← Book details Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete Local reading mode
READING PART 80 OF 247

Sashe 80

Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read

ganewa tun da wani bai ta6a rasa wani a cikin su ba, kuma bata fatan abun da zai raba ta da muradin ranta, her eternal lover "Haris Ina tayaka murna, Allah Ya nuna mana ranar auranku mu sha biki" da mamaki ya maimaita kalmar aure" yar dariya tay"cikar burin masoya kenan idan time yayi basai na maka bayani ba" murmushi kawai yayi duk da baisan me akeyi a auranba but maganarta tasa shi fara jin son ganin auran nasu. arfe tara daidai agogo ta buga, aya bayan aya suke fitowa daga dakunansu zuwa dining Room kowan nan su yayi wanka Ya shirya sunyi kyau daga ganin fuskokinsu zaka shaida Anyi kwanan farin ciki daren Jiya.... Da wani irin aukin junansu suka fara an rungume rungumen juna, gwanin ban sha'awa, aunar su a jini ta ke, harta chefs din dake a dakin cin abincin kallon su sukeyi saboda sun siye zuciyoyin su. Mutun ukune ke babu acikin su, ummi da batool sai Danish, su kadai ne ba su kaiga arasowa ba. Sun cika dining room din da surutu Ko zama sun kasa yai, Gyaran murya chef Yai masu Hankalinsu Ya dawo kan shi "Barkanku mu da safiya yan mata da samari, ina fata kun tashi Lafiya" a tare suka amsa mashi da lafiyalou "Yawwa, Yanzu ba lokacin surutu bane, lokacin bama ciki hakkinsa ne, nasan kunyi kewar Juna amma Ku anyi hakuri ku zauna mana" murmushi Kowan nan su Ya saki, ayan Chef din Yace"Amma in ba damuwa zamu iya sanin sunayenku? Don gaskiya bansan sunanku ba unaisah kadai nasani' Ya fa a Yana nuna ta da yatsa "Ba damuwa ni zan fa a maku sunayen su," unaisah ce tayi maganar, kafin ta fara fa a masu sunayen "wadannan biyun masu kama da twins sunayen su Jemimah sai Azeeza" ta fa a tana nuna su da yatsa sai faman sakin murmushi sukeyi. aga masu hannu chefs din sukai alamar suna miko gaisuwa "Sajeed Naufal and Javed" ta nuna kowannansu da yatsa "Wannan Kuma sunan sa Haris ga deejarsa a gefe, kamar anta da jini suke" "Kina nufin masoya ne"? aga masu kai tay alamar eh" "Wow masha Allah, shiyasa suke bala'en kama da junansu ashe soyayyace atsakani, Muna mi o maku gaisuwa" chefs din suka fada suna aga masu hannu, washe baki deeja tayi shima haris din murmushi ne kan fuskarsa "Ita kuma wannan sunanta Hannah" ta nuna hannah dake tsaye gefen parven, ga kuma Parveen acici" dariya sukai don sunsan Halinta na cin abinci" awa tayi kan su Rubina"rubina, eve and yasmin sai hibba" da sauri eve tace"kin manta jiya na fada maki yaya salsabeel Ya canza min suna hawwa" "Yeah Na tuna sunanta Hawwa, ga kuma sarah da mubeen" ta nuna su da hannu "thank You unaisah, kunga yanzu munsan sunan kowan nan ku saura mu saba da juna koba haka ba"? Atare suka hada baki wurin amsa masu da Yeah "Yanzu zamu fara shirya maku wurin zamanku tun da mun samu aruwa" Ba tare da 6ata lokaci ba, mutun sha Biyu daga cikinsu suka zauna akan 12-seater dining table din da suka saba cin abinci akan shi, sauran suka samu gurbin akan 6-sitter dama ukune a dakin cin abincin. Har sun fara cikin abincin, sautin cokulansu Ya cika dining room din kamar a restaurant yanayin yadda suka zauna, chefs din suna daga tsaye suna kallon. ewa unaisah tayi tare da kallon chefs din tace"zanje na kira aunty ummi da batool" bata jira amsar su ba tay saurin kama hanya don tasan zasu iya tsayar da ita.. Har takusa isa ga stairs, sai ga su sunfito daga daki, Hannunsu ruke cikin juna yadda kasan uwa da iyarta, ummi na asanye da abaya maroon tayi rolling, batool tun kayan jiyane a jikin ta riga da wando na bacci Suna ganinta a tare suka sakarwa juna murmushi da sauri batool ta saki hannun ummi ta nufi unaisah suka rungume juna kamar sun jima ba su a tare "Barka da safiya My own sis, jiya ko ki neme ni, aunty ummi ta wace min ke" ta fa a tare da raba jikin su daga na juna. "Ni da ke waye mai laifi? jiya kamar zanyi hauka wurin nemanki, ina kika je baki fada min ba"? rai a an 6ace tayi maganar suna kallon juna "I'm sorry, nima bada son raina na tafi nabarki ba, naga kuna firar yaushe rabo kuma bana son in katse ku shiyasa na tafi...." "Ina kike je ne"? Ummi ce ta jefa mata tambayar "Part din daddyna dake acikin gidan nan, " da mamaki ummi tace"oh dama anan yake zaune? Ko da yake naga gidan ba karamin girma ne da shi ba, ay ko zan ha u da shi maimakon ya gayyace mu muje baki aya shine ya ware ki ko"? Ta fada da zolaya yar dariya unaisah tayi"wlh ba haka bane, yace min next time kuma zai gayyace ku kuje part dinsa wurin auntyna danejo" Murmushi ummi tayi"ai ko bai gayyace ni ba zanje da kaina, ko dan ingano danejo, inyi mata godiya saboda taimakon da tayi mana wurin ceto rayuwarki" Fuskarta dauke da murmushi tace"naji dadin maganarki aunty ummi, Allah yabarmu atare" amsa mata sukai da ameen "angama shirya mana breakfast a dining, naga baku futo ba shi ne nazo don in kira ku" "Yanzu haka da kika ganmu yunwar ce ta koro mu nida baby girl dina" ta fa a tare da ruko hannun batool har zata ruko na unaisah donsu tafi a tare tayi saurin cewa" zanje na kira danish ne" amsa mata tai da okey, bayan sun tafi ta nufi bedroom dinsa tana gab da zata shiga taji motsin fitowarsa kusan atare idanunsu suka shiga cikin na juna kwata kwata fuskarsa babu annuri ganinta da yayi ne yasa shi an sakin fuskarsa tun daga kan yatsan kafarta ya fara kallonta ba karamin kyau tayi mashi ba, rigar ta ara fito mata shape dinta. "My man, ina fata ka tashi lafiya," lumshe mata ido yai alamar eh "Oh ba zaka min magana ba, kasan kuwa yadda na agu da inzo ganinka" ta fa a tana jifar shi da kallo mai kama da harara irin kallon da ke jan hankalin shi gareta "Saboda kaga na damu kai ko" ta fada tana ru e qugunta yar Ya iya ha iyar yawu Ya furta"kin tashi lafiya" aga mashi gira tayi"ina lafiya, pls ka shiga ka canza kayan baccin nan, sauran yan uwanmu suna jiranmu a dining muyi breakfast" "Mu shiga atare" ma e masa kafada tai"a'a zanjiraka anan, ka shiga ka fito" batai aune ba taji yaja hannunta cikin dakin, ba yadda ta iya dole tabi shi ciki. Juya mashi baya tayi bayan ta cire hannunta daga nashi tace pls ka sanya kayan suna jiran..." kafin ta are maganar ba zato ba tsammani taji Yai huggin din bayanta gaba daya ya kwanto da kanshi kan shoulder dinta tare da zagayo hannayensa kan waist dinta, a matu ar ru e ta furta"meye haka"? Ta fada tana kokarin raba jikinta daga nashi, kamar ya aureta da igiyoyi sam ta kasa watar kanta ara tighting nata yai tuni taji wani irin yanayi da bata ta6a fuskantar shi ba, rai a6ace ta fara zazzaga mashi masifa kamar baisan tanayi ba Muryarshi tamkar tame jin bacci Ya furta"ki taimaka min na sanya kayan" gaba aya nema yake ya burkita mata lissafin kwalwa, muryarta na rawa ta furta"wai meke damunka ne? akan wani dalili zan taimaka maka ka sanya kaya"? A hasale Ta fa a tare da kamo hannunsa dake akan cikinta tasoma kiciniyar banbare shi bakomai take jima fargaba ba face an mayafin data aure kirjinta da shi muddin ya warware danish zaiga abun da yajima yana jira kuma tasan sauran in har ya gani sai wani abu ya faru. Kamar zata fashe da kuka tace"danish ka sakeni banaso, Babu kyau! Ka matse min cikina! tsabar masifa idanunta arufe ta furta maganar Babu akamun zai saketa sai faman goga tsinin hancinsa Yakeyi akan fatar wuyanta wani irin Yanayi da bai ta6a jin makamancinsa ba. A lokacin da baiyi tsammani ba, Yaji ta gartsa masa cizo A hannunsa, ba don Yaji zafi ba Ya saketa, da wani irin kallo Yabita har ta fuce daga dakin da gudu..... Fitarta keda wuya Yaji kamar ancanza mashi tunaninshi, lokacin aya yafara tunanin me yasa yayi mata hakan Tun akan stairs jikinta ke kakarwa kamar wadda sanyi ya kama, Gaba aya Ya jefata cikin Yanayi kamar bata a hayyacin ta Sam bataji takun tafiyar sa ba, har sai da muryarsa ta katse mata zancen zucin ta"Good morning daugher"! Wani irin firgita tayi don sai taji kamar muryar danish ne ganin daddyntane Yasa tayi saurin daidaita nutsuwarta gudun kada Ya fahimci wani abu Ya faru. Jiki asanyaye ta nufe shi ta fada kan kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya ta furta"daddy Ina kwana, Ina auntyna danejo, Ina fata kun tashi lafiya" Dago da fuskarta yai suka hada ido cikin na juna, farat aya ya an fahimci wani abu na damunta "Kamar wani abu na damunki? Ko baki da lafiyane" adan rude ta girgiza masa kai"bakomai daddy lafiyana lau" Ajiyar zuciya ya sauke "Auntynki tana gaisheki, Kamar zata sanyamin kuka tun jiya bayan mun yi maku rakiya mun koma gida ta dinga yi min surutu akanki, yau da safe har ce min tai zakizo nace mata aa sai tace min tana son tazo taganki dakyar fa na lallasheta ta hakura' Murmushi unaisah tayi"Allah sarki auntyna. Kada ta damu har sai ta gaji da ganina' o hannunsa tai acikin nata"daddy muje muyi breakfast" "Am sorry daughter bana Jin yunwa, aunynki ta cika min cikina, but da anjima idan na shigo zamu ci dinner a tare yanzu zan tafi dama na shigo ne don inga sanyin idaniyata" farfari tayi masa da ido yakai hannu ya an ja kumatunta huggin dinta Ya sake yi kamar karsu rabu "Ki kula min da kanki, Allah Yayi maki albarka," amsa mashi tayi da ameen daddyna kaima ka kula min da kanka Bayan sun raba jikinsu daga na juna. har ya juya zai fita sai kuma Ya an dakata tare da waigowa Ya kalleta tana atsaye bata motsa ba itama shi din take kallo "Kin shiga wurin chief "? Girgiza masa kai tay alamar a'a,"pls ki
Chapter 80 · 0% Book details