← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 184

Sashe 62

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin data dawo hannunta ri
e da plate
in data zubowa TAIMIYYAH Jallop
in shinkafa,wanda ya ji busassshen kifi da nama aciki,sai ta aje plate
in akan gado tana cewa, "Ga abincin ki tashi ki ci bari inje in
akko miki magani a
akin Abbah."
TAIMIYYAH ta tashi ta zauna tana fara cin abincin a hankali.So take ta
arfafa kanta ko zata samu nasaran barin garin a gobe,don ta san idan ta cigaba da nuna bata da lafiya to Guggo Bilki ba za ta ta
a bari ta tafi a goben ba.

Shiyasa lokacin da Yasmeen ta kawo mata maganin ciwan kai da zaza
in,sai ta amsa ta shanye tana aje cup
in ruwan dake hannunta ta dubi yasmeen
in tana cewa, "Alhamdulillah!

Har na
an ji ciwan kan ya fara sauka,in gaya miki Mamienku na fita ba sai ciwan kai ba,na fara jin sanyi alamun zazza
i shine fa naje na tara kaina a shower ina fitowa kuma sai rawar sanyi ba,na kifa ciki nai ta kuka ashe
arawa kaina wahala nake, kaina ya
auki wani irin ciwo,gaskiya gobe sai gida don na kula kaman zaman garinnan ciwo zai sani in kwanta,na gaji hakanan gobe gida zan koma gaskiya."
Yasmeen data tsurawa TAIMIYYAH ido ta balla mata harara tana cewa, "Aiko baki isa ba sai next week zaki tafi,ba wani ciwan da zaki kwanta in Allah ya yarda.Ke
ince kin cika raki abu ka
an duk ki narke ki ta faman kuka,ni wallahi har kin bani tsoro da na ga yadda idanunki suka kumbura."
TAIMIYYAH ta narke face cike da shagwa
a take cewa, "Seriously Yasmeen hankalina yayi gida,ai nayi
ary yau fa sati na
aya kuma dama ai sati
aya nace zanyi, monday zamu koma skull don haka ni da gaske nake yi gobe zan koma, zan ma kira Iyah in sanar mata a turo Sani da wuri ya
auke ni,tunda ku ma kai Amarya za ku tafi goben."
Yadda Yasmeen ta ga TAIMIYYAH tayi maganan da serious sosai yasa ta gama gane rigimi take ji,kuma da gasken take yi hankalinta ya yi gida.Sai ta dubi TAIMIYYAH tana cewa, "To shikenan bari Mamie ta dawo sai aji me zata ce."
TAIMIYYAH ta wani kwa
e fuska take cewa, "Oho!

Ni dai babu wani da
in bakin da za a min gida zan tafi gobe Allah kuwa."
Kafin Yasmeen tace komi sai ga kiran Iyah ya shigo wayar TAIMIYYAH,ta
auka cikin sauri tana fa
in, "Hello!

My Iyah kaman kin san ke zan kira yanzu wallahi,ina yini dafatan kuna lafiya?"
Daga
angaren Iyah ta amsa da cewa, "Lafiya lau Zainabu ina fata goben dai zaki dawo ko?

Duk kewanki ya dameni
azu ma Ummien ku da ta shigo take tambayan yaushe zaki dawo." Iyah ta dakata tana sauraran me TAIMIYYAH zata ce daga nata
angaren,TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya tana cewa, "Eh gobe zan dawo Iyah Insha Allah,maganan ma muke da Yasmeen kika kira yanzu,sai ki ma Sani magana tun yau ,gobe idan Allah ya kaimu sai ya taho da wuri mu dawo."
Iyah daga
angarenta ta jinjina kai kaman TAIMIYYAH na ganinta kafin ta furta, "Hakane zan masa magana yanzu ma muna gama wayan da ke,ina su Bilkin suna ta biki tace ke kin
i shiga cikin mutane,nace mata to ina ta ga kina zuwa bare ki saki jiki da mutane dama,gara ki yi dawowarki gida hakanan,dama ai kwana bakwai kika ce za ku yi ku koma makaratar da kike zuwa
in ko?"
TAIMIYYAH ta jinjina kai cike da shagwa
a take cewa, "Eh Iyah wallahi duk na
osa in dawo nayi kewarki sosai." Daga haka suka
an ta
a hira da Iyah kafin suyi sallama da juna akan cewa Iyan zata kira Sani,gobe da wuri sai ya kamo hanya.Yasmeen da ke zaune tana jin wayan TAIMIYYAH da Iyah ta zabgawa TAIMIYYAH harara tana cewa, "Ai saiki ta tafiya goben kifi ruwa gudu ma idan kin so."
TAIMIYYAH ta saki wani murmushin ya
e, tana jin relief a zuciyarta da Iyah ta goya mata baya ta koma a goben,ta dubi Yasmeen tana cewa, "Sorry Babyn Aliyu,da gaske hankalina yayi gida ne."
Yasmeen ta ta
e baki tana fa
in, "To ni bari na koma tunda naga kin ji sau
i,ko kawai ki tashi ki shirya mu koma tare,ke kanki idan kika shiga cikin mutane za ki ji da
Babu musu ko TAIMIYYAH ta tashi, har abin ya so baiwa Yasmeen mamaki,amma sam bata kawo komi cikin zuciyarta ba illa bin TAIMIYYAH da kallo da tayi,lokacin data isa wajen kayanta tana ciro rigan da zata saka.

Wani ha
en doguwar rigan Swiss Excelsior ta sanya,kalan maroon and milk da akaiwa touch da black ka
an-ka
an a jikin kwalliyar.Kalan yayi wa TAIMIYYAH kyau sosai kasancewarta fara,gashi
inkin ya zauna a jikinta wanda ya kasance yankan A-shape ne.

Ta nufi wajen mirrow tana
aukan powder ta murza ka
an,sai tayi lining manyan idanunta da eye liner.Take fuskarta ya
auki wani irin kyau da
yalli don ma idanun nata sun
anyi ja sabida kukan data sha,amma duk da hakan tayi kyau ba ka
an ba, musamman lokacin data kafa
aurin ture kaga tsiya,tai
an baya dashi ka
an bai cokaro gaban goshi sosai yadda wasu ke yi ba.

Yasmeen data zuba mata ido ta bu
e baki tana fa
in, "Masha Allah,wannan irin kyau haka TAIMIYYAH gaskiya kullum ki dinga wa Allah godia wanda ya kyautata halittarki,Masha Allah!

Masha Allah!

Da wannan kyakykyawar halitta."
TAIMIYYAH ta
an harareta ka
an tana fa
in, "Zaki fara ba,godia kam kullum cikinta muke Yasmeen,muje don Allah ni karki tasani kina faman yabon kyawu kaman baki ta
a ganin kyawawaba sai ni."
Yasmeen data mi
e tana
aukan mayafinta ta yafa,sai ta dubi TAIMIYYAH tana fa
in, "Ke dai kawai ayi shiru yanzu dai saka
an-kunni mu wuce,hakan zai sake fito da kwalliyarki, ke baki son saka
an-kunni."
TAIMIYYAH ta
auki wasu
an-kunninta da ke saman mirrow
in ta sanya,aiko nan da nan kwalliyarta ya sake haskawa.
auki wayarta bayan ta yafa gyalen daya shiga da kayan jikinta,ta dubi Yasmeen tana cewa, "Muje Yasmeen kin tsaya sai kallona kike yi." Yasmeen ta saki murmushi tana yin gaba TAIMIYYAH ta biyo bayanta.

A falo s
ukai arba da Yah Emran zaune daga
angaren dining,ya sauya shiga daga farar shaddar
azu zuwa
ananun kaya.

Kallo
aya TAIMIYYAH taiwa wajen da yake zaune,
irjinta ya buga da wani irin
acin rai,da sauri-sauri take dafa
afarta me laluran tana tafiya har ta fice daga falon,yanayin da suka kasance ciki a
azu na dawowa kwanyanta.

Emran da Yasmeen ta tsaya yi masa magana yabi bayan TAIMIYYAH da kallo,yana jin wani yanayi na sake taso masa,don wankanta ya cijesa matu
a.Cikin zuciyansa yake fa
in 'Gaskiya Yarinyar akwai body da laushin jiki,ga kyau babu
arya kawai nakasanta shine illarta."
Maganan da Yasmeen tayi ne ya dawo dashi daga zancen-zucin daya tafi,tana cewa, "Yah Emran ina magana,nace zan samu 5k
in ne ko mu wuce kawai?"
Ya sauke manyan idanunsa akan Yasmeen
in yana cewa, "Bani da cash a jikina yanzu, amma zan miki transper ki turo min details
inki har dana Zaynab zan saka muku ku
in." Daga haka ya maida idanunsa akan abincin da ya zuba bai sake duban Yasmeen dake masa godia ba.

Itama ganin hakan yasa ta fice ta cimma TAIMIYYAH a waje tana tsaye jingine da jikin gate tana jiran fiwowan Yasmeen
Lokacin da Yasmeen ta
ariso sai da TAIMIYYAH tayi mata mitan da
ewan da tayi bata fito ba.Yasmeen ta sanar da ita abinda ya tsaidata,sai kawai TAIMIYYAH ta ta
e baki bata kuma magana ba har suka samu abin hawa suka isa gidan bikin.

Basu dawo gida ba sai dare don tara da rabi ma ta wuce suka shigo gida.Tun a gidan bikin dama TAIMIYYAH ta sanar da Guggo maganan tafiyarta a goben.

Da Guggo Bilkin tace tayi ha
ury har zuwa monday su dawo kai Kausar Amarya,wacce za a kai Katsina amma sai TAIMIYYAH tace wa Guggo Bilki ai har sun gama magana da Iyah, gobe da wuri Sani zai zo su wuce.

Tunda Guggo Bilki ta ji cewa Iyah za ta turo Sani tasan zance ya
are,hakan yasa ta amsawa TAIMIYYAH da cewa Allah ya kai su goben lafiya.

Yanzu da suka dawo daga gidan bikin sai kawai TAIMIYYAH ta hau ha
a kayanta.Yasmeen na taya ta tana mitan yadda TAIMIYYAN ta dage,sai ta tafi kaman wata wadda akai alluran tuburewa.

Ita dai TAIMIYYAH jin Yasmeen kawai take yi,don ba za ta iya sanar da ita irin halin
uncin da zuciyarta ke ciki, akan tozarcin da Yayansu yai mata a
azu bane,shiyasa kawai taja bakinta ta
inke.Suka cigaba da kammala shirya kayanta cikin akwati,Yasmeen
in ta fice daga
akin ta bar TAIMIYYAH na yin waya da Maryam Sanusi.

Washegary da wuri TAIMIYYAH ta tashi sukai sallama da Yah Anas da Ahmad kafin su fita wajen aiki.Kowannensu sai da ya bata ku
i tai musu godi,mutumin nata Emran ne kawai basu ha
u ba.

Lokacin data je gaida Abbah shi ma ku
in ya bata dubu goma yace ta sayi kayan kwalliya,ta amsa tai godia tana fitowa daga
akin Abban.

Ta sanyo kai don fitowa kenan Emran da zai shiga
akin na sanyo kai, saura ka
an suyi karo TAIMIYYAH tayi saurin yin baya ta bashi hanya.Ya shige yana barin mata qamshinsa na turaren SAUVAGE DIOR.

Ta wuce cikin sauri tana jin daga
amshin har mamallakinsa ta tsanesu tsana me tarin yawa.Koda ta isa
aki lokacin Yasmeen ta fito wanka tana shafa ne,TAIMIYYAH ta zauna daga bakin gado tana zube ku
in da ke hannunta.

Ta toilet direct itama ta yo wanka ta fito,cikin sauri ta gama shirinta tsaf cikin wasu riga da skat na atamfa.Suka fito tare da Yasmeen sukai breakfast TAIMIYYAH na ji cikin ranta duk ta
osa Sanin ya iso.
arfe tara da rabi Sani ya iso garin Kano.Bayan an kai masa abin karyawa ya ci ya huta, wajen 11 suka kamo hanya da TAIMIYYAH,bayan su Yasmeen da Guggo Bilki sun yo mata rakiya har bakin mota.

Yasmeen har da kukanta lokacin da TAIMIYYAH ke
aya mata hannu,itama kanta TAIMIYYAH sai data share hawaye.
Chapter 62 · 0% Book details