Sashe 7
Cigaban Kurkukun Kaddara Takun Karshe Complete · about 8 min read
aga Murya ta yi Wanene"? Daga waje tajiyo Muryar Batool Tana fadin"aunty Ummi ni ce" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta jin muryar Batool. "Ki shigo daga ciki," turo ofar batool tayi tare da shigowa ciki, tana bin dakin da kallo kafin ta aura idanunta akan fuskar Ummi, Murmushi suka sakarma juna "Nayi fushi Batool, sai yanzu zaki tuna dani? Nayi tsammanin kece mutun na farko da zaki zo gare ni idan kika ji shiru ban fito ba, amma sai naji shiru babu ke babu unaisah" tafa a tana ha e mata fuska alamar ranta Ya 6aci. "Aunty ummi am sorry, Kina araina, tun azu nake taso in shigo wurin ki' a mata hannu Ummi tayi da sauri Batool ta arasa gabanta tare da fa awa kan chest dinta, sosai Ummi tai hugging dinta. "Nayi missing dinki My babe, kun barni a daki ni ka ai inata kewarku, Ina unaisah ne"! Ta fa a batare data raba jikinta daga na batool ba. "Nima bansan inda take ba, azu muka rabu" "Okey,ina fata kina lafiya, " ago dakai Batool tayi"Lafiyata lou, amma ke kamar baki da lafiya" Shafa gefen fuskarta ummi tayi"bana jin dadi, amma kada hakan Ya dame ki, ganinki da nayi ya faranta raina" ta are maganar tare da ru o mayafin Pakistan din batool"kayan sunyi maki kyau sai naga kinyi min kama da wata Old friend ina da muka rabu da dada ewa, kamar ita ta haifeki, Itama doguwace fara, Mom dinta balarabiya ce" Murmushi batool tayi"amma ni da Unaisah nake kama" Girgiza kai Ummi tayi"No, baki kama da Unaisah kun dai yi yanayi da ita" Kwa6e fuska Batool tayi saboda ita tafison ace tana kama da Unaisah, ummi ta fahimci hakan sai tayi saurin cewa"wasa nake maki, dama don in ga reaction dinki ne, gaskiya kuna kama da ita sosaima kamar twins" jin hakan yasa batool sakin dariyar farin ciki, ummi dake kallonta batayi mamakin hakan ba ta riga data fahimci tsantsar aunar da suke ma junansu. "Mu zauna ki tayani fira, Ko baki gaji da tsayuwa bane" "Aunty ummi, nasan kina jin yunwa, ki tafo muje falo zan sama maki abunda zaki ci" wani irin kallon auna ummi keyi mata ba aramin dadi take ji ba idan Batool ta nuna damuwa akanta. Ru o hannunta ummi tayi acikin nata atare suka fito daga dakin. Sautin Muryoyinsu Naufal ne Yajawo Hankalin Ummi Ga kallon su, tun Dazu suna a falo, Tare da Boss Man, Sun tasa shi gaba sai surutu suke zuba mashi. Jin takun Takalmansu Yasa su dagowa suka kalli su Ummi dake saukowa down stairs, Har suna ha a baki wurin ambaton sunanta Aunty Ummi. Saukowa Jamimah da azeeza su ka yi daga kan sofan da suke zaune, da gudu suka nufe ta, Hannah da Parveen ma suke mi e suka nufe, wani irin da i taji aranta, aya bayan aya ta soma rungumarsu a jikinta, "Aunty Ummi, Yanzu kika tashi daga bacci"? Azeeza ce tayi mata tambayar Girgiza mata kai tayi alamar a'a Parveen tace"Ko dai baki lafiya" Harara Ummi ta jefa ma Parveen tare da cewa"kun damu dani ne? Meyasa ba ku zo bedroom ina kun duba ni ba? Shiru sukayi sai jamimah ce tai kokarin cewa"mantawa mu ka yi" Jan kumatunta Ummi tayi da hannu"Aku sarkin umi, Na riga da nage baku kaunata, Shiyasa baku damu dani ba" ta fa a ha i da marairaice masu fuska, "Wallahi aunty Ummi Muna aunarki, kuma mun damu dake" Hannah ce tayi maganar "Ni dai Inasonki aunty Ummi, kiyi hakuri idan mun 6ata maki rai," murmushi ummi tasakar ma Azeeza da tayi maganar. o hannunta Jemimah Tayi"Aunty ummi nima ina sonki" "Naji na Yarda kuna sona, Yanzu mu shiga ciki," ta fada tare da Jan hannun Batool suka nufi ciki tare da su Hannah Tunkafin Su araso, Boss man Yake Kallon Ummi, sam ya manta da ita. "Barka da hutawa Yalla6ai, Fatan ka wuni Lafiya, Ya iyali" A hankali Ya furta"Lafiyalou Ummi, Ina fata kema haka"? aga mashi gira tai alamar eh, ta fa a tare da samun wuri saman Sofa ta zauna, suma sauran duk suka zauna. hankalin Sajeed na akan screen din wayar Unaisah, Haris da javed suna zaune gefe da gefen shi tare da naufal sai kallon Game din da Yake bugawa suke yi, baijima da sauke shi akan wayar ba. Gyaran Murya Ummi tayi masu atare suka dago suna kallon ta. "Sannunku, ba hello ba Hi kun samu Waya kunata danna waya baku ita ne" "Ta Unaisah ce," Acewar Sajeed Da mamaki Ummi tace"Unaisah ke da waya iphone15pro? Amma ban ta6a ganinta ba" "Dr Laurace ta bata Kyautarta, aya daga cikin Likitocin da suka yi jinyarsu a america" Boss man ne Ya bata amsa, Jinjina kai tayi. "Ina ita Unaisah dinne"? Tayi tambayar tana kallon su Boss Yace"Bansan meya tsayar da ita ba, tun azu da muka shigo tare da big guy Ya tafi da ita zai nuna mata kitchen din gidan nan ban ara ganin ta ba, ba mamaki ta tsaya taya masu aiki girkin dinner" "Dan Allah ka nuna min kitchen din, Inaso In kar6o ma aunty Ummi abinci, Yunwa take ji" acewar Batool. Murmushi boss man Yayi yana dubanta yace"kin damun da auntyn nan naki da alama, kada ki damu, bari na kira big guy awaya, idan suna a kitchen din zansa akawo mata abincin.... " kafin Ya are maganar, Parveen tayi saurin cewa"Dan Allah Nima zanci" dariya sukayi gaba dayansu. Ummi tace"foodie, Baki Gajiya da cin abinci, shiyasa kika fi sauran an uwanki jiki" Kwa6e fuska tai"ay bani kadai bace me cin abincin ba, Ki kalli kumatun jamimah sunyi manya manya da su" maganarta ta basu dariya. Harara jemimah ta watsa mata"ay dai ban kaiki Cin abinci dayawa ba, Ni madara da bonbita nake sha, Sai dafaffan kwai da Fika fikin Kaza," boss dake kallonsu murmushine dauke akan fuskarshi, Firarsu ba karamin nishadi take sanya shi ba Wayarshi Ya zaro daga aljihu Ya danna ma Big guy kira, Bugu uku Yayi Picking Mi ewa yai da sauri Ya nufi cikin falon nesa da su ya tsaya saboda hayaniyarsu. "Malam Ina ka shiga ne? Ka tafin mun da rabin raina" On the other hand sautin dariyar Big guy ta kara e Kunnuwansa, "Nifa Yanzu Haka Ina daki kwance saman gadona" "Bana son Iya shege, To ita ina kabarta? "Ka riga da kasan Halin Jarin naka, yarinyarce da kiriniya, Tunfa dazu dana nuna mata kitchen din nace mata ta dawo cikin yan uwanta, bayan na fada mata hakan na wuce room dina, yanzu haka bata wuce kitchen din, Cikin kattai" ya karasa maganar Yana dariya. Daure fuska boss yayi tamkar Yana agabanshi, "Zamu hadu dakai ne, Allah idan wani abu Yasamu Yarinyar nan jikinka ne zai gaya maka dan rainin wayau" ya fada tare da yin rejecting kiran, Cikin takun sauri Ya nufi hanyar zuwa kitchen din, ba laifi akwai tazara tsakanin kitchen din da main falo, Lokacin da Ya Isa katafaren kitchen din gidan tamkar a restaurant tsabar ha uwarshi, kai kace ba wurin Girka abinci bane saboda girman shi da awatuwarshi, An zuba kayan aiki masu tsada da inganci, gaba aya masu girka abincin Gidan Jami'an Isod ne cikin chef'uniform, matasan samari masu jini a jika, daga ganin Yadda suke aiki zaka shaida kwarewarsu a 6angaren catering, ko mace bazata nuna masu Iya sarrafa abinci ba, A alla sunkai su Bakwai, Babu wanda Ya lura da shigowar Taj acikinsu, Gaba aya Hankalinsu na akan Unaisah, dake agaban kitchen island tana Yanka masu kayan Lambu, abun da ya aure ma taj kai, ganin Yadda sukayi mata rumfa kamar zasu ha iyeta tsabar yadda suke binta da mayataccen Kallo, Ta saki baki sai Labari take basu su kuwa sun Kasa kunne suna sauraron dadda ar muryarta, Tunda suka kafe ta da idanunsu ko kyaftawa basa yi kamar zasu ha iyeta. Gyaran Muryar da Taj yayi masu ne Yaja Hankulansu ga dubanshi, kamar sunga wani mugun abu, A gaggauce su kayi saurin barin Inda Take, kusan atare suka buga afa Ha i da sara mashi. Kallon Harara Ya watsa masu, Cikin harshen turanci Ya furta"wannan wani irin gangancine zaku bar Yarinya tana amfani da wu a? Kun wani tsareta da idanunku kamar zaku lashe ta" Sunnar dakai su kayi Suna faman sosa keya suka hada baki wurin furta"sorry Sir, ba laifin mu bane, Itace ta bu aci damu koya mata girki, munyi kokarin Hanata amma saita sanya mana rigima" Wurga eye balls dinsa Yayi akan Unaisah dake Kallon shi, Har ta ajiye wu ar hannunta, nufo shi tayi fuskarta da murmushin Ya e tace"ay ni nace su bani In tayasu aiki, Kuma dama Na iya ba yar koya bace" ta fada tana ru e qugunta da hannu. Wani kallo Ya jefa mata me kama da harara, bakomai Yake tunawa ba face lokacin da tana yar aramarta, ranar daya tafi aiki yabarta a gida tana jin yunwa taje ta kunna cooker gass da sunan zata yi girki, wuta ta kama a gidan, wai yau itace take mashi kurin ta Iya girki ba yar koyo bace? Girgiza kai Yayi ha i da yin murmushi tacikin face mask dinshi "Daughter, an uwanki sunata nemanki, Yakamata Kizo Mu koma falo" ma e mashi kafa a tayi"ay bamu gama girkin ba" "Bana son gaddama, zo ki wuce mu tafi" Marairaice mashi fuska tai"dan Allah kabarni wallahi inason In Iya girki kala kala," "Kada Ki damu, zansa a koya maki amma ba yanzu ba, dokar Aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, baki ga maza bane a kitchen din"? Cikin lallashi yayi mata maganar Yana nuna mata chefs din dake tsaitsaye cirko cirko suna kallon su "Yalla6ai, da dai anbarta ta koya tun da ta nuna tana so, kuma ni aganina maca ce ita, wata rana zataso tayi ma mijinta.... "Tunkafin chef din daya dauko Maganar Ya karasa boss Yayi mashi wani kallo mai nuni da kashedi, Hakan yasa shi yin saurin Katse maganar, Janyo hannun Unaisah Yayi dakarfi Ya fito da ita daga kitchen din, Chefs din basu ji dadin zuwan Shi ba, Ya raba su da Yarinyar data e6e masu kewa yau, zuwanta Ya faranta masu rai, sunji dadin surutun da tadinga yi masu, komai nata burgesu Yake yi. Ranta Ya 6aci,