← Book details Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 184

Sashe 16

Taimiyyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

rabo,murna a wajen Iya da ita kanta Zainab in ba'a magana,hatta da uban gayyan Alhaji Sameer wanda zuwa lokacin yaje Hajji,murnan ba'a magana,sai dai murnan nasu ya katsene a wani dare da Allah ya auki rayuwan Alhaji Amadu mahaifin su Sameer in,wanda yai mutuwan farat aya domin sun kwanta da Iya lafiya-lafiya,cikin dare ciwan kai na ajali ya samesa kafin gari ya waye yace ga garinku nan,mutuwa ne da ya jijjiga duka Familyn sa,tare da gigita iyalansa domin Iya sai da akai uku ta fara gane kanta,hatta da TAIMIYYAH mutuwan surukin nasu ya ta a ta matu a,haka aka share zaman makoki har kowa ya watse,aka bar Iya da takaba wacce cikin anin lokaci duk ta fita hayyacinta,amma cikin hukuncin Allah tana addu'a kuma ana bata rubutun dangana tana sha,har ta kwantar da hankalinta zuwa lokacin fitanta takaba,ta gama sarewa da kuma sadaukar da cewa Amadun ya tafi inda babu dawowa kuma dole rayuwa tacigaba,don haka sai ta sake mi a wuya ta cigaba da yi masa addu'a,Alhaji Amadun na da watanni shida da rasuwa,Zuwaira ta haifo ar ta Zuhrah yayinda Zainab ita a lokacin cikinta ya shiga watanni shida,amma girmansa kai kace yakai watanni takwas,Zuhrah na da watanni hu u har ta fara koyan zama,wata ranan Juma'a Allah ya sauki Zainab ta haifo ar ta mace atuwan gaske,kyakykywan jinjiran da ta tafi da zuciyoyin mutane da yawa,ciki har da Iya wacce tunda ta auki yarinyan taji wani irin aunarta me zafi yana bin jininta,a ranan ne kuma Alahji Sameer ya dawo Weekend ya riski wannan farin cikin na samun aruwa,lokacin da ya aura ido akan yarinyan sai yaji wani irin soyayyanta na ratsa ilahirin jinin jikinsa,babu inda ta b aro kamannin uwar ta sai manyan idanun ne kawai irin na Sameer in,wanda suma suka gado wajen Iya,sai dai abin tausayi tunda Zainab ta haihu sai kuma ciwo sam babu lafiya,aka kwasa aka nufi asibiti da ita nan take aka basu gado,domin tana kuka da ciwan kai me tsananin gaske,wanda ake tunanin ko hawan jini ne ya sameta,amma bayan gwaje-gwaje aka gano babu wani hawan jini a tare da ita,kwananta biyar a asibitin Allah ya auki a barsa,wani irin mutuwa da ya gigita ahalin Alhaji Amadu baki aya,har fiye da yadda suka ji mutuwansa,Iya tayi wani irin gigicewa da wannan mutuwa da yazo musu a bazata,cikin kuma lokacin da suke tsananin bu ata da fatan Zainab ta rayu ta raini Kyakykyawan iyar ta,sai dai shi Allah baya barin wani don wani,da zaran yayi kira dole a amsa kiransa,to hakan ne ta kasance aka auke Zainab aka bar jinjiran ta,Alhaji Sameer wanwar aka kai shi asibiti baisan wanda ke kansa ba sabida tsaban gigita da fita hayyaci,jininsa yai wani irin hawa cikin ani lokaci,don ko sallan janazanta bai samu ba yana asibiti aka kaita gidanta na gaskiya,duk wanda ya shiga gidan ta'aziyan Zainab dole ya fito da kuka sabida tausayin Iyayenta da danginta,da kuma baiwar Allah jaririyan da ta bari,wacce Iya ta ke ri e da ita gam ta kankane ta hana kowa,ita ke bata madara idan tai kuka tai mata komi,Yayar Zainab in ko Anty Mardiyyah ko magana bata iyawa sai kuka,har akai bakwai suna cikin wani irin yanayi na alhini me ta a zukatan masu tsoran Allah,a kuma ranan bakwai inne akai zama da an uwan Zainab in akan son abasu jinjiran su ri e,amma Iya ta daka tsalle tace bata san wannan zancen ba,babu me raba ta da jikanta indai tana raye wacce tunda tai kwanaki bakwai aka sanya mata sunan Mahaifiyanta wato Zainab,kuma nan take aka cigaba da kiranta da TAIMIYYAH kaman yadda ake kiran Marigayiyan,duk yadda Anty Mardiyyah ta so abata ri on Little TAIMIYYAH amma Iya ta ashe asa tace bata san zancen ba,shi ma kuma uban yarinya Alhaji Sameer ya nuna yafi son arsa a wajen Mahaifiyansa,haka suka ha ura aka bar yarinya a wajen Iya,wanda ya zama sila da kuma tushen tasowan TAIMIYYAH a wajen kakarta Iya,wacce ta maye mata gurbin uwa ta kuma bata nagartacciyar tarbiyan da uwa tagari zata baiwa ar ta,Zuwaira tun TAIMIYYAH tana arama ta tsane ta sabida irin yadda Iya ta auki son Duniya ta aura akan TAIMIYYAN,sam bata bi takan Zuhrah da suka taso kusan kai aya da TAIMIYYAN,sai dai shi ma Sadeeq da zuwa lokacin ya da e da shiga makaranta yayi wayo yana da shekaru hu u,duk inda yaje ya dawo zaka same sa a Sashin Iya yana nane da ita yana shafa kan TAIMIYYAH,a hankali rayuwa ya cigaba da garawa yaran suna wayo,soyayyan da Iya ke wa TAIMIYYAH na sake fitowa fili,lokacin da su TAIMIYYAH ke da shekaru biyu suna gudunsu ko'ina ita da Zuhurah wacce ta bata watanni hu u,tare suke wasa da Zuhurah da Sadeeq ma baki aya,tun Iya bata barin TAIMIYYAH zuwa Sasan Zuwairah don kada ta cutar da ita,har ta ha ura sabida yadda TAIMIYYAN kullum ke nane da su Sadeeq da Zuhurah,Alhaji Sameer da tun mutuwan matarsa yaji gaba aya Zaria tai masa zafi,sai ya zamana ya auke afansa daga zuwa sosai,sai a ha a sati biyu bai shigo garin ba,duk da cewa soyayyan ar sa nanan dan are a zuciyansa irin soyayyan da baki bazai iya misaltawa ba,amma zuwan shi Zarian na masa wani irin fami ne idan har yazo ya bu e Part insu ya ga babu Zainab,shi yasa duk son sa da zuwa ya ga ar sa da ayanzu soyayyan da yake wa uwarta ya gama komawa kanta yake dannewa,sai dai duk wani siyayya na abin bu ata ana jibgewa Iya su,har abin na zarta a'ida sai dai Iya tai ta kwasan rabi tana turawa Zuwairah taiwa Zuhrah anfani dashi,hakan ya sake janyo wani irin kishi da tsanan TAIMIYYAH a zuciyan Zuwairan,tana tsananin adawa da yadda yarinyan ta taso da wani irin kyawu me fisgan hankali,da tarin farin jini, Sadeeq shi ya ra awa Zuwairan Umma tunda ya bu i baki,suma su TAIMIYYAH da bakinsu ya fara bu uwa sai suka bi bakinsa suna kiranta da Umman,a wani dare lokacin su TAIMIYYAH na da shekaru uku ta farka da wani zazzafan Zazza i,gari na wayewa Iya ta kira Alhaji Sameer ta sanar masa,shi kuma ya turo Sani wani yaronsa da ya barwa mota yana kai Iya anguwa da uzurorin kai TAIMIYYAH asibiti idan bu atan hakan ya taso,cikin anin lokaci sai ga Sani ya iso suka wuce asibiti da TAIMIYYAH,tsananin zafin zazza in yasa aka rubuta allurai biyu da xa'aiwa TAIMIYYAN,anyi na farko ranan lafiya lau Iya ta dawo da ita,a washegari aka koma akai na biyun,aiko washegari afan yarinya yai lakaf sam bata iya motsa shi bare aje ga zancen takawanta,babu shiri Iya suka maida TAIMIYYAH asibiti da gaggawa,amma duk iyakan binciken likitoci an rasa gane daga ina matsalar take,domin likitan da yai alluran kowa ya shaida wararrene,daga arshe aka bar abin akan cewa anyi rashin sa'a ne alluran ya ta a jijiya,duk inda tashin hankali ya kai tuh Iya ta shige shi,a washegari Alhaji Sameer ya diro Zaria hankali tashe don ganin lafiyan ar sa,wasa-wasa sai aramar magana ya fara zama babba,TAIMIYYAH afanta da akaiwa allura ya fara shanyewa,ta koma sam bata iya tafiya bare motsa afan,wani likita ya bada shawaran afara mata gashin ashi a asibitin ABU da ke Tudun wada Zaria,cikin ikon Allah ana fara gashin ashin ta fara iya motsa afafun,amma fa har lokacin bata iya tafiya,hankalin kowa a tashe yake da wannan tsautsayi daya gitta a rayuwan kyakykywan iya irin TAIMIYYAH wacce a duk kwanan duniya kammaninta da mahaifiyanta ke sake fitowa arara,Zuwaira ita ce ka ai bata ta a nuna damuwanta akan wannan lalura ba,wanda hakan yasa Iya sake ullatanta a zuciyanta da inta a ranta,fa in irin wahala da fa i tashin da Iya da Alhaji Sameer suka sha akan TAIMIYYAH bazai misaltu ba,kafin Allah yai ikonsa a samu TAIMIYYAN ta fara taka afan da taimakon dafa afan da ya shanye,tun ana ganin kaman idan ancigaba da gashin da yawon asibitocin xata koma da tafiya ba tare da sai ta dafa afanta me laluran ba,har Iya ta fara sarewa ta cire rai tunda ta ga irin shanyewan da afan daya samu laluran yayi,tuni Zuhrah har an saka ta makaranta lokacin,ita kuma Zuwaira tana fama da laulayin ciki na uku,Alhaji Sameer a lokacin da ya sada afan ar sa tabbas ya nakasa sai wani irin aunarta da tausayinsa suka sake kama ruhinsa,kaman yadda ya kasance ga Iya wacce laluran nakasan afan TAIMIYYAH,ya sake janyowa TAIMIYYAN wani irin soyayya da tausayi a zuciyan Iya,hatta da Baba Sani wanda a lokacin ya samu aiki da bankin CBN aka ajesa reshan jihar Kano,ba aramin tausayin TAIMIYYAH yake ji ba idan ya dawo weekend ya ganta,rayuwa ya cigaba da garawa TAIMIYYAH na cigaba da taka afanta bisa tsarin halittan da Allah ya nufa,kullum kuma tana Sasan Baba Sani wajen su Zuhrah,inda abu ka an zatayi Umma zata hauta da fa a tana fa in "Tafi can shegiya gurguwa." Tun Zuhurah bata aukan abinda Umma ke fa i har itama ta fara kiran TAIMIYYAH da suna gurguwa,Sadeeq ne kawai bai ta a bin bakinsu ba ko da wasa,saima wani sha uwa da ke sake shiga tsakaninsa da qanwar tasa,don wani lokacin idan TAIMIYYAH sun ha u da Zuhurah sun ma Umman anna ta bige su,shi za ka ga ya ja TAIMIYYAH gefe yana lallashinta,shi yasa Iya tafi ji da shi a yaran Zuwairan ,lokacin da Zuwairah ta haifo Basmah lokacin Alhaji Sameer ya saka TAIMIYYAH a makarantar boko wani skull da ke tashe a Zaria me suna JETHRO ACADEMY,Sani shi ya zama Drivern TAIMIYYAH yana kaita ya akko ta,su Zuhurah su THERBOW Skull Baba Sani ya sanya su,da yar da fa a da Nasiha Iya ta shawo kan Alhaji Sameer akan maganan aure,har Allah ya ha a shi da Samha ar nan Kaduna Anguwan Rimi,ba'a auki lokaci ba akai bikinsu ya kama mata gida anan Kadunan,don a cewansa bazai kuma sake zaman Zaria ba,sai dai su shigo Weekend ko idan wani abu ya faru su zo su koma,yaso Iya ta amince masa ya auke TAIMIYYAH ya mayar gabansa,amma sai Samha ta nuna sam bazata iya ri e yarinya alhali,ta aure shi a budurwa anya sharaff basu fara moran rayuwansu ba,itama Iya ta nuna sam bata aminta ba hakan yasa Alhaji Sameer da TAIMIYYAH ke
Chapter 16 · 0% Book details