← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 201

Sashe 94

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasan da ke yake son yin magana, tun jiya ya ke neman hanyar da zaku ke6e, dan Allah ki je ku gana." Benazir ce ta fa
Share hawayen fuskarta ta yi tare da mikewa ta nufi kofar ta
an bu
e tare da le
a kanta, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin kwarjini ya yi mata ta yi saurin kawar da idanunta daga kallon shi, mutuncinsa da ya zube a idanunta ada yanzu ya dawo sabo, tun da ta ji komai a bakin Musa.

Ya kafe ta da idanun shi yanata kallonta kamar zai ha
iyeta..

"Zamu iya magana"?

Kamar jira take ya tambayeta, da sauri ta ce, "Eh."
Juyawa ya yi tabi bayan shi suka nufi back yard din gidan, a saman park chair suka zauna wata irin ni'imtacciyar iska ce ke ratsa fatarsu
Ta yi shiru tana jira ta ji me zai ce mata, Idanunta na akan yatsun hannunta da take wasa da su.

Yayin da ya kafe ta da idanunshi, sai kallonta ya ke yi.

"Aisha am..." Katse shi ta yi, "Nasan me zaka ce, komai ya wuce ya Shureim, kada ka yi min magana akan abun da ya faru baya, idan ma akwai wanda ya cancanci ya nemi yafiyar to ni ce, ka yi hakuri ya Shureim na munana maka zato bisa rashin sani, idan na tuna marin da na yi maka a ranar sai in ji bakin ciki ya turnu
e zuciyata, ashe ba yin kanka bane, meyasa banyi maka uziri ba?

Meyasa ban saurareka ba?

Meyasa lokacin da ka ce na tsaya zaka aure ni mu rufawa juna asiri ban yi ba...?"
Bata
are maganar ba ya yi saurin toshe mata baki da yatsan shi, suka
urawa junan su ido yayin da hawaye ke zarya kan kuncinsu, wani irin kallon so da kauna suke ma junan su..

"Aisha bana so kina magana akan abun da ya wuce, mu manta kawai, ina mai baki hakuri akan zaluncin da Uncle Musa ya yi maki, na ji bakin cikin da bazai misaltu ba.
jinjina mashi kai ta yi alamar ta yi...

"Ki yafe min Aisha, na yi kuskure tun farko da ban bayyana maki soyayyata ba, zurfin cikin da na yi shi ya ja min, ban tashi sanin kina sona ba sai da na ji a bakin mahaifinki, a ranar da ya kira ni don ya tuhumeni akan abun da na yi maki...."
labarta mata tattaunawar da suka yi da imam malik ya yi..

"Lokacin da Benazir ta zo dake
akina don ta nuna min ke a ranar dana dawo daga Egypt, na nuna kamar bansan ki ba, amma wallahi Allah shine shaidata Aisha, na yi maki son da ban ta6a ma wata
a mace ba, tunkafin in mallaki hankalina nake son ki, da soyayyarki na girma a cikin zuciyata, lokacin da ina Egypt, bani da abun kallo a wayata da ya wuce hotunanki da videos din da ake yi maki a gurin musaba
a, da zarar an saki videos dinki jiki na 6ari nake zuwa in kalla, dake nake kwana dake nake tashi a raina, kamar yadda kike addu'a a kaina nima haka nake yin addu'a akan ki, kin sha hanani bacci Aisha ..."
Kalamansa sun karya zuciyarta, yanzu ta gane ba ita kadai ta yi dakon soyayyar shi ba, ashe shima ya so ta kamar ran shi..

"A ranar da na gaji da azabtuwa da sonki, na yanke shawarar zan tunkare ki in fa
a maki halin nake a ciki, a ranar ne na jiyo firar da ku ke yi ke da su Benazir a
akinta, na ji kina fadin kinsan babu namijin da zaiso ki tsakani da Allah sai don surar jikin ki, da na ji wannan maganar nan take gwiwata ta sage, na ji tsoron ma in tunkare ki da maganar saboda nasan nima zaki iya tunanin saboda surar jikin ki na ke son ki, dama tun farko abun da ya hana in fa
a maki saboda ina jin tsoron amsar da zaki bani, shiyasa na kasa tunkarar ki da maganar, saboda ina jiye ma kaina tsoron ki ce baki sona, zan shiga mawuyacin hali, haka na ci gaba da tunanin ta wace hanya zan tunkare ki da maganar batare da kin zargi jikinki nake so ba, ban kaiga samun mafita ba, wannan mummunan al'amarin ya faru..."
bata san sa'adda ta kife kanta saman kafa
arshi ba, wani irin son shi ne ke ninkuwa a cikin zuciyarta.

"Yaya Shureim, gaba daya mun yi kuskure da bamu bayyana son da muke ma junan mu ba, nima abun da ya sa na kasa fada maka ina son ka, saboda ina jin tsoron ka ga kamar na zubda
imata, duk da ba haramun bane don mace ta ce tana son namiji, amma wasu mazan na zamanin nan ba su daraja macen da ta ce tana son su, hada kuma
arin nima ina zallumin ka ce baka sona..."
gaba
aya jikin su kerma ya ke yi, sun kasa tsayar da hawayen dake sintiri kan kuncinsu.

"Amma yanzu daka bayyana min soyayyarka, hankalina ya kwanta, sai na ji kamar an yaye min wani sashe na damuwata, ka yi ha
uri ya Shureim na ji kunya, na kuma ji tausayinka da na ji irin izayar da iyayenka suka yi maka kai da babynmu, ashe haka kake son jinina?"
Ta tambaya batare da ta
aga kanta ba..

"Tayaya ba zan so jininmu ba Aisha? har raina zan iya badawa a kanta, a lokacin da nasan tana a raye wlh har raina zan iya sadaukarwa saboda in ceto rayuwarta.

Ina son ta kamar yadda na ke son ki."
"Ya Shureim ko bayan da abun ya faru ban tsaneka ba, saima sonka da ya
ara ninkuwa a zuciyana, kawai dai na yi ba
in cikin ta yadda abun ya faru, amma ya wuce..."
murmushi ya yi, still idanunsa akan ta, ko kyaftasu bai son yi
"Ya Shureim ka ta6a ganin ta?" Ta tambaya tare da
ago kanta ta dube shi.

"Eh, a ranar dana kawo su Benazir gidan nan na ganta, har na taimaka mata gurin cire mata mayafinta da ya sargafe kunnanta.." Murmushi ta yi.

"Ya ka ganta?"
"Kamar na yi kakinta." Ya fada tare da jan hancin ta, murmushi suka sakar ma juna..
(Allah sarki Soyayya ruwan zuma, su boss ko yaushe romeo zai zo
Oh ni, inata aikin jiran baby Junaid.)
"Tun a ranar farko da na fara ganinta nake ta kokarin in tuna dawa ta ke yi min kama, ban tashi tunawa ba sai ranar da na sake ganin ka.

Ina son ta Ya Shureim, ina son jininka sai dai..."
Kasa
arasa maganar ta yi saboda
ululun bakin cikin da ya tokare makoshinta, sakamakon tunawa da ta yi a yanzu yarinyar bata a tare da su, tana can hannun azzalumin mutumin da ya cutar da rayuwarta.

Gefen fuskarta ya shafa,"Aisha nasan me ke damunki, nima ina jin ra
in da kike ji a zuciyarki, but pls, mu yi hakuri mu jure, in sha Allah ba abun da zai faru da su, Allah ba zai bari ya cutar da su ba, tun da mun yi masu addu'oi toh mu jira muga abun da Allah zai yi akai tun da mun yi imanin shine mafitarmu.."
Kalamai masu dadi da kwantar da hankali ya ci gaba da furta mata har saida ya samu ya shawo kanta..

Mayar da kanta ta yi saman kafa
arshi ta dan lumshe idanunta.
~________________Benazir & Anila~
Suna tsaka da yin firar abun da ya faru da su jiya, knocking din kofar da aka yi ne ya katse su.

"May be Aisha ce ta dawo, bari na duba.

" Anila ce ta fada tare da mi
ewa..

Benazir ta ce, "Anya Aisha ne?

Ke kina tunanin ya Shureim zai kyaleta yanzu?

Tun fa jiya da muna yin salla na lura daga an sallame sai ki ga ya juyo da kai ya dube ta.." Duk da halin da suke a ciki na zullumi da fargaba sai da suka dara.
e kofar
akin Anila tal yi,
Taj ta gani a tsaye ya rungume Junaid dake ta yin kuka a
irjin shi..

"Anila tayaya akai Junaid ya ga gawar Ana?

Gashi nan tun da ya farka yake ta kuka yana ambaton sunanta, wlh na yi mamaki, inata lallashin shi ya
i yin shiru." Tausayin shi ne ya rufe Anila, da sauri ta kar6e shi ta rungume a kirjinta tana dan jijjiga shi, fuskarsa ta ji
e sharkaf da hawaye, ta yi mamakin yadda har Junaid ya iya ru
e abun da ya faru bayan baccin da ya sha.

"Ka yi shiru my baby boy, ka daina kuka, ba abun da ya faru da Ana, tana nan.."
Cikin shessheka ya ce, "Mom.. mommy ai na ga Ana, ta mutu, dodo ne ya kashe ta, ba na fa
a maki ba, kuma na ganta bata motsi, Ana ta mutu, ta tafi lahira gidan Allah..."
an zaro ido Anila ta yi ta
an kalli Taj suka hada ido, murmushi suka yi..

"Kana so Ana ta shiga aljanna?" Jinjina mata kai ya yi yana faman mutsustsuke idanunshi..

"To ka yi mata addu'a, amma in ka ci gaba da kuka Ana bazata shiga aljanna ba, ka ga ko mun je wata rana ba zamu ganta ba."
da sauri ya soma share hawayen shi, "Bazan
ara ba, na daina, ina so Ana ta shiga aljanna."
Shafa sumar kanshi ta yi.

"that's my boy."
"Anila, ke da waye ne?

Na ji kamar kukan Junaid."
"Wlh shine Taj ya kawo min, Yaro ya burkice yana ta sambatu kan Ana.." Fitowa Benazir ta yi daga dakin.
hada ido suka yi da aj, gaba daya sun fahimci damuwar da kowan nan su yake a ciki..

"Daddyn Unaisah, ka tashi lafiya?

Ka ci abinci?

Ka yi bacci kuwa?" Da damuwa ya ce, "In har kin yi duk abun da kika tambaye ni toh nima na yi, in kuma baki yi ba, nima ban yi ba.."
Murmushi ta yi, "In har ba su Unaisah ne suka dawo ba, bana jin zan iya cin abinci ko in yi bacci."
Bata
are maganar ba ya katse ta, "Inason magana da ke." Kallon Anila ta yi a lokacin har ta juya ta shige
aki da Junaid..
Chapter 94 · 0% Book details