← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 184

Sashe 121

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka isa Gonar Ganye gidan Hajjah zuciyarta ba ta huta ba,suna isa ana kiran sallar la'asar a masallacin da ke
asan gidan Hajjah.

Suhailah da
yar ta iya sanyo
afarta waje ta fito daga cikin motar,tana ji tamkar
afafun ba za su iya
aukar nauyin gangar jikinta ba, sabida yadda su kai wani mugun sanyi.

A haka ta dinga tafiya cikin slow tana biye da bayan su Anty Rady zuwa cikin gidan Hajjah.

Babu wasu mutane sosai sabida ita ba yau take nata taron ba,sai gobe ne za ta tara mutane ayi walima tunda a gidanta za a sauke Amarya ta kwana,sai bayan an tara mutane anyi walima ne sai a wuce da Amarya zuwa GRA
akinta.
_____________
Daga can Gyallesu kuwa gidan su Amarya TAIMIYYAH,bayan an idar da la'asar ne me make-up ta sake gyare fuskar Amarya TAIMIYYAH.

Wacce ta sake sauya shiga a karo na uku cikin wani ha
en lace mara nauyi, kalar red and black da ya yi masifar amsar jikinta.

Bayan an kafa mata hular
ankwalin lace
in kamar yadda ake yi a yanzu,sai aka yane jikinta da wani irin ha
en mayafi tamkar na
in da akewa sari.TAIMIYYAH ta yi kyau har ta gaji su Yasmeen sai kashe mata hotuna suke yi,suna yana yaba kyawun da ta yi cikin kayan.

Anty Laurat ce kawai ba za ta samu yi mata rakiya ba sabida da ita aka tafi kai Zuhurah Bauchi,sai su Zee da su Maryam Sunusi ne kawai za su yiwa TAIMIYYAH rakiya zuwa gidan Hajjah.

Dukkaninsu sun sauya shiga cikin kaya na alfarma sun sha make-up na kece raini.

Shigowar Ummie cikin
akin yasa TAIMIYYAH
aga ido ta dubi Ummien,wacce ta cake ita ma cikin rantsatstsen lace da ya yi mata mugun kyau,sai ta koma tamkar budurwa irin
ar 25 yrs
innan.

"To Amarya sai ki ta so ga motoci can sun iso,za a mi
a ki zuwa gidan miji."
Ummie ta yi maganar idanunta akan TAIMIYYAH da ta yi wa Ummien mugun kyau kamar ta yi ta kallonta.

TAIMIYYAH nan da nan sai hankalinta ya tashi ta yi wani
wal-
wal da ido tana shirin sanya kuka,hakan yasa Ummie saurin fice wa daga
akin tana sanar da Yasmeen cewa su fito tare da TAIMIYYAH, ga su Guggo Lami can da su Anty Mardiyyah na jiran su a falo.

Daga haka ta yi ficewarta don zuwa ta
akko mayafi don da ita za a kai TAIMIYYAH,bata son tsayawa TAIMIYYAH ta karya zuciyarta ne don ita me saurin kuka ce ,babu wuya zuciyarta ta raurawa ta fara kuka.

TAIMIYYAH lokacin da suka fito zuwa falon Ummie,sun samu duk su Anty Mardy suna jiran fitowarsu ne, don a wuce da ita zuwa part
in Iyah su yi sallama da juna.

Wani irin
aramin film ne ya gudana a part
in Iyah,na yadda rabuwarta da TAIMIYYAH zai kasance, wacce ta
ame Iyah tana kuka tamkar za ta shi
e,tana kuka Iyah na kuka kuma cikin kukan Iyah ke faman rattafo ma TAIMIYYAH addu'o'in sanya albarka.Duk wanda ke
akin sai da ya taya su kuka,sannan kuma ya dara sabida yadda suke kuka tsakanin junansu,da
yar aka zare TAIMIYYAH daga jikin Iyah aka fita da ita.Yasmeen kanta tana kuka ne tana yin musu vedio don ba
aramin tausayin TAIMIYYAH ta ji ba,sabida kowa ya san yadda suke da Iyah zai san cewa rabuwarsu ba zai zo ta sau
i ba dama.

Lokacin da aka fito da TAIMIYYAH ita kuma Basmah za a shiga da ita don sake yin sallama da Iyah ita ma,sabida kusan duk a tare motocin
aukar Amaren suka hallara.

Ita Basmah can
warbai gidan Hajiyar Nass za a fara kaita ita ma ,sai a gobe za a
akko ta daga can a kai ta Gonar Ganye gidan Nass
in da ya gina.

Daga yanayin manyan motocin da ke fake a harabar gidan za ka san cewa akwai ratar arzi
i tsakanin motocin da za su
auki TAIMIYYAH da wanda za a
auki su Basmah.
awayen Basmah irin su Sharifa duk sai suka raina arzi
in Nass
in,sabida motocin sun ru
e su don kana kallo kasan bana
ananun masu ku
i bane,ko wace mota ka kallah za ka ganta sabuwa dal ce.

Kallo bai koma sama ba ma sai da motar da za ta
auki Amarya TAIMIYYAH ta
ariso cikin compound
in gidan.

Amintaccen driver
in Maleek Ado me suna Yusuf ke janye da motar.

Wata iriyar mota da kaf su Sharifa ba su ta
a cin karo da motar da ta
auki hankalinsu irin ta ba,motar ba wani girma ne da ita ba amma kallo
aya za ka mata ka san bana
ananun ku
i bace,sabuwa ce dal don ranar aka fara hawanta.

Maleek ne ya yi ordern su guda biyu tun daga
asar Amurka aka zo masa da su,domin ya mallakawa matan nasa su kyauta halak malak,shiyasa ya yanke shawaran a
akko masa Amaryarsa TAIMIYYAH a cikin nata.

Surutu ya dinga tashi ana zuzuta irin gidan daular da za a kai gurguwa TAIMIYYAH,kamar yadda su Sharifa suka dinga fa
in kalmar suna cewa "Kai!

Yanzu gurguwace ta auri attajirin mutum irin haka?"
Suka dinga mamaki suna jinjina lamarin a tsakaninsu kai kace ita gurguwar ba mutum bace,da Ubangiji ba zai azurta ta kamar yadda ya ke azurta sauran bayinsa ba.

Ita dai TAIMIYYAH bata ma san ana yi ba don kukanta kawai ta ke sha,ko kalar motar aka tsareta ma ta fa
i ba za ta iya ba don ba abinda ke gabanta kenan ba.

Haka Yusuf ya ja motar suka fice daga cikin compound
in gidan,Yasmeen da ke daga gefen TAIMIYYAH ri
e da hannunta na faman rarrashi,ita ma Anty Mardiyyah da Ummie da suke ta
aya gefen na taya Yasmeen rarrashin.

Guggo Lami da ke matsayin
anwar su Baba Sani ita ta kame a front seat su Zee da su Maryam Sunusi suna can cikin
aya motar Maleek, wacce ya zo da ita gidan
azu.

A ciki aka kwashesu su hu
u daga Maryam sai Zee da Bushira,sai Nusaiba cousine Sis
in su TAIMIYYAH.

Sauran motocin suka kwashe ragowar mutanen da za su yi wa TAIMIYYAH rakiya,wasu ma empty suka juya sabida ba da yawa aka je ba,tunda an rabu uku za a ce wasu za su raka Basmah ne, wasu kuma TAIMIYYAH, yayin da sauran kason ke can Bauchi wajen raka Amarya Zuhurah.
__________
*Gonar Ganye.*
Hajjah ta dubi Suhailah da tsananin mamaki da firgicin abinda ta ke ji da gani,wanda ya girmi tunaninta bayan su Anty Safiyyah sun gama zayyane mata komi.

Ta
aga idanunta a karo na biyu ta sauke akan Layun da ke kan gadonta, tana cigaba da shiga mamakin yadda wai Suhailah ce ta iya amso su, don ta tarwatsa auren da take farin ciki da
ulluwarsa a wannan rana.

Zuciyarta ya sake matsewa da wani irin
unci me tsanani, ta maida dubanta kan su Inna Dije da suke faman yiwa Suhailah fa
a da nasiha.

Hajjah ta yi magana cikin sanyin murya ta ce, "Yayah ina ga a barta haka nan, a kulle wannan babin don yanzu za ki ji
an kawo Amarya sun iso.

Safiyyah ki
auki Layun ki je can backyard ta inda babu me sanin me za ki yi,ki
onasu gaba
aya.

Ita kuma Suhailah zan dawo ta kanta amma ba yau ba, ba kuma gobe ba sai an watse wannan taron,sabida yanzu lokaci ne na tsayawa mu amshi ba
in mu bana
atawa akan Suhailah ba."
Daga haka Hajjah ta juya ta bar musu
akin,tana jiyo kukan da Suhailah ta saki zuciyarta na sake
aukar zafi da ita.

Inna Dije ta dubi Suhailah tana me kai hannu ta bige bakin kukan, cikin zallar fushi da
acin rai ta ce, "Za ki mana shiru ko sai na
auke ki da mari,
ar banzar Yarinya mare jin magana.

Duk irin Nasihar da aka dinga miki ashe ta bayan kunninki suke bi suna fita.

Kin bani kunya Suhailah sannan kin ci amanar
auna da tarbiyar da Hajjah ta baki,don baki taso kin ga tana aikata mummunar abu irin wannan ba,kada ki bari
awayen bariki su kai ki su baro Suhailah.

Tun wuri ki dawo cikin hankalinki ki kama mijinki tare da rungumar
addararki da hannu biyu,kishi ba hauka bane Suhailah don dukkkanmu ni da Radiya gata nan duk kishiyoyin gare mu,amma kin ta
a ji ko ganin ance ga mu a hanyar amso asiri don mu cutar da su?"
Suhailah ta girgiza kai hawayen tsananin nadama na sake biyo fuskarta,Inna Dije ta cigaba da cewa, "To ki shiga hankalinki tun wuri, duk wata
awa da ba za ta saki a hanyar bin Allah ba ki yi gaggawar rabuwa da ita,don ba mai
aunar ki bace.

In da ace kina dagewa da addu'a tare da ro
on Allah akan ya rage miki wannan zafin kishin,da tuni kin samu nutsuwar zuciyarki.

Maleek na
aunarki Suhailah don haka ki yi anfani da damarki wajen kwantar da hankalinki,tun yana bibiyarki yana rarrashi kafin ki kai shi bango ya tattaraki ke da mummunar kishin banzar ki ya watsar a gefe guda.Don yanzu sabuwar Amarya ya yi idan kika cigaba da wannan sokoncin da iskancin da ki ke yi ,wallahi tun kina bashi tausayi yana rarrashinki kina botsarewa, tuh fa zai fita daga sabgarki ne ya rungumi Amaryarsa da za ta faranta ransa, don haka ki dawo cikin hankalinki ki aje duk wani zafin kishi.

Ki rumgumi mijinki tare da tarairayarsa, ki bashi goyan baya wajen tabbatar da adalci a tsakaninku.

Duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki ki dinga yawan nanata wannan addu'ar ' _Allahummah Atinifuh sanahtaqwaha_ wazakkiha Antah Khairumanzakkahah_ Anta waliyyuha_ wamaulahah!_ ' sannan ki dinga yawan fa
in ' _Allahummah lah sahlan_illahmaja'altuhu sahlan_wa'antah taj'alul haznah_ izahshi'itah sahlan!'_
Idan har ki ka dagewa fa
in wa
annan addu'o'in a duk lokacin da ki ka ji kishin ya taso miki,tuh ina tabbatar miki da cewa Ubangiji zai sanyaya zuciyarki.

Amma bin Boka ko kauce hanya babu in da zai jefa rayuwarki sai a halaka da danasani marar iyaka.

Ga
inbin zunubin da zai iya kai ki wuta,kuma ki daumama a cikinta idan har kika mutu kina shirka baki tuba ba, to ina riba Suhailah?
Chapter 121 · 0% Book details