← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 184

Sashe 40

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matsanancin tsoro da fargaba ya hana ta duban idanunsa.Saima kuka da ta sakin masa da
aramin sauti,cikin muryan kukan take fa
"Yah Deeku please ka sakeni zan gaya maka koma me kake son ji please!"
are maganan tana kuka sosai,hakan yasa Sadeeq sake hannunta,yana zuba mata mayun idanunsa,yake fa
"Ina jinki Zaynab."
TAIMIYYAH ta sauke ajiyan zuciya,tare da sanar da shi komi.Tun daga randa Nass
in ya fara zuwa gidan,har kawo wayan da su ke yi da yadda Iyah ta matsa sai ta fita,duk bata
oye masa komi ba.Ta
are maganan da fa
in "Yah Deeku ni Allah ba ni ce na janyosa ba,kuma ina sauraransa ne sabida bana so Iyah tai fishi dani.Baba kuma yaga kaman na
i jin maganansa na cewa infito da wani,amma ni sam babu ma Soyayyah a lissafina, sai karatu kaima kasani ai,amma kayi ha
ury in ranka ya
aci please!"
Yadda take bashi ha
ury tana kuka ne ya sake karya zuciyan Sadeeq.Wani irin soyayyanta ya motsa masa wanda har ya kasa controlling kansa,ya janyota jikinsa baki
aya ya rungumeta.Abinda ya tsaida bugun zuciyan TAIMIYYAH cak!

Jikinta ya
auki wani irin rawa,kafin ta fashe masa da kuka lokacin da take jin kansa bisa kafa
unta.Yana sauke wani irin numfashi kaman wanda yayi gudu,gaba
aya qamshin turarensa ya gama cika kafofin hancinta.Cikin muryan kuka take fa
in "Yah Sadeeq don Allah ka sakeni,kasan dai haramun ne hakan da kayi ko?

Pleas......" Maganan TAIMIYYAH ya ma
aleni ne lokacin da Sadeeq ya sake shigar da ita jikinsa sosai,yana
arin ha
e bakinsu waje
aya.Gaba
aya hu
uban da she
an ke masa ne ke aiki,don burinsa bai wuce yayi duk abinda zai bashi relief ba.Sai dai kukan da TAIMIYYAH ta saki me tsananin
arfi ne yasa shi janye fuskansa daga gareta,yana maida kansa ya kwantar bisa kafa
unta,dukkaninsu jikinsu rawa yakeyi bama kaman TAIMIYYAH, da ke ji numfashinta na yin sama.

Cikin wani irin murya Sadeeq yake fa
in "Zaynab bansan ta yadda zan sanar dake nakasa cire soyayyanki daga cikin zuciyata ba.Bansan cewa duk iya
arin da nake na danne feeling
ina akanki shirme nakeyi ba,sai yau da dana ganki da wani namiji bani ba.Please!

Zaynab mu ture duk wani
iyayyan da Umma ke miki,ki amince in samu Baba Sani in gaya masa muna son junanmu.Nayi miki alqawarin kare ki daga duk wani cutarwa ko tsangwama.Domin bazamu zauna anan ba bare har Umma ta ganki tai miki abinda ranki zai
aci,please Zaynab ki amince dani bazan iya kallo wani namiji ya aureki alhali ni zuciyata na azabtuwa da soyayyarki."
Sadeeq yayi maganan har lokacin TAIMIYYAH na jikinsa,yai mata wani irin runguma da ta kasa kwacewa.Kuka kawai takeyi me tsuma zuciya,amma Yah Deekun da alamu sam hakan baya damunsa.Cikin kuka take fa
in "Ka sakeni tuh sai muyi magana Yah Sadeeq please!"
Bai yi musu ba ya saketa tai baya tana zamewa ta sauka daga kujeran.Kaman yasan shirin da takeyi na son ta gudu,sai yayi saurin ri
o hannunta yana tsareta da rinannun idanunsa.TAIMIYYAH tayi saurin fa
in "Yah Sadeeq don girman Allah ka barni in tafi lokaci na tafiya,zamuyi magana gobe nayi maka alqawari." TAIMIYYAH tayi maganan cike da magiya,dukkanin jikinta rawa yake burinta bai wuce ta ganta a Sasan Iyah ba.

Kafin Sadeeq
in yace wani abu aka bu
ofan shigowa falon nasa ha
e da yin sallama.Muryan Zuhurah ce ta shigo kanta tsaye tana sauke idanunta akan su TAIMIYYAH.Ta wani waro ido tsananin mamaki na cika zuciyanta,tuni TAIMIYYAH taji maranta yai wani irin
ullewa,tana jin lokacin da fitsari ya zuba cikin pant
inta.Tsabagen yadda ta ru
e da ganin irin kallon da Zuhurah ke jifanta dashi.Da
arfin gaske ta kwace hannunta daga nasa hawaye masu tsananin zafi na sake
alle mata.Dukkanin jikinta babu inda baya rawa sabida tashin hankali,shiko Sadeeq rinannun idanunsa ya
ago ya sauke akan Zuhurah dake tsaye daga bakin
ofan,ta zubo musu ido.

Yayi magana cikin
acin rai yana fa
in "Uban me kika zo yi,da zaki shigo min
aki ba tare da an baki iziniba,sabida ke da
iyace ko?" Ya
are maganan da dakawa Zuhurah tsawan daya sake ru
a TAIMIYYAH ta sanya masa kuka.Zuhurah ko ta wani kya
e fuska tana fa
in "To ai Umma ce tace inzo in kira mata kai,don ta kira wayanka har sau uku baka
aga ba."
"Get out!

Stupid kawai,idan kinje kuma ki gaya mata cewa kinga wani abu,kiga idan ban
alaki ba!" Yah Sadeeq
in yayi magana a fusace idanunsa akan Zuhurah data juya da sassarfa tana barin
akin.TAIMIYYAH da gaba
aya ta rasa inda zata sanya kanta,itama sai mi
ewa tayi tana saurin dafa
afatan zata fara tafiya,amma sai Yah Deekun yayi saurin isowa wajenta yana kama hannunta.Ta
ago manyan idanunta da hawaye suka kasa daina zuba,cikin muryan kuka take fa
in "Kaga abin da ka janyo min ko Yah Deeku?

Yanzu Allah ne ka
ai yasan abinda zata je ta gayawa Umma,shikenan na shiga uk....." Hannun da Sadeeq yakai bakinta yana fa
in "Shihhshhhh..!" Shiya katse TAIMIYYAH daga
arisa maganan data faro,cikin low voice yake fa
in "Babu abinda zai faru Zaynab calm down please!

Muje in rakaki,amma ki sani duk abinda na fa
i da gaske nake yi.Bazan iya ha
ura da soyayyarki ba Zaynab,don haka ki fara koyawa zuciyanki yadda za ta so ni,ki kuma dakatar da wancan gayen bana son in sake ganin ku tare."
Yadda ya
are maganan cikin wani irin murya,ya tabbatarwa da TAIMIYYAH cewa duk abinda yake fa
i da gaske yake yi,sam babu alamun wasa ko ka
an.Ita dai TAIMIYYAH burinta kawai ta ganta a Sasan Iyah shine kawai samun nutsuwanta,don haka sai kawai ta gya
a masa kai ba tare da tayi magana ba.

Hannunta cikin nasa suka fito daga
akin nasa,kobi ta kan Tray
in lemu da ruwan TAIMIYYAH bata yi ba,bare har ta tuna da wani ku
in da Nass
in ya bata.Sai da Sadeeq ya ga shigan TAIMIYYAH cikin Sasan Iyah,sannan ya juya yana nufan hanyan Sasan su,don amsa kiran Ummansa.

TAIMIYYAH dake tafiya cikin wani irin slow motion,gaba
aya jikinta a sanyaye yake.Zuciyanta na tsananin bugawa da tsoron abinda zai je ya dawo,don tasan tabbas sai Zuhurah ta sanar da Umma cewa ta ganta a wajen Sadeeq.Ba kuma zata rage komi akan yadda idanuwanta ya gane mata su sar
e da hannun juna ba,har ta shiga cikin falon Iyah bakinta
auke da sallama,zuciyanta babu nutsuwa sam.Da idanun Guggo Bilki ta fara cin karo lokacin data sanya kai cikin falon,sai tayi saurin yin
asa da kanta tana takowa cikin falon.Tana shirin gota su ta wuce muryan Iyah dake zaune tare da Guggo Bilkin ya shiga kunnuwan TAIMIYYAH ,Iyah na fa
in "Sai yanzu ne ya tafi Naseerun?" TAIMIYYAH bata jiyo ba ta gya
a kai kawai tana yin gaba,domin bata son yin magana bare Iyah ta gano akwai matsala.Daga Iyah har Guggo Bilki suka bi bayan TAIMIYYAH da kallo,Iyah na fa
in "Anya lafiya Bilki,naga duk tayi wani sanyi ne gashi ta jima bata shigo ba." Guggo Bilki ta dubi Iyah tana fa
in "Lafiya lau Iyah,ai kinsan dama bata so fitanba,watakila da
ewan da yayin ne ya bata haushi."
Iyah sai ta saki rai tana fa
in "Hakane fa kuma,to shine kuma tabar min faranti a waje sabida ta
ara,to ai sai ki kira Yasmeen ta je ta
akko min."
TAIMIYYAH kuwa tana shiga
aki toilet ta nufa direct.Yasmeen dake kwance akan gado tana kallo a System
in TAIMIYYAH,sai tabi bayan TAIMIYYAN da kallo kawai.

Lokacin da TAIMIYYAH ta fito kan gadon ta nufa tana aje Hijab
in data cire shi tun a toilet.Tayi kwance kawai tana lumshe idanunta ba tare data kula Yasmeen dake ta faman binta da kallo ba,ganin haka yasa Yasmen danna pause tana ture System
in gefe
aya.Ta matsa kusa da TAIMIYYAH da tayi rub da ciki tana fa
in "TAIMIYYAH lafiya,meyafaru?"
TAIMIYYAH kaman jira take Yasmeen tayi magana sai kawai ta saki kuka,tana gayawa Yasmeen
in abinda duk ya faru a part
in Yah Sadeeq.Sai dai ta
oye mata cewa ya rungumeta,ta ta
are maganan da cewa "Yasmeen bansan da wani fassara Zuhurah zatai min ba,ban kuma san iya abinda zata gayawa Umma ba.Sannan bansan me zan cewa Iyah ba idan ta tambayeni yadda akayi har na biye masa naje
akinsa,ni dai Yah Sadeeq na son jefani cikin masifa Yasmeen."
TAIMIYYAH ta
are maganan tana sake sakin kuka sosai.Hakan yasa Yasmeen fara lallashinta tana kwantar mata da hankali,akan cewa babu abinda zai faru ai Zuhuran na tsoran Yah Deekun bazata sanar da Umma komi ba.Da wannan lallashin na Yasmeen TAIMIYYAH ta
an kwantar da hankalinta,amma har suka kwanta bacci ta rasa wani irin tunani zatayi akan zancen Yah Sadeeq.Na cewa ta rabu da Nass
in,ita dai tasan ko sama da
asa zasu ha
e ba zata iya auren Yah Deekun ba,sannan kuma bata san ta yadda zata iya koran Nass wanda a yanzu ta fara jin zuciyanta na nutsawa dashi.......

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAuxFVUMsQhHYfF5qiGklY
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu bu
atan yin payment zakui min magana ta wannan number
in 08167768704, ko kuma ku turo ku
in ku kai tsaye ta wannan account
in 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line
in 08167768704.*
ansabo ce#
[12/14, 3:42 PM] +234 703 040 9541: *Page 29*
*Friday, 8:49pm.*
Suhailah ce ke ta faman kai-kawo a cikin falonta da ke
upstairs,tana jiran isowan Maleek Ado, wanda ya shaida mata goslow ne ya ri
e su a Kaduna tun
azu.

Sanye take cikin wata english straight gown,da ya amshi jikinta sosai tare da fiddo suranta.Make-up sosai tayi wa fuskanta wanda hakan ne ya sake qawata kwalliyan,ta sanya manyan
an kunni da sukai mata kyau matu
a,qamshin Turarukan ta masu asalin sanyi da da
i ke fita daga jikinta.
Chapter 40 · 0% Book details