Sashe 218
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
tsani yadda yake zafafawa akan addini kuma A ganinta kullan da ya ke yi ma Aisha takura ce. shi kuma yanayi ne saboda Farin jinin da Allah yayi mata, Babban abunda Ke ci mashi tuwo a warya yadda wasu mazan basa iya kau da maitarsu akan Aisha, saboda Dirin da Allah yayi mata, tun tana anuwarta wani irin dirin jiki ne da ita mai jan hankali, duk taku daya idan tayi sai jikin ya girgiza koda kuwa ta sanya dogon hijabi ajikinta ne sai shatun dirinta Ya bayyana wani irin farin jinin samari gare ta kuma mafi akasarinsu ba don Allah suke son ta ba sai don kwa ayin Surar ta. wannan dalilinne yasa shi tsananta mata tsaro ko fita za ta yi dole ta sanya dogon hijab da ni ab, daga makaranta sai gida makarantar ma shi ke kai su da kanshi In an tashi ya dauko su ita da Benazir, wani sa'in In aikin yayi mashi yawa ko zaiyi zaman shari'a Aunty Laura ce ke dawainiyar kaisu wani lokaci in ta samu damar dauko su daga school in an tashe su sai ta saci hanya takai su Shopping mall tayi masu siyayyar kayan amfanin su na mata. Awata rana ne Aisha tana a zaune kan darduma sai ga Benazir ta shigo gidan da rawar jiki ta shigo har dakinta ta ruko hannunta da farin ciki take fada mata tazo taga Uncle musa da Yaya shureim sun dawo Nigeria, kasantuwar su dukansu A lokaci ba mazauna Nigera bane, Shi Alhaji musa harkar kasuwancin shi yakeyi a kasashen ketare yayin da Shureim ke karatu a kasar egypt can gurin ammin su ya ke da zama. da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta. fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta ame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu.. ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda warjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe. Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth.. ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta. Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim.. Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo aya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya bu e al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria. Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke ya a videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba. sun an jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su. a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji. A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita. ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya. kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon bu e ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta auketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta. Tun bata sake ma Uncle musa in suka ha u harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta. Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa. A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata. Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi. shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah. A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam