← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 184

Sashe 180

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma Zaynab ce ko?"
Suhailah ta
aga ido ta dubi namiji wani abu me
arfi na harbawa cikin zuciyarta, ta yi saurin aje macen a hankali daga gefe tana amsar namijin ta tsura masa ido, tana jin wani irin
aunar Yaron na ratsa zuciyarta, cikin wani irin murya ta ce, "My Maleek dukansu kyawawane da babu wanda ba za a sace a gudu da shi ba idan ana sata, but dis bouncing Boy
in is my Fav!"
Yadda ta yi maganar tana sake manna idanunta akan Babyn ya motsa zuciyar A.Maleek
in, ya ji wani irin tausayinta na ratsashi sabida ya san
arfin soyayyar da take masa da kamanninsa da Yaron ya yo ne yasa ta ce shi ne Fav
inta.

Ya rungumesu ita da yaron yana kai bakinsa bisa kunninta ya ce, "Suhailah in dai shi ne Fav
inki to ki fara shirin rainonsa bayan an yaye sa, ni Maleek na baki shi har abada!"
Daga Suhailah har TAIMIYYAH da ke saurarensu suka
ago a razane suka dubesa, kowacce zuciyarta na bugawa da
arfin gaske, A.Maleek bai kalli side
in TAIMIYYAH ba sam ya cigaba da kallon Suhailah ya ce, "Da gaske na ke yi Suhailah na baki Muhammad Sameer, a hannunki zai tashi da izinin Allah."
Suhailah sai ta sake rungume yaron tana sakin kuka mara sauti, wani irin abu ke kewaye jinin jikinta, ta dubi A.Maleek muryarta na rawa ta ce, "Thank u luv, but ita bata ce za ta bani ba, kar ka yi saurin yin kyauta da abinda ba kai ka
ai ka ke da hakki akansa ba."
Sai lokacin A.Maleek ya
ago ido ya dubi side
in da TAIMIYYAH ta ke, wacce ta tsura musu ido shi da matar tasa tana kallon ikon, zuciyarta na sake shiga tashin hankali da wani irin fargaba me tarin yawa.

'Me A.Maleek ke shirin yi ne haka?'
Ta tambayi zuciyarta tana ji hawaye na taruwa a idanunta, ganin ya fara takowa zuwa gareta ya sanya ta yi saurin sadda kanta
asa.

A.Maleek ya zauna daga bakin bed
in yana ri
o hannuwanta tare da
ago da face
inta,ya bu
e baki zai yi magana ta riga shi da fa
in, "Kar ka cemin komi Hubby!

Idan har abinda ka furta mata hakane har a cikin zuciyarka, ba sai ka yi magani da ni don Allah!"
TAIMIYYAH ta kai
arshen maganar tana zame jikinta ta kwanta, hawaye na zuba daga idanunta wani irin abu na cigaba da danne zuciyarta,hakan yasa A.Maleek tsura mata ido with so much shock!

Ya sake kai hannu zai ri
o nata ta yi saurin janyewa, murya can
asa ta ce, "Don Allah ku barni na samu hutu please!

Ka kwashesu A.Maleek tunda kana da ikon yin hakan sabida kai ne mahaifinsu, but now ina da bu
atar ku bar ni da huta please!"
Ta yi maganar tana juya masa baya tare da sakin kukan da take ri
ewa, Suhailah da ta zuba musu ido tana kallon komi sai ta taso tana nufo bakin bed
in ta tsaya.

Ta zubawa jaririn da ke hannunta ido
aunarsa da na A.Maleek na sake huda zuciyarta, cikin wani irin raunin murya ta ce, "Yah Maleek na gode da tarin karamci da nuna tausayinka gare ni, wanda shi ne jigon da yasa ka ke ganin za ka iya min irin wannan sadaukarwa, sai dai kash!

Ba zan ta
a goyan bayan raba uwa da
anta, ba tare da amincewarta ba, na ha
urah Yah Maleek kai ma ka ha
ura ka janye wannan maganar, ba za ta bani ba koma ta bayar za ta bayar ne bisa tirsasawarka gare ta, don haka na ha
ura Allah ya san dani kuma ban cire rai daga rahamarsa ba, Allah ya raya mana su cikin musulunci.

Zaynabb ki yi ha
ury ba zai rabaki
anki ya bani ba alhali baki yi na'am da hakan ba!"
Suhailah ta
are maganar tana sakin kukan tausayin kanta,hakan ya soki zuciyar Maleek tare da TAIMIYYAH wacce tun fara maganar Suhailah ta ji jikinta ya
auki rawa, wani irin tausayinta ya lullu
e zuciyarta.

"Na baki shi Suhailah, kamar yadda ya furta miki hakan ne zai kasance, abinda na ke so ku gane kawai ina bu
atar hutu ne a yanzu, ki yi ha
ury!"
TAIMIYYAH ta furta hakan cikin rawar murya, Suhailah ta lumshe idanunta tana wa A.Maleek sign da ido akan ya je ga TAIMIYYAH, ita kuma ta taka a hankali ta koma wajen gadon da aka kwantar da Baby gal
in, ta sanya Baby boy
in a cikin nasa gadon ta fice daga
akin, tana kasa fassara wani yanayi zuciyarta ke ciki.

"Zaynab ki yafe min idan abinda na yi ya
ata ranki, ban yi don in nuna isa ko
arfi iko ba sai don ina jin tsananin tausayin Suhailah, na san baki san issue
inta akan rashin haihuwa ba ko?"
TAIMIYYAH ta gya
a masa kai hawaye na cigaba da biyo face
inta, A.Maleek ya sanar da ita tun farkon matsalar da Suhailah ta samu har kawo yanzu, da suke jiran rabo ya samu a gare ta amma Allah bai kawo ba.

Ya
are maganar da cewa, "Shiyasa na ke tsananin jin tausayinta Zaynab, ki taimakeni in cika wannan promise
in a gareta, ba don na isa ba sai don ke ma ki nuna mata sadaukarwa, ko babu aure a tsakanina da ita wallahi zan iya sadaukar mata da abinda na haifa, domin mahaifiyarta ta nuna min so da gata Zaynab, kuma ta bar duniya ba tare da na cika burina akanta na nuna mata gata da kulawar da naci buri ba, so akan Suhailah ka
ai zan kyautata mata domin ita ka
ai ta bari a duniya, please TAIMIYYAH ki taimak......."
Hannun da TAIMIYYAH ta kai ta rufe bakinsa ya hana shi
arisa kalamansa,ta bu
e baki a hankali ta ce, "Ka daina ro
ona Hubby in dai yadda ta ka ke nema na amince, Allah ya raya su cikin aminci zan bata shi kamar yadda kasanar mata sai an yayesu za ka bata."
A.Maleek ya rumgume TAIMIYYAH yana gaya mata maganganu masu nauyi na nuna zallar
auna,tare da farin cikin yadda ta kasance me son duk wani abinda ya ke so, cike da nuna jarumta da
oye damuwar da ke zuciyarta ta cigaba da biye masa, har zuwa lokacin da Hajjah ta shigo ta korashi akan cewa ya barta ta huta.

Sai washegaryn ranar aka sallamesu daga asibiti zuwa gida,har lokacin kuma bata sake sanya Suhailah a idanunta ba, sai can dare ta shigo
akin ri
e da Baby Boy
in a hannunta, A.Maleek ri
e da macen sun dawo da su don a basu nono.

TAIMIYYAH ta
aga manyan idanunta ta sauke akan Suhailah, tausayinta na sake huda zuciyarta sosai, Suhailah ta aje Babyn a kusa da TAIMIYYAH tana cewa, "Zaynabb yana bu
atar nono in ji Hajjah."
TAIMIYYAH ta dubeta da murmushi akan fuskarta ta ce, "Okey! tuh."
Har Suhailah ta nufi
ofa don fita daga
akin TAIMIYYAH ta kira yi sunanta ta dawo, ta dubeta cikin ido ta ce, "Ki yi ha
ury Anty jiya na ga kamar baki fahimceni ba game da al
awarin da Hubby ya yi miki, ni da yaran duka ikonsa ne yana da damar ya sarrafamu yadda ya ke so, na amimce za mu mallaka miki Abbana ki raineshi a matsayin
an cikinki, ina fata za ki
aunacesa tamkar yadda ki ke
aunar mahaifinsa, ina miki addu'ar ke ma Allah ya kawo miki rabo me amfani."
TAIMIYYAH ta kai
arshen maganar tana jifan Suhailah da murmushi, Suhailah sai ta tako ta zauna daga bakin bed
in tana duban TAIMIYYAH cikin ido ta ce, "Zaynab da gaske za ki iya sadaukarmin da
anki na rainesa?"
TAIMIYYAH ta gya
a kai ta ce, "Me zai hana ?"
Suhailah sai fuskarta ya washe da wani irin wide smile, gaba
aya sai ta rasa kalar farin cikin da za ta nuna, ta
akko Yaron ta rungumeshi tana jin wani
aunarsa na sake huda jinin jikinta, ta sumbacesa ta
ago ta dubi TAIMIYYAH ta ce, "Na gode Zaynabb, na gode da wannan sadaukarwan ina ro
on Allah ya bani ikon bashi ingatacciyar tarbiyya, ha
a ke
in ba kishiya ba ce abokiyar zama ce.

Luv say something please!"
Ta kai
arshen maganar tana kallon A.Maleek da ke blushing, zuciyarsa cike da zallar
aunarsu da soyayyarsu me zafi, ya isa wajen TAIMIYYAH ya rungumeta ya ce, "Thank u Luv, Allah ya faranta ranki ya baki Aljanna Firdaus."
Daga haka ya sake ta ya koma wajen Suhailah ita ma ya rumgumeta ya ce, "Luv u Wife, ina fata Abban mu ba zai ture gwamnatina anan ba?"
Ya yi tambayar yana kai hannu bisa
irjin Suhailah daidai saitin zuciyarta,suka saki dariya a tare har TAIMIYYAH, kafin su tsaida dariyar Suhailah na cewa, "Ai ko da wuya bai ture ba sweety, na ji kuna ta cewa Abba an sa musu suna ne?"
Maleek ya jinjina kai ya ce, "An saka musu suna Muhammad Sameer da Nana Aysha,amma za mu kira ta da Nahar."
Suhailah ta jinjina kai ta ce, "Wow!

Nice names Sweet ka ce princess Hajjah mu ka samu."
A.Maleek ya jinjina kai ya ce "Yes!"
yar Suhailah ta iya barin
akin bayan TAIMIYYAH ta gama shayar da yaran tana kallo cike da birgewa,har cikin zuciyarta take jin kyawun zuciya irin na TAIMIYYAH, sai ta ji jikinta ya sake sanyi akan zazzafar kishin da ya
ebeta a baya har ta yi yin
urin binne layun da ta amso, ta dinga jin tarin nadama tana sake yin Istigfari akan Allah ya yafe mata.

Da dare A.Maleek suka ke
e da Hajjah ya sanar mata yadda suka yi da TAIMIYYAH,akan cewa idan Allah ya raya twins har aka ya ye su zai
auki Sameer da suka kira da 'Abbah ' ya baiwa Suhailah.

Hajjah ta yi farin ciki sosai tare da zuwa ta yi wa TAIMIYYAH godia me tarin yawa, sai lokacin Iyah ta ji maganar ita ma kuma ta yi na'am tare da jin da
in yadda TAIMIYYAH ta baiwa A.Maleek ha
in kai su yi wannan sadaukarwan.
Chapter 180 · 0% Book details