← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 186 OF 247

Sashe 186

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya bu e mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba. Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun aya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku.. "Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya. Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa. "Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi. dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince. boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun shirya"? "Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke. Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya... (Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya ana masa"?) Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a inta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta. Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata. Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden. Abakin kofar Room in suka dakata da yin tafiya, Gently ta aura Thumb inta akan Biometric scanner in dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking in kanta... Juyawa tayi tare da kallon P.a inta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am.. shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta.. akin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi. Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps inta. shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa? tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci aya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye. a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area. Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups in, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa. Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne. Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba.. fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata.. "Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban "Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.." Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta mi a mata. Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma akin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar. Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi.. Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka ka a jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru. "Owais," jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi.. "My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa. Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya arasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha! "Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"? ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba. Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..." fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"? A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined" gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ? girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..." an rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da an nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba. Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel. Gaba aya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matu ar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa. afafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su. har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa.. Kallo aya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ru ar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi. A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi. Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan. abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj. bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci. A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta aga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata anta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske. yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar" mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta. Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana.. Ko gama wayar basuyi ba
Chapter 186 · 0% Book details