← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 201

Sashe 15

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....."
kasa
arasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un..

"Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..."
Benazir bata
arasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu.

"Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.."
Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse
ofar.
*Daga Al
alamin Boss Bature
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
~___________________________________~
A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu
auke da damuwa.

"Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki fa
a ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi
ona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......"
yar Benazir ta
are maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa.

Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin.

"Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda ba
in cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan"
Aneelerh ta
aura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki fa
a min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu?

Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike?

Kina raye ko kin mutu?

Meke faruwa a cikin rayuwar ki....

"
Aneelerh bata
arasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba
aya
okin ganinki mu ke yi"
Babu alamun zata tanka masu.

"Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita"
Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun ka
a jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake sa
awa a cikin Zuciyar shi.

Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su.

"Pls ina son insan meye ala
arku da Aisha ne?

A nan take zaune?"
Murmushi Taj ya
an yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar.

A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya
ara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..."
Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita.

A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina!

Meke damunki?

Meyasa ki ke kuka?

Waya 6ata maki rai!"
Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so!

Ki fa
a min meke damun ki?"
dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini!

Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi!

Baki ji radadin da nake ji ba..."
sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ru
ewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa.

"Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake
ba?" ta fa
i hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi.

Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta mi
ar da ita zaune saboda karfin hali irin nata..

Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest
inta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta ha
u data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya
auka har a jikinta tana jin shi.
ewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki..

"
ta fa
a tana
arin
wace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta fa
a ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi ta
i bari ta motsa.

Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta.

Kafin Ta
aura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke
an bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya.

Ji ta yi inama ace Batool ce
iyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran da
ewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne.

Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta
ara tabbatar da hasashen ta.

"Aunty Ummi da sauki?"
Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh .

Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu
aya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da
afarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arzi
i ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar
afa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sau
i, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya fa
a tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta
arin mi
ewa yana kasawa har saida Dr.

Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi.
__________________________________
Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta
urawa ceilling idanunta da suka ka
a jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita?

Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi
ona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka?

In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta?

Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai ma
ura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara.
_______________________________
Around
arfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari
aya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit.
Chapter 15 · 0% Book details