← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 184

Sashe 74

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ita kuma TAIMIYYAH da sam hankalinta bai kai kan me Napep da ke
arin tsallakowa wajenta ba,ganin kamar mota da mashin
in dake tahowa a nesa suke,sai kawai ta nufi titin gadan-gadan tana dafe da
afarta don tsallakawa,sai da ta shiga tsakiyan titin ta kula da me mashin
in daya taho a guje,sai tayi baya don komawa
aya
arayin ba ta san mota ta taho ba, kawai ji tayi an wantsakali da ita can gefen titin kanta ya bugu da dakalin kwalbatin bakin hanya.

Lokaci guda ita da me Napep
in da ya taho don taimakonta suka saki ihu,me motar da ya ka
e ta yayi saurin gangarewa gefen hanya ya faka motar suka nufo inda TAIMIYYAH take a yashe shi da matar da ke cikin motar.

TAIMIYYAY da ke yashe a gefen kwalbatin sai zubar da jini take, da alamu wani waje a fuskarta ko gefen wuyarta ne ya tsage ko ya fashe shiyasa jini ke zuba sosai.

Gabaki
aya kanta yayi wani irin nauyi gingirin,sabida ba
aramin bugawa tayi ba tama kasa kuka,sai idanunta da ta lumshe tana jin wani azaba na ratsa hannunta da ta dur
ushe akansa.Sama-sama take jin maganganun wanda ya ka
etan da muryar wata mata da ke faman salati tana cewa, "Shehu maza ku
auke ta zuwa mota wannan jinin da take zubarwa yayi yawa."
Babu
ata lokaci Shehun ya kwashi TAIMIYYAH zuwa mota,wacce jikinta ke faman rawan
ari sabida ruwa ake she
awa har lokacin.Dama ga shi ita ba mai son ruwa ya ta
a lafiyar jikinta bace, shiyasa kafin kace kwabo ha
oranta har sun fara karo da juna,ga jinin da ya
i tsayawa wanda ke zubowa daga gefen wuyarta da ya tsage sosai.

Hajiya Aysha da ke ri
e da ita a jikinta salati kawai take yi tana
arawa, cikin tsantsar tashin hankalin wannan tsautsayi daya gitta musu.Shehu ne ya mi
o jakar TAIMIYYAH daya
akko daga bakin kwalbatin ya aje kusa da Hajiyan,ya zagaya ya koma mazaunin driver ya tashi motar yana tambayar Hajiyar wani asibiti za su nufa?

Hajiya Aysha dake ri
e da TAIMIYYAH wacce Hajiyar ta sanya
ankwalin kan TAIMIYYAH ta
aure wajen da jinin ke zubowa tayi saurin cewa Shehu, "Muje ABU tudun wada kawai Shehu don gara a kaita asibitin da za a duba ta da kyau."
Tana maganan ne cike da tashin hankali musamman yadda taji jikin TAIMIYYAN ya fara
aukan zafi.Har lokacin jikinta rawar sanyi take yi, ha
oranta na faman dukan juna,suna isa asibitin Shehu yai farking motar lokacin ruwan ya
an tsagaita babu laifi.

Cikin
anin lokaci aka zo aka
auki TAIMIYYAH don ta kasa tafiya sabida yadda jikinta ke faman rawa,sai a lokacin kuma Hajiya Aysha ta kula da cewa tana lalurar
afa ma.Hakan yasa tausayin halin da yarinyar ke ciki ya ninku a zuciyarta,bata samu nutsuwa ba sai da aka baiwa TAIMIYYAH gado tare da bata kulawar gaggawa don tsaida jinin dake zuba har lokacin........
ansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.

Za ku iya min magana ta wannan number
in 08167768704, ko kuma ku turo ku
in ku kai tsaye ta wannan account
in 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line
in 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line
in 08167768704.
_Ina
an kasuwa masu bu
atar a tallata muku hajar ku?

Maza ku garzayo da ku
alilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don bu
atan sayan kayan ku,ku tuntu
eni ta layina kamar haka 08167768704._
*48*
Lokacin da Likitan ya kammala baiwa TAIMIYYAH duk wata kulawa da ta dace,sai ya yi mata
inki a wajen daya tsage daga gefen wuyarta na hagu inda jinin ke zuba,sannan ya yi mata allura tare da
aura mata drip.

Yana juya ya yiwa Hajiya Aysha bayani akan dole admiting
in patient
inta za a yi ta samu kaman kwana
aya da yini, sabida buguwan da tayi a hannunta na dama,da kuma ciwan kai da take kuka da shi.

Hajiya Aysha sai ta gya
a masa kai cike da gamsuwa tana fa
in, "Okey!

Babu damuwa." Tayi maganar lokacin da take
arisawa bakin gadon da TAIMIYYAH ke kwance, idanunta a lumshe amma hawayene ke zubowa daga idanunta yaba sauka a kan kyakykyawar face
inta.

Sai lokacin ne ta samu daman kuka dukkanin inda ta bugu na mata tsananin ciwo,ga kanta da take ji tamkar xai rabe gida biyu ne.

Muryar Hajiya Aysha da ta jiyo daf da ita yasa ta bu
e idanunta da sukai mata nauyi, ta sauke akan kyakykyawar face
in matar da bata san ko wacece ita ba, Hajiyan ta dubi TAIMIYYAH da ta zuba mata ido tace, "Sannu Zainab." Don taji lokacin da TAIMIYYAH ke sanar da likita sunanta.

TAIMIYYAH ta maida idanunta ta lumshe bayan ta amsa sannun can
asan ma
oshinta, ta sake bu
e baki a hankali tana cewa, "Don Allah a
auki wayata a kira min Iyah."
Hajiya Aysha ta jinjina kai tana cewa, "Nima tunani na kenan,sannu Allah ya baki lafiya kiyi ha
ury komi ya farune bisa tsautsayi da
addara ,don tu
in ganganci ba halayyar Shehu bane da alamu ke ce kika shiga titin cikin ru
u ba yadda ya dace ba,Allah ma ya auna arzi
i da ba wani mummunar rauni kika ji ba, buguwace kawai inji likitar sai
inkin da akai miki a inda kika sami rauni."
Ita dai TAIMIYYAH jin Hajiyar kawai take yi sama-sama don bacci ya fara rinjayar idanunta, sabida alluran da akai mata.Hajiya Aysha ta nufi in ta aje jakan TAIMIYYAH kusa da nata,ta bu
e tana ciro wayarta tai swiping sai ta ga babu lock,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciyar tana shiga contact kai tsaye don lalubo sunan Iyah data ji TAIMIYYAH ta ambata.

Cikin sau
i ta gano sunan ta kuma dannawa layin kira, kasancewarta wayayya da ta saba anfani da manyan waya na zamani.

Bugu biyu muryar Iyah ya shiga kunnuwarta lokacin da take fa
in, "Salamu alaikum!

Zainab kina ina ne har kika bari yamma tayi miki a waje?"
Hajiya Aysha tayi saurin cewa, "Barka da yamma Hajiya ba mai wayar bace,wallahi ta ha
u da tsautsayine gamu nan a asibitin ABU da ke Tudun Wada Zaria."
Tana jiyo yadda Iyah ta rafka salati kafin ta furta, "Subhanallahi!

Amma dai da sau
i ko baiwar Allah?"
Hajiya Aysha tayi ma Iyah bayani yadda hankalinta zai kwanta,kafin suyi sallama Iyan na sanar da ita gata nan bisa hanya yanzu Insha Allah.Sai Hajiya Aysha ta sauke wayar daga kunni tana maida shi cikin jakar TAIMIYYAH ta koma bakin gadon tayi tsaye, tana
arewa kyakykyawar face
in TAIMIYYAH wacce barci yai nasaran
aukarta kallo.

Hajia Aysha ta dinga yaba kyawun yarinyar cikin zuciyarta, tare da jin tausayinta me tsanani lokacin da idanunta ya sauka akan
afafun TAIMIYYAH,wanda
aya ya sirance sai lafiyayyen dake da
ibarsa.

Ta sauke numfashi tana kai hannu ta gyara mata rigar jikinta da kyau ya rufe
afafun sosai, ta isa ta zauna a kujeran da ke
akin tana sauke zazzafar numfashi.

Shehu driver ne ya shigo yana tambayar jikin TAIMIYYAH Hajiyar ta bashi tabbacin da sau
i sosai,tunda buguwace kawai sai
inki da akayi a wajen daya tsage.

Shehu ya yi fatan samun sau
i ga yarinyar yana komawa waje ya zauna cikin mota, kamar yadda Hajiyar ta bashi umurni tare da sanar da shi zasu jira Mamar TAIMIYYAH ta zo kafin su bar asibitin.

Mintuna talatin da biyar sai ga Iyah sun iso asibitin tare da Sani da ya kawo su ita da Babah Ladi.

Iyah ta
aga waya ta kira layin TAIMIYYAH sai Hajiya Aysha ta
auka, tana sanar da Iyah gata nan fitowa ta taho da su,ta kashe wayar tana fitowa kai tsaye zuwa waje, cikin sa'a sai ta hango Iyah da Babah Ladi daga can nesa su na faman dube-dube.Ta isa wajensu suka sake gaisawa da jajanta abinda ya faru,kafin su
arisa zuwa
akin da aka kwantar da TAIMIYYAN.
Chapter 74 · 0% Book details