← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 184

Sashe 63

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sun
akko hanya da Sani wanda ke tu
insa cikin salama da
warewa.Idanun TAIMIYYAH suka sauka akan wajen ATM machines da ake cire ku
Tace wa Sani ya tsaya daga bakin hanya ta bashi ATM card
inta,ta gaya masa pin
in tace ya ciro mata duka dubu sha biyar
in da Yah Emran ya tura musu ita da Yasmeen a jiya.

Sani ya ciro ku
in ya dawo suka kama hanya bayan ya baiwa TAIMIYYAH ku
in da ATM card
inta.Sai ta sanar da shi cewa tana son ya kaita inda zata iya ganin nakasassu masu bara akan hanya,zata basu sadaka ne.

Sani ya kai ta inda yasan masu nakasa suna zama,kama daga gurugu har ma da makafi da kutare.

TAIMIYYAH ta rabar musu da duka ku
in sannan suka kamo hanyar Zaria.Tana ji zuciyarta na rage zafi da ra
in ba
in cikin da Yah Emran
in ya kimsawa zuciyartata,amma bata ji memory
in abinda ya yi matan zai goge daga kwanyarta har abada.

Ta kai bakin gyalenta ta
auke hawayen da suka ziraro mata..........
ansabo ce#
[12/14, 3:43 PM] +234 703 040 9541: *Littafin TAIMIYYAH paid book ne,ga duk wanda ta tsincesa a kowani irin group ne,kiji tsoran Allah karki karanta sai kin biya 500 naira only.*
*Za ku iya min magana ta wannan number
in 08167768704, ko kuma ku turo ku
in ku kai tsaye ta wannan account
0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line
in 08167768704.*
Masu turo credit za ku turo katin MTN na 500 ta wannan line
in 08167768704.
_*Ina
an kasuwa masu bu
atar a tallata muku hajar ku?

Maza ku garzayo da ku
alilan a tallata muku kayan siyarwanku sai dai kawai ku ji ana kiran waya don bu
atan sayan kayan ku,ku tuntu
eni ta layina kamar haka 08167768704.*_
*42*
*Zaria,Gonan Ganye.*
Motar Suhailah ce ta faka daga cikin parking space na gidan Hajjah.Ta fito sanye cikin lafaya me asalin kyau tsada ta yane jikinta daga sama har
asa,kai kace irin kanuri
innanne dangin shuwa.

Kalar Lafayar wani irin Blue ne da akaiwa ado da kalan Red and Black ha
e Silver ajiki.Tayi kyau da shigan sosai hannunta ri
e da key
in motarta da hand bag ta nufi cikin gidan.

Da sallama ta isa cikin falon Lubah me aiki ta amsa sallamar tana ma Suhailah sannu da zuwa,Hajjah ta fito daga
angaren kitchen kenan tayi arba da Suhailah.

Sai ta saki murmushi tana fa
in, "Ashe ma gaki kin iso yanzu muka gama maganarki a waya da Antinku Raliya,tana gaya min kin biya kinyi mata sallama tun
azu."
Suhailah ta aje bag
inta saman kujera tana
arin zama take cewa, "Wallahi Hajjah saloon na biya shiyasa,da tun
azu na iso nan
in,kuma na tadda har mutum biyu a wajen shiyasa na da
Hajjah da itama ta nema waje ta zauna ta jinjina kai tana fa
in, "Ai Maleek yace tafiyan ma ba gobe ba sai jibi,amma dai angama miki duk abubuwan bu
ata har garin kunu dana
an-wake duk an gama,ni kaina har na gama shiri amma na sanar masa kwana
aya zanyi na gama ganin wuri sai a dawo dani,bazan iya wata guda a cikin yara ba kamar mara fa
i haka kawai ba haihuwa ba bakomi ba."
Suhailah sai ta zum
ure baki tana cewa, "Kai Hajjah don Allah karki ce haka,ni wallahi ji nake yi kamar kada na koma indai ba za ki yadda ki bimu kiyi wata a can ba,ki daure Hajjah please!"
Hajjah ta girgiza kai tana cewa, "Wallahi bada ni za a yi wannan haukan ba,sai dai ki fasa bin nasa wannan matsalarku ne ke da shi,au kinga na manta jiya
awarki ta zo nan gidan,take tambayata wai ko kun bar gari ne ta je gidanku yafi sau uku mai gadi na hana ta shiga,baki ga abin arzi
in data kawo min ba gashi can a
aki banma juye su daga ledan ba."
Suhailah taiwa Hajjah
uri zuciyarta na
aci da jin kalmar sunan Zuby da Hajjah ta fa
a,ta ja tsaki tana fa
in, " Hajjah ita Zubaidan ce tazo har gidan nan
i?

Lallai ne wato tanan zata
ullo sabida nayi blocking duk wata hanyar ha
uwata da ita,to wallahi tayi kuskure kamar yadda Maleek yasa ai mata iyaka da shiga gidansa,haka zai sa ai mata iyaka da xuwa nan
in ma, banza kawai maciyiya amana."
Yadda Suhailah take magana cike da
acin rai yasa Hajjah sakin baki tana kallonta har ta kai aya.Kafin ta bu
e baki tana duban Suhailan take cewa, "Lafiya me kuma yafaru tsakaninki da ita,yadda naga kina jida wannan Zubaidar,me tai maki nacin amana ni Hajjah?"
Suhailah nan take ta zayyanewa Hajjah duk yadda suka yi da Zuby,har kawo
aukan numbern Maleek data yi ta ba Zubyn,da irin sa
onnin iskancin da Zubyn ta dinga tura masa bata rage komi ba ta zayyanewa Hajjah,ta kai
arshen maganan da cewa, "Shine yanzu don an toshe kafan da zata dinga shiga min gida,ni kuma nayi blocking line
inta shine zata zagayo ta
angarenki sabida tana son cusa kai a wajen Maleek taci amanata."
Hajjah da tsananin mamaki da takaicin Suhailah ya rufeta,ta ballawa Suhailah harara tana cewa, "Ai bai birgeni ba Maleek
in da bai amsa tayin aurenta ya aureta ba,tunda ke kin maida kanki sakarya shashasha..!!

Na rasa wani irin wauta kike dashi Suhailah,an gaya miki yanzu ana wani amintane yadda xamani ya lalace da cin amanan juna,hatta
an uwanka na jini baka tsira da ya ci amanarka ba indai akan abin duniya ne.To wallahi ki kuka da kanki tun wuri ki aje duk wani sakarci ki kama kanki da mijinki,me ma ya kaiki aminta da Bazawara kamarta da idanu a tsatstsaye na fitsara,to ai yanzu kinga ta fito miki da halinta dama ba sabida Allah ta shiga jikinki ba tana da manufa.To kurwanta kur akan ku daga ke har Maleek
in,Allah yai min tsari da ha
a zuri'a da irin su,tsaye kyam nake akanku ba dare ba rana,musamman Maleek da yake namiji sabida ina jiye masa ru
in zamani da sharrin ku
i,domin yanxu idon mutane da yawa na kansa maza da mata,shiyasa daga ance miki
arfe uku tayi na gama bacci kenan,ina kan sallaya ina mi
ama Ubangiji kuka na akan ya tsaremin gaba da bayansa,ya karesa daga dukkanin sharrin zamani da ru
insa,duk wacce xai saukar dashi akan hanya Allah ya shiga tsakaninsa da su.Don haka ina da ya
ini Ubangiji yana jina kuma yana amsa bu
atuna,daga ke sai shi nake kallo a matsayin sanyin idanuna Allah yai muku tsari daga dukkan sharrin na mutum da aljan."
Suhailah ta amsa da cewa, "Ameen ya hayyu ya qayyum Hajjah,Allah yaja kwana ya barmu tare har abada,yadda kike tsaye akanmu Allah ya bamu ikon yi miki biyayya har abada."
Hajjah ta amsa da cewa, "Ameen." Sannan ta cigaba da yiwa Suhailah fa
a da Nasiha akan ta kula,ta kuma yi hattara da sharrin
awayen zamani,ta kama mijinta da kyau ta aje duk wani sakarci,maganan haihuwa kuma ta dage da addu'a sai ta ga Allah ya kawo mafita cikin sau
i,idan ma har
addara zai sa Maleek sake aure duk ta barwa Allah ikonsa,tayi addu'a Allah ba zai kawo wacce zata cutar da ita ba.

Suhailah dake sauraren Nasihar Hajjah da kunnuwan basira duk sai jikinta ya yi sanyi.Wani irin
aunar Hajjah da ba zai misaltuba na sake mamaye zuciyarta,ta sani Hajjah uwa ce ta gari a wajenta wacce bata da tamkarta har abada,kuma tayi mata dukkanin gata da ko uwarta na raye iyakan gatan da za ta yi mata kenan.

Hajjah ta cike mata gurabe da dama cikin rayuwarta ta zame mata uwa kuma uba duk a lokaci
aya.Sannan bata barta haka ba sai da ta
auki aurenta ta baiwa nagartaccen tilon
anta,wanda duk duniya ba za ta iya ha
a soyayyarsa da kowa ba.

Hawaye suka cika idanun Suhailah a lokacin da zuciyarta ya tuna baya,tun daga kan tashinta a hannun Hajjah tun tana
ar shekaru biyar,har kawo kan aurenta da Maleek wanda akayi lokacin ba wani son ta yake a zuciyarsa ba.Ya dai amsheta ne sabida Hajjah da kuma soyayyar da ke tsakaninsa da mahaifiyarta da yake kira da Anty Hauwa.

Itace ka
ai ke masa wata irin azababbiyar soyayyah a lokacin, wanda hakan yasa Hajjah jajircewa har sai da Maleek ya amince da aurenta.Bayan anyi auren ne a hankali shi ma zuciyarsa ta kamu da
aunarta me
arfi.
Chapter 63 · 0% Book details