ta ke kamar in ta fita zai koma yar gidan jiya, har sai da boss yace mata zai kira chief yanzu awaya tare da sheikh imam tukunna ta an samu kwarin gwiwar barin dakin..... Batare da 6ata lokaci ba, Taj Ya kira chief awaya ya sanar da shi dangane da farfa owar danish, A lokacin chief Har Ya kira likitan da zai duba shi, yayi murnar jin zancen tashin danish, kafin ma karasowar su dakin sai da ya Kira Shiekh Imam suka jira Ya zo falon Kafin suka sauko shi da likitan dayazo duba dashi a tare suka nufi dakin shigar su keda wuya Chief owais ya nufi danish, tamkar dan uwansa na jini Ya mi a mashi hannu ya taimaka mashi ya sauko daga kan gadon gaba aya yayi hugging dinsa a jikin shi, ya aura hannayensa abayansa yana dan bubbuga shi, har rada yai mashi a kunna ya furta"nayi farin ciki da samun lafiyar ka, Ina fata babu abun da ke yi maka ciwo ayanzu..." ya fada tare da dafe kafadun danish ya dago da shi. Babu wanda baiyi farin ciki acikin su ba, Musamman sheikh imam Ya ambaci kalmar alhamdulillah tafi sau a kirga, ya aga hannayensa sama ya dinga zubawa Allah kirari Ha i da nuna godiyarsa ga nasarar da suka samu, Bayan ya gama ya janyo danish din duk da bai sakar masu fuska ba wannan bai shafe su ba, dama su burinsu ya farfado kuma Alhamdulillah kwalliya tabiya kudin sabulu, Rungume shi shiekh imam yayi tamkar zai mayar dashi cikin sa, ya dinga shafa sumar sa yana karanto addu'o'i yana shafe mashi ko'ina na jikinsa. Ko da likitan ya duba danish baiga komai ba sai ma wani abun ban mamaki daya gano wato Lafiyar dake gare shi, har ta wuce wadda hankali zai dauka, babu ko ciwon kai a tare da shi. Bayan tafiyar likitan shawarwari suka tsaya sunayi atsakanin su, kafin daga bisani chief ya raka shi bathroom don yayi wanka, Kafin ya fito aka shirya mashi lafiyayyan abinci a daki aka shigo mashi da shi, atare da chief suka ci abinci, gwanin ban sha'awa kamar wasu yan uwan juna sai daya tabbatar danish Ya cika cikinsa tukunna ya samu kwarin gwiwar sanar da shi dangane da uncle dinsa dake son ganinsa, ya nemi alfarmar yana so su tafi atare, shiru danish yayi mashi dama ya i furta masu magana tun da ya farka kamar wani kurma sai dai yabi su da ido. Tarairayarsa suka dinga yi suna lalla6a shi, duk don ya amince, amma an tahalikin nan yai shiru, dabara ce ta fadowa taj da sauri yace mashi a tare da su unaisah zamu tafi da sauran an uwan ka, kuma duk sun amince zasu je. Jin ya ambaci zasu tafi da su unaisah ne yasa shi saurin amince masu ta hanyar jinjina masu kai, domin kuwa bazai bari su tafin masa da yan uwansa ba, Murmushi sukayi gaba dayansu ganin sunyi nasara akanshi... Nan fa suka fara shirya shi, kamar wani yarima. Lokacin da su sajeed suka ji labarin Farkawar danish, Aguje suka watsa da gudu suka nufi bedroom dinshi, Tsabar farin ciki maimakon suyi dariya saima suka fashe da kuka suka dinga rungumar shi, Dadi kamar zai kashe su, Shi kanshi yayi farin ciki da ganin su duk da yaki tanka masu sunyi sunyi dashi akan ya bude