← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 184

Sashe 88

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can sasan Iyah kuwa TAIMIYYAH ce kewa Iyah
orafi tana cewa, "Iyah yanzu daga cewa ga ba
o sai ki ce a kaisa falon Abie,meyasa ba za a ce ya zauna a waje kamar ko yaushe ba?"
Iyah ta fige kanta daga kitsa goran
arshe da TAIMIYYAH ke yi,ta aika mata wani kallo tana cewa, "Haka na ga ya dace kuma ina da dalilina na cewa ya je can,kiyi maza ki tashi ki fita bana son wani zancen banza."
TAIMIYYAH ta shagwa
e fuska tare da narke murya tana cewa Iyah, "Gaskiya Iyah ni dai da kin bar sa a waje,miye na wani cewa a kaisa can sasan kamar wanda ki ka sani,ko ki ka san da zuwansa, ni waima waye zai zo da yamman nan yace wani ana sallama da ni?"
Iyah ta zabga mata harara tana cewa, "Zainabu ki fita ido na,zaki tashi ki wuce ki kintsa kanki ki fita, ko sai anji kan mu ni da ke?"
TAIMIYYAH sai ta tashi tana dafa
afarta ta nufi hanyar
akinta,sai faman mita take yi a zuciyarta ,ga wani fa
uwar gaba da take ji tunda Tukur ya zo ya sanar cewa wani na sallama da ita a waje.

Wajen kayanta ta nufa ta ciro dogon Hijab red ta sanya,tsayinsa ya sauka mata har
asa dai dai
waurinta.Ta
arisa gaban madubi bayan ta sanya takalmi tana gyara wuyan hijab
in ya zauna dai dai,ta kalli face
inta da babu komi a kai sai kwalli da ta sanya tun wankan safe,sai ta
an goga man le
e me taushi, ta juya ta dafe guiwarta ta fara takawa don barin
akin.

Tana ratsowa cikin falon Iyah ta tsareta da idanu,tana kallon yadda jan Hijabin ya haske farar face
in TAIMIYYAN ya yi mata mugun kyau.

Manyan fararen idanunta na haskawa, da
yallin ba
in kwalliin da ta sanya a idanun, yana
ara
awata kyawun fuskarta.

"Masha Allah!

Zainabu kin yi kyau matu
a, sai dai ki saki fuskar mana TAIMIYYAH,wannan irin
aure fuska kamar wacce aka ce ga ma
iyinki na jiran ki,ki sawa zuciyarki salama duk wanda ki ka ga yazo gare, ki yi fata cewa Allah sa alkhairy ne ya kawo sa,amma ba ki dinga
ata rai kina cuskune fuska ba,kin kai munzalin aure Zainab, kuma duk masoyinki zai miki fatan kiyi auren, don shine cikar mutuncin
a mace, don haka ki saki ranki don Allah,ki je an bar shi yana jira tun
azu,zan bai wa Ladi
an lemu da ruwa ta kawo masa."
Iyah tayi maganar idanunta akan TAIMIYYAH da ke ta faman zumbure baki,ta dubi Iyah da muryar shagwa
a tana cewa, "Ni Iyah wallahi tsoran fita nake yi,bana son abinda ya faru ya sake faruwa,shiyasa bani sha'awan sake kula kowa a yanzu."
TAIMIYYAH tayi maganar cikin sanyin murya sosai,wani abu na ta
a zuciyarta sosai.Iyah ta dubeta da fuskar tausayi tana cewa, "A'a Zainabu kada ki karaya komi da ki kaga ya faru da bawa mu
addari ne,don uwar Nass ta gujeki don kina gurguwa,hakan ba shi ke nufin ba za ki samu wanda za su amsheki a yadda Ubangiji ya so ganinki ba.Ki je babu abinda zai biyo baya sai alkhairy Insha Allah."
Da wannan
warin guiwar na kalaman Iyah,TAIMIYYAH ta fito daga sasan ta nufi na Ummie.Cikin tafiyarta me cike da nutsuwa dafe da guiwar
afarta take takawa,har ta isa cikin sasan Ummien,tana karya kwana zuwa hanyar da zai sada ta da
ofar falon Abie ta waje.

Ta tsaya daga bakin
ofar shiga falon, tana kallon takalmar da ke zube daga bakin
ofar,wani irin fa
uwar gaba ke cigaba da riskar zuciyarta.

Ta yi
arfin halin yin sallama cikin siririyar muryarta,kafin tayi jim!

Don jiran ya bata izinin shiga amma sai taji tsit!

Da alamun ko sallamar nata ma da wuya idan an amsa,don bata ji alamun hakan ba ko ka
Ta sake doka wata sallamar nan ma shiru babu amsa,hakan yasa ta yin
undubala ta
aga labulen
ofar ta sanya kanta ciki.

A.Maleek Ado dake zaune yana facing
ofar shigowa falon,tun sallamar farko ya ji ta, ya kuma amsa a ta
aice ta yadda ba za ta iya jiyo sa ba.

Ya zubawa
ofar shigowan idanu yana son ganin halittar da za ta kutso kanta cikin falon,don haka akan idanunsa TAIMIYYAH da ke dafe da guiwar
afarta tana takowa zuwa cikin falon suke.

Wani irin dokawa
irjinsa ke yi lokacin da take sake kusantowa cikin falon.

Maleek sai ya samu kansa da kasa
auke ido daga gareta, har ta samu waje ta zauna cikin kujeran da ke daura da inda yake zaune.

Amma ita TAIMIYYAH har lokacin ta
i kallon inda Maleek
in yake zaune, sai qamshinsa da hancinta ke shaqo mata,wanda bata ta
a jin wani mahaluki da irin qamshin ba sai yau.

Sai da ta nutsu cikin kujeran sannan ta
ago manyan idanunta ta saci dubansa,cikin sa a shi ma na shi idanun na kanta, ba tare da ita ta san cewa yana kallonta ba.Wani irin abu ya doka a zuciyar duka su biyun, TAIMIYYAH tayi saurin janye nata idanun daga kansa,bugun
irjinta na
aruwa da sauri-sauri.

Shi ko Maleek Ado wani irin abu ne kaman tsawa,ya ji ya doka a tsakar kansa,lokacin da idanunsa su kai tozali da manyan idanun da yake cin karo dasu cikin barcinsa.Idanun da ke jefashi cikin ru
u da tunani me tarin yawa duk lokacin da zai yi mafarki ya gansu a cikin baccinsa,bai san lokacin da ya mi
e tsaye yana sake tsareta da manyan idanunsa ba.

Jikinsa har wani irin shaking yake, na tsananin shiga ru
u da ki
ima,ya shiga takawa a hankali don isa gaban TAIMIYYAH, wacce ta sunkuyar da kanta
asa,tana ji kaman ana sanya igiya ana
aure dukkanin jijiyoyin jikinta ne.

Har Maleek ya iso gare ta, bata sani ba sabida kanta na du
e a
asa ne,sai da ta ji
amshin turarensa yayi yawa a hancinta,sannan ne ta
ago manyan idanunta ,don tabbatar da ko shi
in ne ya taho kusa da ita,aiko sai karaf idanunsu suka sake har
ewa da juna.

Wani irin fa
uwar gaba ya sake ziyartan zuciyar Maleek Ado,wanda ke tsaye kyam a gabanta,ganin zata sake maida kanta
asa ,yasa yayi gaggawar kai hannu ya ri
o fuskarta baki
aya a tafukan lallausar fatar hannunsa.

Lamarin da ya girgiza zuciyar TAIMIYYAH,tare da haifar da matsanancin fa
uwar gaba daga
irjinta,tayi gaggawar lumshe idanunta jikinta da zuciyarta na wani irin rawa.

Maleek Ado da yake jin tamkar an tsaida gudun jini daga jiyoyin jikinsa,sai yayi azamar sakin face
in nata yana
arin ri
e kansa.Gaba ki
aya kansa yayi wani irin kullewa na ban mamaki,babu tamtama ko kokonto wannan gurguwar da ke gabansa, irin idanunta yake gani kullum cikin mafarkinsa,wanda ba a ta
a nuna masa zahirin face
in ba illah wa
annan manyan fararen idanun kawai.

Jikinsa ya yi wani irin sanyi
alau, har kuma lokacin yana tsaye a gaban TAIMIYYAH ya kasa motsawa,sai da yaji
afafunsa na neman kasa
aukar gangar jikinsa, sannan ya lalubi kujeran da ke kusa da ita ya zauna, yana me kai hannu ya dafe goshinsa da hannuwa bibbiyu.

Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na cigaba da tariyo masa, yawan mafarkan da ya dinga yi da idanun Yarinyar da ya kasa tantance wacece ita?

Sai gashi yau ya ga irin idanun sak akan fuskar wannan gurguwar da Hajjah ta turo sa zuwa wajenta.

Yayi saurin bu
e idanunsa ya sake zubawa TAIMIYYAH,wacce ta kasa
agowa bare ta sake dubansa,gaba
aya itama zuciyarta ta shiga mummunan yanayin da ba za ta iya fassarawa ba.
amshinsa da laushin tafukan hannayensa da suka sauka akan face
inta,ke sake jefa zuciyarta cikin wani yanayi,jin shiru bai sake wani motsi ba yasa ta
ago kanta ta saci dubansa
asa-
asa.

Idanunta su kai masa kallon sakanni kwanyarta na yaba ha
uwarsa.Tayi gaggawar
auke ganinta daga garesa, lokacin da idanunsu ke son sake shiga cikin na juna,sai ta bu
e baki cike da
arfin hali ta gaida shi.

Memakon ya amsa sai ya cigaba da zuba mata idanu,tasirin abinda yake ji a zuciyarsa na sake hauhawa kamar farashi.Zuwa wani lokaci can ya sauke wata zazzafar numfashi ,yana cigaba da kallon yadda TAIMIYYAH tayi
asa da kanta sosai,kamar wacce take jira yace ket...!

Ta arce da gudu,sai ya bu
e baki cikin
asaitacciyar muryarsa yace, "Zaynabb!
ago idanunki ki kalleni please..!"
Yadda ya fa
i sunanta, da yadda muryansa ke fita cike da aji da
asaita,yasa TAIMIYYAH ta
ago kanta,tare da sanya idanunta cikin nasa.Maleek ya yi saurin sake xubawa kwayar idanun TAIMIYYAH ido, zuciyarsa na cigaba da girigiza da tarin al'ajabi da shiga ru
u,ya janye nasa idanun tare da lumshesu yana kiran sunan Allah a hankali.

Abinda ya yi matu
ar baiwa TAIMIYYAH mamaki da shiga ru
u kenan,ta dinga mamakin yadda du
k ya wani birkice,tun daga shigowarta cikin falon.Sai ta tashi tsaye tana dafe guiwar
afarta don ficewa daga
akin ta bashi waje, ko ita ma zata daina jin abinda take ji daga cikin zuciyarta,amma sai amon muryarsa a dake ya tsaida ita, inda yake fa
"Koma ki zauna."
Babu musu ta koma ta zauna, tana jin tamkar ta
aga waya ta kira wani ya zo,don ya zauna a tsakaninsu,sabida ta fara tsorata da lamarin wannan mutumin,wanda kallo tayi masa ta ji kwarjininsa ya cika
akin baki
aya.

Maleek Ado ya fara da cewa, "Zaynabb sunana Abdulmaleek Ibrahim Ado,na kawo kaina gareki ne don mu ga juna,kuma ina fata zaki bani dama don sanin cikakken asalinki, koda a ta
aice ne."
Yadda ya yi maganar yana tsareta da manyan idanunsa,ya hana TAIMIYYAH dubansa cikin ido,amma gaba
aya sai ta ji duk wani musu da take son yi masa ta kasa.
Chapter 88 · 0% Book details