← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 201

Sashe 78

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ko dai ni da bani da ilmi bazan iya aikata abun daya aikata ba, abun daya faru tsakanin Aunty Ummi da Uncle shureim sharrin shai
anne, bayin kansu bane, duk da ba agabana komai ya faru ba, amma ni ina kyautata masu zato, kuma duk wata kaddara da ta faru da bawa, da akwai wata hikma ta ubangiji wanda mu ba zamu iya gani ba, kamar yadda bamu taba sanin ta arayuwar mu ba sai gashi silar taimakon mu da sojojin America su ka yi mun hadu da ita, kuma mune silar da ta dawo Nigeria harta sake haduwa da mahaifinta, da aminnanta, da kuma ya shureim.."
muryarta na rawa ta karashe maganar, Unaisah tace"kinyi magana mai ma'ana, pls ki share hawayenki, nasan labarin akwai taba zuciya, amma ni ban fada maki donna sanyaki a damuwa ba, tsakanin mu da su aunty Ummi da babynta Addu'a ne da ita kadai zamu iya taimaka masu..." ta fada tana kur6ur juice da ta zuba a cup.

"Chief yayi alkawarin zai sasanta tsakaninta da kawayenta, da kuma Mahaifinta, in sha Allah.."
ta karashe maganar tare da zaro tissue cikin box ta mika mata, yatsun hannayenta na kerma ta kar6a tana share hawayen ta, Unaisah dake satar kallonta, batai mamakin ganin yadda jikinta ke kerma ba saboda tasan irin kaunar da take ma aunty ummi, dole labarinta ya karya zuciyarta, shiyasa ba komai ta sanar da ita ba, ta boye mata batun Uncle musa da kuma binne jinjirar da Uncle shureim ya yi.

"Inama ace babyn aunty Ummi tana araye, da yanzu muna a tare da ita, Ni dai na kamu da son ta, Inason aunty ummi da ya shareim harma da mommynki da Aunty Anila"
dariyar farin ciki Unaisah tayi"kuma kinsan wani abu, dana ji labarin nan sai na ji araina kamar ke ce babyn Uncle shureim saboda bala'en kama da ki ke yi da shi, don dai ta rasu ita bata araye.."
murmushi Batool tasaki aranta tana tariyo farkon haduwarta da Uncle shureim har yau takasa manta lokacin daya cire mata errings dinta daya sargafe veil dinta.

Ganin ta shagala da tunani yasa ta katse ta"mu karasa cin abincin kada ya huce" sai da suka ci suka koshi tukunna suka koma falo a saman sofas suka zauna.

Sai jaraba kiran layin Ummi ta ke yi baya shiga, Har kiran daddyn ta
arayi shima baya picking, ta damu sosai, a karshe ta kira layin Danejo kamar dama jiran kiranta su ke yi, suna
agawa muryoyinsu suka cika kunnuwansu dayake handsfree ta saka kiran
"Angel, Kun manta damu, almost one month and weeks An kulle mu a part din daddy taj, Pls mun gaji, wallahi, Muna so mu dawo inda kuke..

"Unaisah wai har yanzu su Chief basu dawo daga kai farmakin bane?

Muna jira shiru ba labari, Ko mun kira bakya daga kiran mu, Hankalinmu ba akwance ya ke ba ku fada mana in wani abu ya faru pls"
Angel, Ina danish dinmu?

Ina yaya Salsabeel da Chief?

Ina daddy taj, babu mai leko mu, kowa ya manta damu.

"Ni abinci ma yanzu ya daina min da
i, ki6ar har tayi min yawa, baku ga yadda na koma ba, pls Unaisah ku fada ma Chief abude mu, kullen Ya isa haka, mun takura sosai, Muna so mu sakata mu wahala.." muryar Parveen ce
tuntsirewa su ka yi da dariya ita da Batool kamar zasu shake .

"Pls ku kira mu video call mana" maida kiran Unaisah tayi video call, sai gasu reras su goma shabiyar, waro idanu sukayi ganin yadda hutu ya zauna masu, sunyi kiba kamar rainon turai, fatarsu tayi jajir yadda kasan ya'yan larabawa hatta masu duhun fatar cikinsu sun yi fresh fatarsu tayi kyau.
fashe masu da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, ji suke kamar su yi tsalle su shige ta cikin screen din wayar.

Haris sai tambayar Danish Ya ke yi, yana ina?

Ya yake?

Sun dawo daga kai farmaki ko har yanzu basu kaiga zuwa ba, Kasa amsa mashi su ka yi, shiyasa suke fargaban su kirasu saboda tsoron su tambayesu ina Danish gashi kuma duk sun damu da shi sai tambayar shi sukeyi.

"Pls Sis, Ku fada mana gaskiya, ina ji araina kamar wani abu ya faru, sunje kai farmakin ko basu je bane"?

Sajeed ne ya tambaya, fuskarsa amarairaice
dakyar Unaisah tayi karfin halin furta"har sun dawo" waro idanu waje suka yi cikin mamaki da rudu, atare suka hada baki gurin firta"suna ina?

Sunyi nasara?

Meya faru da suka je?

Sun kashe su um?

Sun taimaki sauran prisoners din um?

Kamar yan jarida suka tsare su da tambayoyi.

Numfasawa tayi cikin karyayyar murya tace"sunyi nasarar taimakon fursinoni, yanzu haka suna a asibiti karkashin kulawar likitoci.." tunkan ta kare maganar Suka fara shewar Farin ciki..

"Yar uwata fa?

Hada ita cikin su?

Cike da zumudi Sajeed ya tambaya.

Bata san amsar da zata bashi ba, Batool ce tay saurin cewa"hada ita, wata mai bala'en kama da kai, ai munje asibitin mun gansu, tana nan cikin koshin lafiya, sai tambayar dan uwanta Gabriel ta ke yi"
bai
arasa sauraran Batool ba ya shiga furta Alhamdulillah, Alhamdulillah...

"
"Mu damuwar mu, ina bugun zuciyar mu?

Murmushin ya
e Unaisah ta saki"ku kwantar da hankulan ku, Danish, Yana nan Cikin koshin lafiya, ya
an samu rauni ne shi da ya Omar da salsabeel, shiyasa aka kwantar da su asibiti amma jikin nasu da sauki, har tambayar ku ya ke yi kuna ina muka ce mashi kuna nan lami lafiya.."
jikinsu yayi sanyi lakwas, duk basu ji da
in jin cewa baida lafiya ba, don basu san baya araye ba da ba karamin hauka zasuyi ba
"Ku sanyasu a addu'a pls, ita suka fi bukata" amsa mata sukayi da toh.."
"Amma da su ka je kai farmakin sun kashe Giants da mugayen da suka azabtar da rayuwar mu"?

Mubeen ne ya tambaya
"Sunyi nasarar kashe giant sosai, amma basu kashe elders ba, amma kada hakan ya dame ku, ita nasara ba'a samun ta cikin sauki, sai ansha wahala, cikin ikon Allah yanzu sun fara gano su wanene Elders kuma nan bada jimawa ba, cikin ma kwanakin nan zasu kamosu, gaba daya zamu gansu da idanun mu..." da
ine ya lullu6e su.

"Yanzu mu sai yaushe za'a bude mu daga kurkukun nan?

Muna so mu ganku, ko ku dawo nan, sannan dan Allah ki roki Chief yasa akai mu asibitin da aka kwantar da su danish mu ganshi ko hankalinmu ya kwanta"
acewar haris"Kada ka damu zamuyi masa magana"!

"Nima pls, ku rokarmin Chief, ya taimaka ya hadani da sister dina"
Batool tace"kada ka damu zaka hadu da ita, yanzu bayanan in ya dawo zamu fada masa"
Haris bai yarda da maganganun su unaisah ba, yana kokwanton in gaskiya suka fada musu ya dai bar abun aransa, tun da ba yadda zai yi.

"Ina Aunty Danejo na"?

Jemimah tace"tana can dakin ta kan gado ta hangame baki tana bacci, Ni na sato mana wayarta, don mu kiraki, Kuma munata kira ma bata shiga.."
yalkyalewa su ka yi da dariya..

"Munyi missing dinku, kuna aran mu, idan akwai abunda ke damunku bayan wanda kuka fada mana ku sanar damu" cikin kulawa batool tayi maganar .

Har suna hada baki gurin furta bamu da damuwar komai, akwai abinci available ga kayan more rayuwa kawai mudai so muke abude mu mu dawo gurinku sannan akaimu mu gano su danish din mu.." murmushi suka sakar masu..

"Okay zamu fada ma Chief idan ya dawo, duk yadda mukayi da shi zakuji daga gare mu"..

"Dan Allah kada ku manta, babu kyau jan rai, kullum haka kuke ce mana kuma sai muji shiru ko mun kira bakwa dagawa akai akai" acewar rubina..

"Wannan karon ba zamu manta ba, in sha Allah" amsawa sukayi da toh.

"Kunyi kyau, kun
ara haske, wasu sunyi
iba, tubarkalla masha Allah.." dadine ya lulu6e su jin abunda Unaisah tace..

Sarah tace"kuma haka, kun kara kyau,.."
"Mungode, Ku more lokacinku, soon zamu zo maku da abun ban mamakin da zai girgiza ku"
"We can't wait to see" Cikin nishadi suka cigaba dayin fira da yan uwan su sun debe masu kewa, baka jin sautin komai a falon sai sautin dariyarsu da surutun su, kamar wadanda suka shekara basu gana da juna ba..
~_____________________________
Around
arfe karfe shida na marece, ta farka da wata irin kasala a jikinta, tana kokarin motsawa taji ta a jikin mutun, bu
e idanunta tayi a disashe take kallon fuskar shi, tunawa tayi da abun daya kawo ta, a ru
e tayi dabarar raba jikin ta daga nashi ganin baccin nashi ya yi nisan kiwo farkawarsa ba yanzu ba, ta karance shi tun da jimawa, In ya fara bacci da wuya ya farka ko da za'a buga ganga ne a kusa da kunnansa.
zanan tattoo din bayansa ta
ura wa idanu ya fito sosai, cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta janyo rigart
a daya cire mata, ta saka a jikinta, gabanta na fa
uwa ta
auko wayar ta daga cikin yar purse dinta data jefar
asa, gabanta na faduwa ga tsoro da fargaba da suka mamaye zuciyarta ahaka ta nufe shi, bayan ta kashe camera sound din wayar ta saita bayan shi da camera ta
auki hoton tottoo din shi.

Cikin san
a ta juya ta nufi toilet dinsa, ta bude ta shiga daga ciki, taja
ofar tare da yin locking dinta, ajiyar zuciya ta
an sauke, Yatsun hannunta na kerma ta tura ma Chief hoton tattoo dinsa ta whatsapp chat dinsa.

Unexpected taji anyi knocking toilet door din, waro idanu waje tayi tare da hadiyar yawu..

Daga waje tajiyo voice dinsa da alamun bacci bai ishe shi ba ya furta"Ummi, na farka ban ganki ba, kina a ciki'?

Wani irin faduwar gaba taji, da rudu ta zare idanu aranta ta ayyana tayaya akai ya farka da wuri?

Mutumin dake da nauyin bacci, Dakyar ta furta"yeah am in wanka zan yi"
"Okay, open the door for me, nima zanyi wankan" dafe kirji tayi da hannu
aya, ta rasa ina zata saka phone dinta, Idan har yaganta da waya a cikin toilet zai zargi wani abu, kuma idan ta hana shi zai iya zarginta tun da sun saba yin wanka atare wani lokacin.
Chapter 78 · 0% Book details