← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 184

Sashe 178

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Baba Sani ya shigo motar sai ya ajewa Ummie ledar Yalon akan cinyarta yana cewa, "Gashi wife." Ummie ta dafe ledar tana dubansa cikin ido ta ce, "Thank u Baby, i luv u."
Baba Sani ya jinjina kai ya ce, "Luv u too wife."
Umma ta ji wani kuka me
arfi ya taho mata amma sai ta yi gaggawar dafe bakinta, tana jin wani abu me nauyi na sake danne zuciyarta, 'Wai ita ce yau ake gwadawa wannan bu
ewar idon babu kunya bare tsoran Allah?'
Ta ayyana hakan a cikin zuciyarta tana jin
irjinta na mata wani irin zafi, kanta ya cigaba da sarawa tana jin lallai suna isa gida sai ta danna maganin hawan jininta, don yadda kanta ke juyawar nan da wuya ta samu bacci a daren yau.

Suna isa gida Ummie part
in Iyah ta wuce, shi kuma Baba Sani suka wuce part
in Umma, yana son ya watsa ruwa kafin ya fito zuwa part
in Iyah su gaisa.

Daga can asibitin kuwa Sharifah ce ta kira wayar Basmah don ta gaida ta da jiki, sai Zuhurah ta
auki wayar ta shiga danna mata zagi bayan ta saka wayar a speeker, memakon Sharifah ta kashe wayar ko ta ji haushi sai ta saki dariya tana cewa, "Easy Yah Zuhurah miye abin zagi da cin mutunci don zan auri mijin
anwarki?

Bafa ni na janyosa zuwa gare ni ba shi ya kawo kansa, ni kuma na ga ya yi min zan iya aurensa to sai me, haramun ne ko kuwa akaina aka fara cin amana?

Ina ce ita ma anamar gurguwar gidanku kuka ci ta auresa bayan kun nemesa da asiri kun samu kansa, ni kuwa babu Boka ba Malam soyayyace min indillahi ya ke min ina masa, to kuma sai me don zamu auri juna?

Don haka kar ki
ara zagina da kirana maciyiya amana,ina Basmar ta ke?"
Zuhurah ta saki wata uwar ashar lokacin da Basmah ta fisge wayar tana kuka ta ce, "Sharifah ni za ki ci amana har kina kiran hakan ba a bakin komi ba?

Meyasa sai Nass za ki aura bayan ga mazanan da suka fi shi komai?

Meyasa sai mijin ni aminiyarki ki ka ga ya dace ki aura don ki sanya min ciwon zuciya,bayan kin gama sanin sirrina, meyasa hakan Sharifah?

Me nayi miki dana cancanci wannan sakayyar ta cin amana daga gareki?"
Basmah ta kai
arshen tambayoyin tana kai
aya hannunta ta dafe sautin zuciyarta,wanda ke bazanar rabewa gida biyu.

Sharifah ta ja numfashi tausayin Basmah na son danne ta amma ta yakicesa tana cewa, "Basmah ha
ury za ki yi don tsakani da Allah tun randa ki ka fara nuna min hoton Nass zuciyata ta kamu da
aunarsa, shiyasa lokacin da ya taya ni kuma ban tsaya sanya ba wajen bashi zuciyata, ina miki bushara da cewa zamu zauna lafiya ba zan ta
a cutar da ke ba, hasalima ba za mu rayu inuwa
aya ba Basmah , ki yi ha
uri ni da ke
addararmu kenan bye!"
Daga haka Sharifah ta kashe wayarta ta bar Basmah da rushewa da wani irin kuka tana shure-shure tamkar za ta zare, sai da Zuhurah ta kira Doctor ya zo ya danna mata allurar bacci sannan suka samu sukuni.

Washegary
arfe sha
aya na safe aka
aura auren Nass da Sharifah akan sadaki naira dubu
ari, aka zarce da shagalin biki har zuwa lokacin da aka
akko Amarya Sharifa, aka kai ta Fam house
in su Nass
in da ke
warbai cikin City.

Hajiya Hajara da aminanta an sha shagali, don murna ta ke da wannan auren sosai da sosai, shiyasa ta zage wajen ganin an tarbi amaren yadda ya dace, sai zuwa next week Ango zai wuce da Amaryarsa Abuja, in da ya kama haya a Jabi nan zasu zauna sai dai ya dinga shigowa Basmah weekend Zaria.

Basmah ba don a
ashin kulawar likitoci ta ke ba da Allah ka
ai ya san irin mummunar yanayin da zata shiga, don kuwa hauka kawai ne bata yi ba lokacin da ta tabbatar cewa an
aura auren, Sharifa yanzu ita ce za ta amsa sunan kishiyarta.

Hatta Zuhurah sai da ta taya Basmah kokawa tana jin tausayin junansu na ratsa zuciyarta, da
yar aka samu Basmah ta dangana bayan an sanyata yin baccin dole don samun hutun
walwarta, cikin jikinta kansa ba don Allah shi ne me iko akan komi ba, kuma bai
addari fitarsa ba tabbas da tuni ya da
e da zubewa.
_____________
*Abuja.*
TAIMIYYAH da ke da watanni uku a garin Abuja, zuwa lokacin ta jima da sabawa da garin tana kuma jin da
insa matu
a, hannunta ya jima da fara nuna a iya driving don kusan yanzu da kanta ta ke fita duk in da to, duk da cewa har lokacin ba a cire Laner daga jikin motar ba.

Ta kammala yin duk wasu jarabawa da za su kaita matakin shiga Jami'a, kuma ta samu nasarar tsallakewa yanzu zaman jiran addimision later kawai su ke yi ta fara Registration.

Cikin jikinta da ita kanta suna cikin
oshin lafiya da samun cikakkiyar kulawa daga A.Maleek Ado, wanda duk ran duniya sake ninka kulawarsa akansu da nuna musu
auna ta zahiri da ba
ini ya ke yi.

TAIMIYYAH ta sake cika ta yi wani irin kyau me fisgar hankali,duk weekend A.Maleek na kan hanyar zuwa dubasu, su sha soyayyarsu monday ya bi flight ya juya, haka rayuwar ta dinga garawa har kawo yau ya da ya kama Friday.

Tun safe ta kintsa
akin baccinsa tare da bu
esa da turarukan wuta masu
amshi na Northern Regalia, ta gyara ko'ina fes tana jin wani shau
i da
okin son ganinsa tamkar sunyi watanni ba su ga juna ba.

Ita ta taimakawa Rabecca suka gama shirya abincin Lunch don bata iya zama bata aikin komi, tun A.Maleek
in na masifa har ya gaji ya daina ya gane cewa haka nature
inta ya ke, kuma tana da
oshin lafiya ne don haka Hajjah ta sanar masa lokacin da ya kai
arar TAIMIYYAH wajenta.

Shiyasa ya ha
ura ya barta tana yin
ananun ayyukar da ba za su jigatar da ita ba, sun kammala shirya dining
in da ke upstairs
in ne ta wuce
akinta don yin wanka da sallah.

Tana cikin shiryawa A.Maleek
in ya iso, shi ya
arisa shafa mata mai da sanya mata kayan da ta ciro riga da wando na shan iska marasa nauyi, kalar pich and black masu laushin jiki.

Wuyar rigar me fa
i ne da ya fito da dukiyar fulaninfa a fili, ta yi kyau matu
a cikin kayan, A.Maleek ya kai bakinsa ya sumbaci wajen yana wani lumshe idanunsa, tare da sake rungumota zuwa jikinsa.

TAIMIYYAH ta sake shigewa jikinsa tana lalubar bakinsa ta ha
e da nata, a hankali take aiki masa da deep kisses da suka fara birkita lissafinsa.
yar ta kwaci kanta tana magiyar ya tashi ya yi wanka ta bashi abinci , ya dinga aika mata harara bayan ya ra
a mata wasu kalamai masu nauyi a kunni.

Bayan ya fito daga wankar ne ta taimaka mai ya shirya sannan suka fito zuwa dining, ita ce ta ciyar da shi abincin kafin shi ma ya ciyar da ita da kansa.

Bayan sun kammala me ya
auke ta cak!

Zuwa bedroom
insa, ban sake jin
uriyarsu ba sai can yamma da suka tashi don yin sallar la'asar.

Kwanaki biyun da ya yi na weekend
in kullum sai sun fita wajen hutawa abin su, sai yamma li
is suke shigowa gida duk a waje suke yin Lunch sai dinner ne kawai TAIMIYYAH ke dafa musu abu mara nauyi su ci su kwanta.

Monday ya juya zuwa Lagos ya barta da tarin kewarsa, don ma yanzu business
in da suka fara na sake
auke hankalinta da rage mata kewa, sabida sun fara abin a sa'a daga shigo da Abayun nan su Yah Anas suka tallatawa
an kasuwa, take wani me shagon sayar dasu ya sare duka guda 150
in.

Yasmeen kanta sai wajensa ta je ta darza wanda za a zuba a lefenta, sabida ita ke ha
a kayan auren da kanta wanda bikin ya rage saura 4weeks wata biyu kacal aka saka, za ta auri Aliyunta
an nan Kano ne amma haifaffen Yola ne, yana aiki a Nasarawa can za a kaita.

Kamar da wasa sai TAIMIYYAH ta sake ordern wasu har ma da Hijabai da gyaluluwa, su ma bugun farko suna isowa duk aka sare su daga haka sai abu ya fara yin gaba,ita ma Suhailah abin ya amsheta don yawan nata ma sun zarce na TAIMIYYAH, don ita ta yi renting shago ne a Ikoyi ta zuba kayan, tun daga kan Abayas da takalma zuwa jakuna, duk tana order daga Dubai da Egypt duka, tana kuma sararwa
an kasuwa akan farashi me sau
i.

Nan da nan sai suka ji son yin business
in na sake bun
asa a ransu, shi kuma A.Maleek sai ya
ara musu jari don yana jin da
in yadda abin ya amshe su shi ma, kuma bashi da burin barin su suyi aiki sai dai business
in dama.

Sai ya zamana Subailah yanzu duk wani kishi da wauta ta aje sa a gefe ta kama mijinta da business
inta hannu biyu, sai yanzu da ta fara business
in ga kuma mijin a kusa da ita,sai take gane cewa tabbas shawarwarin Meenah da Anty Safiya sune masu inganci, don gashi yanzu hankalinta ya fi karka akan nawa za su shigo nawa kuma ta fitar, ba tunani kishiya da son sanin wani hali take ciki ba.

Cikin TAIMIYYAH na da 5month ta fara
aukar lacture a Jami'ar Baze, ta fara karantar Law cikin
oki tare da
inbin maida hankali, musamman da ya kasance tana cikin wanda Ubangiji ya yi wa baiwar kwanya, tana sahun gifted da aka fara ji da ita a faculty
in tun a semestern farko.

Ita ke driving kanta zuwa skull
in ta kuma dawo gida cikin kwanciyar hankali, sosai ta ke jin da
in course
in tare da shan
ammaran fitowa da first class idan Allah ya bata nasara.

Dukkanin dokokin A.Maleek
in daya kafa mata akan sanya dogayen Hijabai duk ta
auka, ta kuma kiyaye domin a zauna lafiya.
Chapter 178 · 0% Book details