← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 201

Sashe 157

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke kika jefani a halin da nake ciki Unaisah, kallonki da nakeyi a yanzu ba karamin fusgana kike ba.."
gabanta ne ya fa
i ta manta rigar bacci ce a jikinta time din daya kira picking kawai tayi ba tare data rufe jikinta ba, a rude ta soma dudduba jikinta duk fa yana kallonta da alama ta manta.

Mikewa tayi daga kan kujerar ta je ta dauko throw pillow da duvet, ta dauki wayar ta koma kan couch ta kwanta tare da rufe rabin jikinta da bargon, ta rungume pillown a kirjin ta.

Saida ta daidaita nutsuwarta tukunna ta saita fuskarta akan screen din wayar..

"Hello!

Husband to be kana ji na"?

Shiru taji bai tanka mata ba..

Tayi zaton matsalar network ne, batasan duk wani motsinta akan idanunsa.

Har ta fidda rai da sake jin muryar shi taji yace"Ina ma ace nine kika rungume kamar yadda kika rungume pillow din hannunki.."
runtse idanunta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa, sometimes idan yana furta mata kalaman soyayya har tunani takeyi ina matarsa Nazli sarauniyar kyau?

Ko itama yanayi mata irin haka?

Ko da yake ita da take agida ai already tafi ta jin ire iren da
an kalamansa.

"Am sorry idan baki ji dadin maganata ba, bazan iya jurewa bane Unaisah, ni kadai nasan halin da nake shiga idan ina sauraron muryarki, kona kalli fuskarki shiyasa na haramtawa kaina ganinki har sai bayan an shafa fatihar auranmu, a lokacin dana tabbatawar kaina kin zama mallakina halak malak..."
nema ya ke ya kasheta da da
an kalamansa gashi yanzu baya kunyar gaya mata irin wadan nan kalaman, gaba daya ya haifar mata da jin kasala a jikin ta..

Cusa kanta tayi cikin pillow duk wani abu da ya ke ji itama tana jin shi sosai..

Cikin harshen turanci ya daura da cewa
"A wannan lokacinne zan bayyana maki irin kaunar da nake maki kamar raina, zan gatantaki Unaisah, zan baki dukkan kulawata da soyayyata, zan mantar dake duk wani bakin ciki da kika taba dandana a cikin zuciyarki, zaki zama sarauniya a masarautar gidana, zan zama hadiminki me yi maki hidima, zan kuma zama sojanki mai baki kariya, in kuma zama likitan da zai dinga ceto rayuwarki a kowani hali na ciwo, na maki alkawari a dare
aya zan canza maki rayuwa.."
bitting lower lip din ta tashiga yi tsigar jikinta na
an tashi
Cikin rawar murya ta furta"yaya Owais, bacci nake ji, sai Allah yakaimu, ka kulamin da kanka.."
tana karashe maganar bata jira amsarshi ba tayi rejecting call din.

Fashewa tayi da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya ya tuna mata yanayin da su ke shiga ita da Danish idan suna a tare, da
yar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ita.

Allah yayi dare gari ya waye, Da sassafe Amarya da
awayen suka farka daga bacci kowaccen su ta shiga toilet tayo wanka, suka shirya kan su cikin abaya, Already an tanadar masu abinci mai rai da lafiya na breakfast din su a dining area..

Bayan da suka zauna yin beakfast, kowa Ya ci ya koshi, In ka cire Unaisah data kasa ci dayawa, kalaman chief owais ne keta dawo mata a cikin tunaninta, duk ta rasa sukununta, da tunanin shi ta farka daga bacci, batason ganin komai in ba shi ba, gashi ya haramtawa kanshi zuwa zance har sai bayan an shafa fatihar auransu.

Around
arfe shabiyu na rana, Benazir ta kira Unaisah awaya ta ce tana son ganinta tare da
awayenta, su hadu a part din Danejo...

Bayan ta sanar da su, gaba
aya suka dunguma izuwa Sashen Aunty Danejo, suna shiga main falo suka fara hango ha
un Invitation bags a saman rug, daga jikin kowace jaka an rubuta will you be my Bridemaid? tare da sunan mamallakin jakar.

Nan take suka gane nasu ne za'a basu, farin Ciki Ya cika su kamar su zuba ruwa kasa su sha.

Anan suka taras da Benazir da Ummi tare da Danejo, with respect suka gaishe da su, Unaisah ta zagaya ta bangaren mommynta tayi hugging din ta bayan sun gaisa tayi hugging din Danejo dake ta sakar mata murmushi.

Batool tuni ta yi gurin mommynta, su kayi hugging din juna.

Bayan sun gama gaggaisawa da
an matan amarya..

Benazir tace"gaba daya munayi maku barka da zuwa, jiya bamu samu zama ba, shirye shiryen biki ya hana mu leko gurin ku, shiyasa bamu samu zuwa munyi maku barka da zuwa ba, amma kuna aranmu, munji dadin zuwan ku..." Ummi ta
aura da cewa"muna fata kunyi bacci lafiya kun tashi lafiya, Ya kuma gajiyar zaman
un shi"
atare suka hada baki gurin furta"Alhamdulillah, Mun tashi lafiya, muma munyi farin ciki da kuka gayyace mu, kuma in sha Allah da mu za'a kare bikin nan"
murmushi suka saki gaba dayansu sunji dadin maganar su.

Danejo tace"wadannan invitation bags din da kuka gani, musamman saboda ku ango ya bada akayi maku daga Company, ba wai iya jakar bace, hada kyaututtuka na musamman a cikin su, Kun shirya gani?.."
Ihun Farin Ciki suka sanya tare da shewa Yeehhhhhh..

Ummi tace"yawwa my ladies, ku jera layi, duk wadda muka kira sunanta sai tazo ta kar6i nata"
cikin sauri suka shiga layi suka yi shiru cike da zakuwa suke jira abasu don su ga menene a ciki..

Ummi da Danejo ne ke daukar bags din idan suka duba sukaga sunan dake a jiki sai su kira su ba mai ita..

"Sadeeja, Zeenatu, kuzo ku kar6i naku" Benazir
ce ta kira sunansu atare.

Bayan da sukazo ta damka masu bags din a hannayensu kafin ta manna masu peck a forehead dinsu"yan matana, Allah ya nuna min naku da raina da lafiyata..."
ta fada tana shafa kafadarsu cike da jin dadi suka amsa da ameen Aunty tare dayi mata godiya.

"Deejatun harisu!

Azeeza matsoraciya, naja'at Sojanya foodie Rai ba aburi, kuzo ku kar6i naku.."
Unaisah ce ta kira sunayensu tana jin dadin tsokanar su, gaba daya mutanan dake falon suka tuntsire da dariya jin sunayen data kirasu, Benazir sai kallonta takeyi kamar zata hadiyar yar tata, wani irin alfahari ta ke yi da ita.

Bayan ta mimmika masu bags din su, ta
aga murya ta furta"UKHTY will You be My babbar kawar amarya?

Ta fada tare da daga jakar dake a hannunta sama mai dauke da sunan Batool.

Farin cikine Ya lullu6e Batool da sauri ta nufeta suka rungume juna.
kallon juna Ummi da Benazir su kayi wani dadine ya lullu6esu ganin yadda ya'yan nasu suka hada kansu, suma sun zama aminnan juna kamar dai su
Bayan Sun gama rarraba masu jakunkunan, tun anan wasu suka fara budewa suna duba kayan dake a ciki..

A hankali Batool ta zaro outfit din da ke a ciki, fitted gown ce dinkakkiya, ta code lace maroon da ashoke, asaman sofa ta daura kayan, ta fiddo
invitation card mai
auke da event programmes, hada phone case with wedding logo harafin sunan amarya dana Ango ne a jiki O&U ga wani karamin kit, bayan data bu
e cikin shi, tissues ta gani tare da breath mints and pain relievers.

Murtuke fuska tayi wani irin 6acin raine Ya turnuke zuciyarta, babu wanda ya lura da yanayinta sai Unaisah dake ta satar kallonta, aranta ta ayyana meke damun Batool?

Kishi take dani?

Ko bakin ciki takeyi!

Ya Allah kasa zargina karya zamana gaskiya.

Batool in wani abu kikeso ni me iya bar maki ce ta fada a ranta.
awayen amarya sun rude da ganin zunzurutun kyaututtukan da aka basu, ango ya gama masu komai, sun fahimci Yana ji da su, sai santin kayayyakin sukeyi suna yabawa banda babbar kawar amarya.

"Yeehh hohoho Wayyo Allahna Nima ga nawa kayan"
Jemimah ce ta furta da karfi, gaba daya hankali ya dawo kanta, tana akan kujera ta zazzage kayan dake a cikin jakarta sai washe baki takeyi farin ciki Ya cika ta..
yacewa su ka yi da dariya suna kallon ta.

"Amma ni abin daya
aure mun kai?

Tayaya akai wadanda suka dinka mana kayan sukasan size din mu, ku dube ni ku gani?

Nayi kyau"?

Parveen ce tayi tambayar yayin da take nufo su daga wani daki ta fito, jikinta sanye da kayan data gwada.

Sakin baki su ka yi suna kallon ta, Kayan sunyi mata kyau sunbi shape din jikin ta.

Benazir tace"masha Allah, autar minister, you look gorgeous, nafi tunanin angone ya bada awonku may be yana da shi, Ko kar6a ya yi agurin parents din ku"
har suna ha
a baki gurin yi masu godiya.

Ummi tace"bamu yakamata ku godemawa ba, Unaisah da angonta.." sunnar da kai Kasa Unaisah tayi, gaba daya suka nufeta sunayi mata godiya"thank you sis, pls ki fadama hubbynki muna godiya, Allah ya kaimu lokacin da rai da Lafiya, Allah ya cika maku burinku" kasa kasa da murya take amsawa da ameen.

Tana lura da Batool data ha
e rai, sai ci ka takeyi tana batsewa, kowa yana yi mata godiya ban da ita, ta rasa gane laifin me tayi mata
"banga na yan uwanmu maza ba, Ko su banda su ne"?

Deeja ce ta tambaya taji shiru ba abata na yayanta ba..

Benazir tace"hada su, amma nasu ba gurin mu aka kawo ba, ai su ta bangaren ango suke ko"?
ta fada tare da
age mata gira..

Dariya Deeja tayi"nagode auntyn mu.."
Cikin kwanakin da suka rage, bothside dangin ango da dangin amarya sun dage damtse suna ta shirye shiryen Bikin ya'yan na su, haka zalika Amarya da ango suma shiri su ke yi na musamman domin tarbar ranar auran su.
*ANEELERH
Fitowa tayi daga Bedroom din ta dake a downstairs ta nufi main falo, sanye take da bubu gown ta material, tayi rolling mayafi akanta, Masha Allah ta zama babbar mace, fatarta tayi haske irin na wadanda hutu ya samu mazauni a jikin su, daga gani tana samun kulawa agidan mijin ta.

A cikin kunnanta ta tsinkayi muryar mijin nata "idan ina yi maka Assignment ka dinga maida hankali akan bayanin da nake yi maka, kana ji na ko"?
agowa tayi a hankali ta
aura idanunta akan shi, Su biyu ne zaune kan rug, ya tasa baby junaid agaba yana yi masa Assignment da textbook dinsa, daga gefen sa Laptop dinsa ce da ya ke aiki da ita..
Chapter 157 · 0% Book details