← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 184

Sashe 150

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baban Basmah wani magana na ke ta ji yana tasowa, shi ne na ce ni dai ba zan gasgata kowa ba sai na ji daga gareka."
Umma ta yi maganar idanunta akan Baba Sani da ya kammala yin wayar, ya maido hankalinsa gareta sabida yadda ta kwantar da murya tana magana, jin ta dakata da alamu tana son jin ta bakinsa ne sai ya ce, "Wani magana ki ka ji Zuwairah?"
Umma ta sake nutsuwa sosai tare da kwantar da murya ta ce, "Ji na yi wai za ka sake aure, shi ne abin ya
aure min kai don dai na san da gaske ne, ni ya kamata na fara sanin hakan ba wai in tsinci magana a gari ba.

Da gaske Baban Basmah kai ne za ka yi auren ko kuma auren Sadeeq ne ake jujjuya zancen ana cewa kai ne za ka auro min abokiyar zama?"
Umma ta kai
arshen maganar da tambayarsa tana sake aro jarumta da nutsuwa ta sanyawa kanta, Baba Sani ya dubeta da kyau kafin ya saki
aramin murmushi ya ce, "Zuwairah a bakin wa ki ka fara jin wannan jita-jitar?"
Umma sai ta rasa abin cewa don kuwa bata san a wajen wanda za ta ce ta ji wannan maganarba, sabida babu wanda ya tare ta da magana akan wai Baba Sani zai sake aure, a bakin Boka Kallah kawai suka ji hakan, ganin yadda ya tsareta da ido yasa ta tsuke fuska ta ce, "Maganar duniya ai bata
uya Baban Basmah, kuma shi
arin aure ai lokaci ne amma ni abinda na ke son ji kawai shi ne da gaske ne ko bada gaske bane?"
"Da gaske ne Zuwairah tabbas zan
ara aure, dama ina shirin nufarki da maganar cikin wannan satin."
Baba Sani ya yi maganar idanunsa akan Umma,wacce zallar ka
uwa ya sanyata zubar da duk wani jarumtar bogi da ta ara ta yafa, cikin rawar murya ta ce, "Da gaske ne Baban Basmah amma shi ne ka kasa sanar dani hakan, sai da na tsinto maganar daga waje, wace ce wacce za ka aura
in tuh?"
Baba Sani ya
an ha
e fuska yana duban Umma da wani irin kallo ya ce, "Zuwairah ba wai na
oye miki maganar bane sabida abin ne zai zo da gaggawa, kuma maganar wace ce duk ba huruminki bane, za ki sani idan lokaci ya yi abinda kawai na ke so ki sawa ranki shi ne, aure lokaci garesa kuma ina fata za ki goya min baya ku zauna lafiya, duk da cewa ba waje
aya za ku zauna ba ita zan tafi da ita can Kano ne."
"Kutumar ubancan kai!!!

Sani kasan me kake fa
a kuwa, kana nufin ni zaka bari a Zaria zaman jiran gida, ka
auki Amarya ka maida kusa da kai kuna holewarku ni ina zaman jira sai weekend ya zo ka le
o ka koma?"
"Haka na ke nufi Zuwairah kuma babu wanda ya isa ya sauya hakan, tun da fari babu yadda ban yi da ke akan mu tattara mu koma can da zama ba, amma kika nuna cewa ke ba za ki iya zama da kanawa ba kin fi son zaman Zaria.

Don haka a yanzu ma ba za ta canza zani ba, anan
in za ki cigaba da zama."
Umma da ta tsurawa Baba Sani ido tana jin tamkar ta fasa ihu sai ta yi
arin danne zuciyarta, sabida tunowa da hu
ubar Hajiya Barirah da ta yi, ta bu
e baki cikin son danne zuciyarta ta ce, "Ni yanzu abinda ya fi damuna wace ce budurwace ko bazawara?"
"Bazawarace Zuwairah sanin wace ce ita idan kin kwantar da hankali nan da lokaci ka
an za ki sani."
Daga haka Baba Sani bai sake bu
ewa Umma komi ba, duk iya nacinta akan ta san ko wace ce wacce zai aura da kuma sanin yaushe ne auren ya
i bata damar hakan, daga
arshema sai ya tashi ya ce mata fita zai yi zuwa can Fam House
in su.

Yana barin gidan Ummah ta
ule a
akinta ta kira layin Hajiya Barirah, ta zayyane mata yadda suka yi da Baba Sani ta
are maganar da cewa, "Hajiya Barirah tabbas kwanan nan hawan jini zai mun mummunar kamu, domin bana iya bacci sabida ru
u da shiga tashin hankali, na rasa da wani kalar masifan zan ji, da ta
a ko ta Sani da
arin aurensa?

Duk iya yadda na yi akan ya sanar dani ko wace ce wallahi kaucewa ya yi, sannan babbar tashin hankalina shi ne tafiyar da zai yi da ita can Kanon, Hajiya Barirah ki dubi girman Allah ki sanar da ni menene mafita ?"
Hajiya Barirah daga
angarenta ta ja numfashi ta ce, "Hajiya Zuwairah har kullum ina sanar da ke illar gaggawa a yayinda da ka ke son lamura su daidaita, ko ka gano bakin zaren wani abu da ka ke so.

Ki sanya nutsuwa ki cigaba da bin sa a hankali, ko ka
an kada ki nuna masa hankalinki ya tashi da zancen aurensa, maganar tafiya da ita can in da yake aiki kuwa, ni banga abin tashin hankali ba su tafi ma bangon duniya, ke dai idan akai aikin da zai dawo tafin hannunki ba shikenan ba."
Umma ta numfasa tana cigaba da sauraren Hajiya Barirah, wacce ke cigaba da bata shawarar yadda za ta kwantar da hankalinta, har zuwa lokacin da za su gano wace ce Baba Sani zai auro
Lokacin da suka gama waya da Hajiya Barirah ne ta kira layin Zuhurah amma wayarta a kashe, sai ta dafe goshinta tana jin zuciyarta na sake
aukar zafi.

Gaba ki
aya bata san yadda za ta kwatanta irin ru
anin da ta ke ciki ba, burinta kawai ta san wace ce ke shirin kutso kanta cikin rayuwarta da gaggawa haka?

Misalin
arfe uku na yammah Ummah na zaune tare da wata ma
wafciyarsu, wacce suke business
in siyar da atamfofi tare me suna Hajiya Jummai, sai ganin shigowar Zuhurah suka yi kamar daga sama.

Ummah ta yi saurin tashi tsaye a firgice tana sauke idanunta akan Zuhurah da ke janye da
atuwar luggage, duk fuskarta ya ko
e ta yi wani firgai-firgai alamun tana cikin rashin kwanciyar hankali, ta bu
e baki ta ce, "Zuhurah sannu da isowa."
Umma ta yi maganar tana son
oye tashin hankalinta don gudun kada Hajiya Jummai ta fahimci wani abu, Zuhurah da ta fahimci in da Umma ta dosa sai ta saki murmushin
e ta ce, "Umma sannunku mun iso a gajiye ne bari in shiga daga ciki, Hajjaju ina yini mun sameku lafiya?"
Hajiya Jummai da ke bin Zuhurah da kallon
urillah ta amsa gaisuwar da fara'a tana cewa, "Amarya ce a gari haka sannu da zuwa barka da hanya."
Zuhurah ta amsa tana cigaba da jan Luggage
inta ta nufi hanyar corridor
in da zai sadata da
akinsu, Ummah ta rakata da ido kafin ta maido dubanta kan Hajiya Jummai tana
aro murmushi ta ce, "Hmm!

Yaran yanzu dai basa son zaman gidan miji idan ba suna tare da juna bane, wai tafiya ce ta kama shi zuwa wata
asa shine ta matsa sai dai ta dawo gida kafin ya dawo, tunda tafiyar ta zo daga sama ne babu yadda za a yi su wuce tare.

Na ce ta yi zamanta ko
annin mijin ne sai ta ro
a a tura mata su gidanta su tayata zama, amma kin ga sai da ta kamo hanya ta dawo gidan dai."
Hajiya ta saki murmushi ba don ta yadda da abinda Umma ta fa
i ba ta ce, "Allah sarki kin san kowa da irinsa ne, ita me
awazucin gida ce shiyasa, Allah ya dawo da shi lafiya aiba wani abin aibu bane."
Daga haka Ummah ta
atar da maganar suka koma tattaunawa akan kayan da za a turo musu cikin satin da za a shiga, rabin hankalin Ummah na ga Zuhurah duk ta
osa Hajiya Jummai ta tashi ta bar gidan.

Lokacin da sukai sallama da Hajjya Jummai ta tafi, cikin sauri Umma ta nufi
akin su Zuhurah zuciyarta na sake
aukar zafi.

A tsaye ta samu Zuhurah har ta fara jere kayanta cikin sif
inta, Umma ta zauna daga bakin bed tana cewa, "Yanzu Zuhurah sai da kika taho bayan na ce ki zauna mu ga abinda zai iya yuwuwa, kin fi so mu ji kunyar ma
iya kenan?"
Zuhurah ta dakata daga shirya kayan ta tako xuwa bakin bed
in ta zauna, ta dubi Umma cikin ido ta ce, "Ummah gara in ji kunyar jama'ar duka duniya da in cigaba da zama da Ameeru, don Allah ki dubi yadda na koma kwana takwas kawai da kaini gidansa.

Tun da aka kaini kwanaki biyu kacal na yi cikin farin ciki yana tarairayata, shi ma don yasan ya rabani da budurcina ne ya dinga rawar
afa, amma duk sauran kwanakin na yi su ne cikin
unci da tashin hankali, sabida sai ya shawo giyarsa daga waje zai shigo min a buge, kuma da zaran giyar ta sake sa akaina zai
arar da kuzarin da ya rage masa, da na yi magana ya ce zai doke ni,don haka ni kam ba zan iya wannan rayuwar ba Umma, sannan babbar abinda yasa na tsani Ameeru ya fita a raina shi ne, ba yaron Honourable bane ba a ma san cikakken asalinsa ba,
an me shara da wanke-wanken gidan ne, tsabagen samun waje ne ya ke abu tamkar
an cikin gida, sabida ya ga Allah bai ba Honourable
in haihuwar
a maza ba, shiyasa uwargidarsa ta ri
esa tamkar
an cikinta, tana
aure masa gindi yana famtamawa tamkar
an mai gidan.

Ba zan ta
a cigaba da aurensa ba ko a kotu ne sai ya bani takardata Umma, gara mu ji kunyar koma su waye da in cigaba da zama da shi rayuwata ta lalace."
Zuhurah ta kai
arshen maganar zuciyarta na sake
ashewa da jin tsanar Ameeru me tsanani, Umma da ta zura mata ido ita ma nata zuciyar ce ke sake cika da tarin ba
in ciki da jin tsanar Ameerun me zafi, sabida yadda ya rufesu a baibai bai ta
a sanar da su koda wasa, cewa bashi da wata ala
a ta jini da Honourable Attah ba.
Chapter 150 · 0% Book details