← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 184

Sashe 174

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TAIMIYYAH ta furta lokacin da ta sanya kanta cikin falon Umma,Zuhurah da ke zaune cikin falon hankalinta akan wayarta ta yi saurin
ago idanunta jin muryar TAIMIYYAH, ta akanta lokacin da ta cigaba da ratsowa cikin falon.

Wani irin kibiya ya cake ta a
ahon zuci lokacin da idanun nata suka cigaba da yiwa TAIMIYYAH rakiya har wajen seaten da ta nufa, ta cigaba da kallonta tamkar ranar ta saninta wani irin yanayi ke tasowa daga
asan zuciyarta yana bayyana a kan fuskarta.

"Zuhurah sannu da gida dafatan kuna lafiya?

Ashe haka abu ya kasance to Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairy."
TAIMIYYAH ta yi maganar lokacin da mazaunanta suka daidaita a cikin seater
in, kafin Zuhurah ta ce komi Umma ta fito daga cikin
akinta da alamu wanka ta yo, don kuwa gashi nan ta sha uban ado sai
amshi ke tashi a jikinta.

Idanunta ya sauka akan TAIMIYYAH da ke zaune cikin seater, lokacin da Zuhurah ta yi
arfin halin cewa, "Ameen na gode!"
Umma ta
ariso ta zauna akan kujera tana
arin saita kanta da zuciyarta da ke faman bugu, TAIMIYYAH ta zamo ka
an tana gaida Umma ta ce, "Umma ina yini mun sameku lafiya, ya
arin jiki kuma?

Allah ya
ara lafiya yasa kaffara ne."
Umma ta tsurawa TAIMIYAH ido tana jin wani abu na matse zuciyarta, da
yar ta fisgo kalmomi daga bakinta ta furta, "Lafia lau, jiki Alhamduillah!

Yaushe ku ka dawo kenan?"
TAIMIYYAH ta koma ta zauna sosai kafin ta ba Umma amsa da fa
in, "Yau kwanan mu biyar kenan Umma."
Umma ta kasa cewa komi illah cigaba da
arewa TAIMIYYAH kallo ita da shigar jikinta, gashi gaba
aya falon ya kaure da wani
amshin turaren TAIMIYYAH da ya kama komi nata, jin shiru babu wanda ya sake tanka ta tsakanin Zuhurah da Umma yasa ta mi
ewa ta dubi Umma ta ce, "Umma in ce ya
ariso ciki zai gaida ki."
Umma ta dubeta ta ce, "Shi wa fa?"
TAIMIYYAH ta sadda kai
asa ta ce, "Megidan nawa ai tare mu ke."
Daga haka ta nufi wajen corridor
in ta kora A.Maleek suka dawo cikin falon, yana ri
e da jakar tsabar da TAIMIYYAH za ta bai wa su Umma, daga Zuhurah har Umma wani abu ne ya daki zukatansu, ganin yadda ya ke biye da TAIMIYYAH ri
e mata da bag a hannu.

A.Maleek ya kwashi gaisuwa wajen Umma, Zuhurah ta gaida shi tana faman
arewa ha
uwarsa kallo, ya amsa da kulawa yana sanya hannu a aljihu ya irgo ku
in da bai san adadinsu ba ya ajewa Umma yana cewa, "Umma ga shi a siya lemu, Allah ya
aro afuwa."
Umma ta ha
iye wani abu me nauyi da ke neman danne
irjinta, ta mi
a hannu ta janye ku
in tana cewa, "An gode madallah!

Ai jiki ya warware gaba
aya Alhamdulillah!"
Ganin A.Maleek ya tashi don barin falon ya sanya TAIMIYYAH dubansa ta ce, "Hubby wannan ita ce Sis
ina Zuhurah ba ka gane ta ba ko?"
A.Maleek ya dakata daga tafiya yana juyowa ya zube idanunsa akan Zuhurah da ta
ura masa ido ya ce, "Ayyah!

Sorry Sis ai ban gane ba, da ya ke har akai biki ba mu ha
u ba ya ki ke?"
Zuhurah ta ji tamkar ta sanya ihu yadda salon muryar A.Maleek
in ke dukan zuciyarta, ta yi
arfin saita kanta ta ce, "Lafiya
alau wallahi!"
A.Maleek sai ya sake zura hannu a aljihu ya irgo ku
i ya mi
awa TAIMIYYAH ya ce, "My pure zuwa bata wannan."
TAIMIYYAH da jin kunyar sunan da ya kirata da shi agabansu ya sanyata sadda kai
asa ta amsa ku
in tana cewa, "Thank u!"
Daga haka ya yi gaba abinsa yana jiyo Zuhurah na biyo bayansa da godia, TAIMIYYAH ta mi
awa Zuhurah ku
in ta amshe, ita kuma sai ta
auki bag
in da Maleek ya aje ta ciro
ullin tsabar Umma ta aje a kusa da ita tana cewa, "Umma ga tsaraba ba yawa."
Umma ta sake ha
iye wani abu me
aci ta ce, "Madallah an gode, har da mu kuma a tsaraba lallai kam!"
TAIMIYYAH ta mi
awa Zuhurah bag
in tana fa
in, "Sis ga naku ke biyu Basmah biyu, sai ki za
a desighn
in da ya yi miki a aje mata nata, na so ace zan samu zuwa gidanta amma gobe za mu juya, sai na zo bikin Yah Deeku kenan zan sama time In Sha Allah."
Zuhurah ta amsa bag
in tana cewa, "Allah sarki mun gode TAIMIYYAH, Allah kai mu bikin lafiya ai ba damuwa."
Daga haka TAIMIYYAH ta yi sallama da su ta fito, suka yo mata rakiya da idanunsu tamkar za su cinyeta
anya.

Sai da TAIMIYYAH ta koma part
in Iyah sannan ta fito ri
e da robar dambun ta, ta nufi motar Maleek da ke tsaye ya bu
e mata seat yana jiran
arisowarta, ya amsa robar ya sanya a back seat bayan ta shiga ya rufe mata murfin motar.

"Umma ke kin ga yadda TAIMIYYAH ta koma kuwa, dama haka Mijin mata ya ha
u?

Tabbas ba mu kasance masu sa a ba kambala'i!

Aini duk ku
insa sunan da ya yi ban
auka ajinsa da ha
uwarsa ya kai har haka ba shiyasa har aure a gurguwarta."
Zuhurah ta yi maganar wutar hassad na sake cinye zuciyarta, Umma ta ha
iye wani abu me nauyi ta ce, "Hmmm!

Zuhurah kenan ke ta ha
uwar mijin ki ke yi bata yadda ya fara zama boyi-boyinta ba, baki ga shike ri
o mata jaka tabbacin sun gama samun kansa, bansan wasu irin Malamai Iyah ke bi akan wannan gurguwarba wallahi.

Don abin ya yi yawa kamarta musaka ace ta taka irin wannan matsayin alhali ku ba taka ba, tabbas rayuwata daga farkonta ne kawai na samu sa a, amma gashi yanzu da aka zo tsakiya za a tafi gangara gaba
aya abubuwa sun juye, dukkanin lissafina babu wand na yi nasaran lissafashi daidai Zuhurah!"
Umma ta kai
arshan maganar da wani irin tone me ta
a zuciya,wasu hawaye masu
umi suka zubo mata, ta kai hannu ta share tana bu
e ledar tsabarta lokacin da Zuhurah ke cewa, "Wallahi Umma wannan karon ba zan ta
a yin saken da ba zan shiga irin arzi
i ba ni ma, sai na dar je wallahi inaaa!

Ai ba zan sake wannan saken ba, dole mu ma ace ga wata a cikin ta taka gidan girma ta fantama."
Umma ta jinjina kai lokacin da idanunta ke sauka akan dalleliyar doguwar rigar da ke cikin ledar, ta zaro ta tana jin
aunar rigar na
arsuwa a ranta don ta san ba
aramin kyau za ta yi a ciki ba,
amshin da TAIMIYYAH da A.Maleek suka bar musu a cikin falon irin dai ta ke ji daga jikin rigar, wanda hakan ke alamta musu cewa
amshin ya kama komi nasu ne.

Zuhurah ta ciro nasu tana dubawa ita ma suna sake sakin zance da jin hassada da kishi me tsanani na danne zukatansu, Zuhurah ta kira Basmah ta labarta mata zuwan TAIMIYYAH, tare da zuzuta mata yadda ta koma wata irin classy woman, daga
arshen ta yi snaping ha
un Abayar da ta kawo musu tsara ta turawa Basmah. (Ni dai na ce an ji kunya, na
auka sabida hassada ba za ma ku kar
a tsarabarba).

Washegary TAIMIYYAH gidan Hajjah suka isa tunda safe, sai da suka tsaya suka
auki Suhailah a gidanta sannan suka wuce.

Hajjah ta tarbesu cike zallar farin ciki, ta dinga ji ina za ta sanya kanta da farin cikin ganin yadda TAIMIYYAH ta yi wani irin kyau da cika, da zaran kuma ta tuna jikarta ko jikan na
auke a mahaifar TAIMIYYAR sai ta farin cikin ya ninku.

A gidan su ka yi breakfast gaba
ayansu bisa babban dining, bayan sun kammala ne Suhailah suka ke
e da Hajjah a
aki, suna tattauna maganar business
in da Suhailah za ta fara, don ta cewa Hajjah tana bada jimawa ta bu
e shago ne a garin Lagos, wanda za a dinga shigo mata da Abayoyi
an gaske zuwa su Veils da takalma.

Hajjah ta bata goyan baya domin dukiyar gadon Suhailah na uwa da uba duk a hannun Hajjah suke a na
an juya mata su, kuma sun hauhawa babu laifi, daga
arsha Hajjah ta ce ta bar komi a hannunta za ta yi magana da A.Maleek
Hajjah ta jima tana ma Suhailah nasiha akan ta kwantar da hankalinta game da jinkirin rashin haihuwa, kada ta ce za ta sanya damuwa a ranta don Allah ya ba abokiyar zamanta rabo, In Sha Allah ita ma nata na tafe.

Suhailah ta rungume Hajjah tana kuka tare da sanar da ita cewa ta jima da sanyawa zuciyarta dangana, Hajjah dai ta dinga rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali, shi ma kuma A.Maleek Hajjah ta yi mai magana akan ya kula wajen kwatanta adalci, sannan ya zama me rarrashi da
arfafa zuciyar Suhailah, hakan zai sa hankalinta ya kwanta ta gane cewa ko bata haihu ba ba zai kasance me wofintar da ita da rashin nuna damuwa kanta ba.
arfe
aya suka bar Zaria bayan Hajjah ta cika su da tsaraban kayayyin amfani da za su nema, ita TAIMIYYAH har da su kayan ciye-ciye irin wanda ba a rasa me ciiki da cin su duk an tanadar mata.

Da yake flight
in 6pm za su bi zuwa Abuja, hakan a gurguje suka tsaya a gidan Ummie suka gaisa, tare da bata tsarabarta ko mintuna sha biyar ba su yi a gidan ba suka tafi, bayan A.Maleek shi ma ya yi mata alkhairy ya bata ku
i masu kauri.

A gidan guggo Bilkine ka
ai suka
an zauna har Suhailah ta ci dambun shinkafa da ya
auki hankalinta,tare da yi mata mugun da
i shi A.Maleek ruwa kawai ya sha ya jira su a mota tare da Yusuf driver, bayan ya aje wa Guggo Bilki ku
i ita ma.
Chapter 174 · 0% Book details