← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 184

Sashe 15

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bari mu ji miye asalin wa annan bayin Allan. _______ Alhaji Amadu haifaffen garin Zaria ne,a wata anguwa da ake kira da Rimin tsiwa,tun asali ya taso da son karatun zamani dana addini,hakan yasa ya kasance me tsananin wazo da maida hankali,har yakai matakin shiga jami'a inda ya karanci MASS COMMUNICATION,lokacin da ya kammala karatun bai wani jima ba ya fara aiki da gidan Radion tarayya da ke Kaduna,a lokacin ne kuma Allah ya ha a shi da Fatima wato Iya kenan,ba'a auki lokaci ba suka fahimci juna Iyaye suka shiga cikin maganan akai aure,Iya itama Iyayenta duk haifaffun Zarian ne suna zaune a anguwan Juma,lokacin da biki yazo sai ya kama mata haya a wani anguwa da ake jira Tudun Jukun a cikin birnin Zazzau in,yana tafiya aiki Kaduna ya dawo duk arshen mako ko kwanaki uku,Fatima wayayyace itama ar boko wacce ta kai matakin kammala Sakandiri Skull,sai dai daga matakin Sakandiri sam bata cigaba da karatun boko ba,sai ta dagewa zuwa islamiya na matam aure tana kwasan tarin ilimin addini,cikin shekaru biyar da auren su Allah ya azurta su da samun a uku,na farko me suna Sameer sai Sani sai mace me suna Bilkeesu,daga nan Iya bata sake samun haihuwa ba,shi kuma Alhaji Ahmad bai kuma wani auren ba,duk da a lokacin an uwa sun sha zuga shi akan hakan,musamman lokacin da aka ga bu i ya same shi yayi ku i har ga gina aton gidansa a Gyallesu sun tare,amma yai biris ya maida hankalinsa akan gina rayuwan ansa,da basu nagartaccen ilimin zamani dana addini,hakan yasa yaran suka taso da wani irin nagarta da tarbiyya me kyau,don Iya ta kasance jajirtacciyar uwa,mara wasa da aukan wargi, ta tsayu matu a akansu har suka kawo lokacin girma,manyan mazan suka shiga jami'a ita kuma Bilkisu na matakin gama Sakandiri a lokacin,da yake ta taso da jikin girma da kyawun halitta wanda ta gado a wajen Iya ,sai manema suka fara mata sallama,ganin hakan yasa Alhaji Amadu cewa da zaran ta kammala Jarabawan kammala Sakandiri aure zai mata,ta cigaba da karatun a akin mijinta,hakan ko ya kasance bata auki dogon lokaci ba wani ya fito da aka aminta da shi me suna Ameenu, an Zaria ne amma yana aiki a Kano,aka sanya lokaci ka an akai bikinsu tare da kai Amarya Kano,su kuma su Baba Sani aka cigaba da karatu,lokacin da suka kammala karatu kowa ya fara kawo arfi don suna sana'a bawai bokon suka tasa agaba ba,musamman Sameer yafi an uwansa son nema da dogaro da kai,kuma cikin sa'a duk abinda yasa agaba sai ya samu bu i,bayan sun kammala bautan asa ne Allah ya ha a shi da Zainab,wata irin kyakykyawan budurwa me tarin hankali da nutsuwa,anan asan layinsu take gidan da ake ri onta,don asalinsu an Daura ne katsinawa,aure ya kawo Yayarta Zaria da take kira da Anty Mardiyyah shine take ri onta,tunda Sameer ya yalla ido akanta su Iya basu sake ganin nutsuwansa ba,har sai da Allah ya nufi aurensu da ita,wani irin soyayya suke gwadawa juna na ban mamaki,lokacin da akai musu aure Zainab da ake kiranta da TAIMIYYAH a gidansu tana matakin Degree ne a ABU da ke congo tana karantar Law,Sameer mahaifinsu Alhaji Amadu ne ya gina masa babban flat a filin da ke cikin gidan wanda ya siya ne dama sabida su biyun shi da qaninsa Sani,da aka tashi fara ginin sai aka gina duk biyun a lokaci guda kuma ginin iri aya komi da komi,daga Iya har Baba Amadu kaman yadda ake kiran mahaifinsu Sameer in,hankalinsu ya kwanta da auren Sameer tun abinciken farko da sukai game da nagartan Iyayen TAIMIYYAH,sai dai basu sake gasgata hakan ba sai da TAIMIYYAH ta shigo cikin gidan,sannan Iya ta sake sanin anta yayi dace da mace ta gari,sam bata da hayaniya ga tsananin kunya kaman ba ar boko ba,tana da biyayya matu a agun mijinta da su Iya,hakan yasa cikin anin lokaci ta siye zuciyan Iya,wacce Allah ya aura mata son matan an nata,har yakai ta daina mata kallon suruka ta koma yi mata kallon ar da ta haifa,kasancewan mace aya ta haifa kuma tayi nesa da ita,don Anty Bilki kaman yadda ake kiran Bilkisun sam bata cika zuwa gari ba inba da wani abu ba,mijinta me kulle ne sosan gaske shiyasa Iya da ta samu TAIMIYYAH a matsayin suruka ta gari sai ta maida ta tamkar a,sam bata ta a ganin aibun yarinyar ba sabida biyayyan da take mata da yadda ta iya kula da anta,domin cikin shekaru biyu da aurensu da Sameer in kowa sai tanka irin kyawun da yayi wanda ke alamta yana samun nutsuwa da kwanciyan hankali,itama TAIMIYYAH tayi wani girma da cika duk da cewa bawai jikin iba can gareta ba,cikin kwanciyan hankali take cigaba da karatunta,sam Iya bata sanya musu idanu a lamuran su irin yadda wasu surukan keyi,ba ruwanta da shiga Sasan su sam sai in wani ba lafiya a cikinsu ta le a tace sannu,TAIMIYYAH itace me tarewa a Sashin Iyan da zaran ta dawo Skull,cikin haka Sameer ya samu aiki a Kaduna a wani ma'aikata me suna NNDC,don haka sai ya koma zuwa duk Weekend,haihuwa shiru-shiru har sun shiga shekaru uku da aure,Iya bata ta a nuna damuwa ba sai binsu da addu'a da take yi,a cikin haka shima Baba Sani ya gabatar da Zuwaira a matsayin wacce zai aura,sun ha u da ita tun wajen bautan asa wanda shi aka tura shi Yobe,a can suka ha u suka kamu da son juna wanda arfin soyayyan duk ta wayane,don Yobe ba kusa bane baya samun zuwa,sai da Iyayen Zuwairan suka bu aci ganinsa sannan ya wanke afa yaje can Yoben,Maman ta asalinsu Shuwa ne sai Baban ne fulanin Yobe,lokacin da Sani ya gabatarwa Iya zancen sam ba haka taso ba,ta so ya samu yarinya a kusa yai aurensa ko don sau in bincike amma ya dage shi sai Zuwaira,Alhaji Amadu yace a barsa da za insa ya tashi qanninsa da wani abokinsa ya tura su Yobe domin bincike,aka tabbatar musu da Iyayenta mutanan kirki ne..... ansabo ce# [12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *TAIMIYYAH* Ayshat ansabo Lemu *Page10* Ba'a auki wani dogon lokaci ba aka sanya ranan auren Sani da Zuwaira,kwanaki suka cigaba da shu awa har zuwa lokacin da aka aura aure aka akko Amarya daga Yobe aka kawo masa ita Zaria,Iya da an uwanta sun sha hidima TAIMIYYAH ma ba'a barta abaya ba wajen hidima da ba i,har zuwa lokacin da taro ya watse aka bar Amarya da Angonta,Amarya Zuwaira bata wani jima ba ta fara bayyana halayyanta tsaf,irin matannan ne masu hassada da ba in hali,tunda ta fahimci matar wan mijinta wato Zainab TAIMIYYAH ta fita hutawa,mijinta yafi na ta wadata shikenan ta auki karan tsanan da nuna kishinta afili akan TAIMIYYAN,kai kace sun ha a miji aya ne,Iya tun ba ta kula da yadda Zuwairan ta fara nunawa Zainab munanan halaye har ta karanci inda Zuwairan tasa gaba,hakan yasa ta zaunar da Zainab tai mata nasiha akan cewa sam ko da wasa kada ta biye ta Zuwairan har wataran aji kansu,ta kama girmanta a matsayin ta na babba kuma mijinta shine gaba dana Zuwairan,Zainab TAIMIYYAH ta auki nasihan Iya da girma sosai,kuma sai akai sa'a ita in me tsananin takatsantsan da kauda kaine,sam bata shiga shirgin Zuwairan tunda ta gane inda tasa gaba,ta maida hankali da kula da karatunta da Mijinta idan yana gari,a hankali watanni suka fara shu awa cikin da Zuwaira ke auke da shi ya fara turowa,wanda sam babu wanda yasan da samuwansa daga Iya har Zainab in,domin sam Zuwairan bata shiga shirginsu ko Iya bata damu da zuwa Sasanta ta gaida ta ba,sai ta busa iska wanda sam Baba Sanin bai san da hakan ba,Sosai Iya har ma da TAIMIYYAH sukai murnan samuwan cikin,Iya ta dage da yiwa TAIMIYYAH addu'an itama Allah ya kawo mata nata rabon,amma shiru kake ji har zuwa lokacin da cikin Zuwaira ya isa haihuwa,ta haifo anta Namiji ato wanda bai baro komi ba a kamannin ubansa,Kyakykyawan gaske duk wanda ya zo barka sai yayi santin yaron kaman a auke a gudu,tunda Zainab TAIMIYYAH ta aura ido akan yaron taji duk wani soyayyanta akan yara da take dannewa don kada a fahimci rashin samun haihuwan su na damunta,sai ya taso gaba aya ta ji wani irin son yaron ya dira a zuciyanta,duk wani motsin Zainab TAIMIYYAH akan yaron ashe Zuwaira na ankare da ita,aiko ana gama shan shagalin suna aka watse aka bar Zuwairan da wata Innar ta da zatai mata zaman Jego,sai ya zama duk lokacin da Zainab zata shiga don duba jaririn da yaci suna Abubakar Sadeeq sai Zuwaira ta tsiri aukansa ta ri e,ko ta iri ba shi Nono sam bata bari yaje hannun TAIMIYYAH sai idan ta shigo yana hannun Inna shine Innan zata bata ta auka,tun TAIMIYYAH bata fahimci Zuwaira ba ta son ta da anta ba har ta gane,hakan kuma ya ta a zuciyanta matu a,har da ta koma sashinta sai da ta zubda hawaye,karon farko da taji tana tsananin son haihuwa,Iya ma ta da e da gane cewa Zainab in tunda Zuwaira ta haihu ta fito da son haihuwanta a fili,hakan yasa watarana ta zaunar da ita tana mata nasiha da kwantar mata da hankali akan cewa komi na Duniya rabo ne kuma yana da lokaci,kada ta saka damuwa a ranta suma nasu rabon nanan zuwa,TAIMIYYAH taji kunya sosai a lokacin amma daga baya kaman yadda Iyan tace ta dagene da addu'a hakan ya kasance,duk idan tasa goshinta a asa sai ta ro i Ubangiji ya basu rabo me anfani,amma fa soyayyan da takewa Sadeeq ya i barin zuciyanta sai dai taja baya sosai da kai kanta Sasan Zuwairan da sunan taje aukan mata yaro tunda ta nuna bata so,don tana da matu ar gudun zuciya,takan gansa ta auke shi idan Inna takaiwa Iya shi,a haka rayuwa ta cigaba da gangara musu sam Sameer bai ta a nuna damuwansa akan rashin haihuwan su ba,kuma sosai Allah ke ara masa bu i yana matu ar samu da kasuwancinsa da yake,ga kuma arin promotion da yake samu a wajen aiki,lokacin da Sadeeq ya samu shekaru biyu da watanni a lokacin Zuwaira ta sake samun ciki,a kuma lokacin ne Allah yai ikonsa akan su Zainab itama ya bata
Chapter 15 · 0% Book details