← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 201

Sashe 90

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ru
o hannayenta ya yi a cikin nashi, saboda kerma da jikinshi ke yi itama nata jikin ya kama kerma idanunsu a cikin na juna yana kuka tana kuka ya ce, "Allah Ya yi maki sakayya Aisha, Allah ya bi maki hakkin ki.

Wlh bamu ya cuta ba kanshi ya cuta, la'ananne, In sha Allah sai rayuwarsa ta wula
anta tun a gidan duniya, na yi danasanin sanin shi a rayuwata, dama wasu mutanan Allah yana hadamu da su ne don ya jarabcemu da su, wasu kuma don su zama alkhairi a cikin rayuwarmu.."
kasa
arasa maganar ya yi saboda kululun bakin cikin da ya tokare makoshin shi, ya ji zafi a ranshi, bakin ciki ya cika shi kamar zai ha
iyi zuciya ya mutu.

Kwantar da kansa ya yi saman kafa
ar Ummi, ya
aura hannayensa a saman bayanta.

Cikin sigar lallashi yake dan bubbuga bayan nata, tsananin tausayinta ne ya kama shi, saboda gaba daya rayuwarta a cikin jarabta ta ke, kowa dake a falon sai da ya tausaya masu, Hajiya Laila ta yi danasani, sai cizon yatsa take yi, gani take kamar hada laifinta komai ya faru, idan har Musa yana sarrafa Alhaji Ubaid da sihirinsa toh ita da hankalinta take yin komai.

A fakaice ta dinga share kwalla tana satar kallon Aisha da mahaifinta..

Cikin ru
u Alhaji Ubaid ya ce, "Har yanzu na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye min!

Dan Allah ku fahimtar da ni!

Kaina ya
aure, Wani musan kuke nufi?
anina musa ko wani musan ne daban?"
Hajiya Layla ta yi saurin cewa, "Wallahi zai aika!

Fiye da haka ma, ai baida mutunci ko ka
an, mutun sai bakar zuciya kamar ta kafuran farko, na da
e ina zargin ba mutumin kirki bane Musa, kuma dukiyarsa bata Allah da Annabi ba ce, Ai ni bazan ma Musa ba..."..

Benazir ta kar6e da cewa, "Abun da Aisha ta fa
a gaskiya ne daddy, na dade ina jiran wannan ranar da zan fadi ta cikina, ku yi hakuri da ban ta6a sanar da ku ba, na boye maku ne saboda nasan zai yi wuya ku yarda da ni a wannan lokacin, saboda ku kan ku sai yadda ya yi da ku...."
mayar da hankalinsu su ka yi akan Benazir..

A tsanake ta labarta masu komai da ya faru tun daga lokacin data ta kama shi yana yin waya agidan shi, har izuwa kan asirin da ya yi mata..

Daura hannu biyu Hajiya Layla ta yi akanta.

Mami ta zabga salati, Dr Shureim ya zabura ya mike a kidime jin
arsa da ya binne Uncle Musa ne ya dauke ta, yama kasa magana sai zazzare idanunsa ya ke yi gaba
aya ya ru
e, nan ta ke
walwarsa ta fara tariyo masa abubuwan da suka faru a baya, lokacin da ya je ya tone
abarinta ya ga
asusuwa saida ya yi zargin wani abu, just in two weeks da ya binne ta har ta zama
ashi, bayan haka ya da
e yana ji aranshi tana a raye saboda bai ta6a mafarki da ita a mace ba, Ya Ilahi!

Yanzu ya gane komai.

Jirin tashin hankali ne ya
ebesa yayi taga taga zai kife, Alhaji ubaid ya yi saurin mi
ewa ya tallabo shi, tare da rungume shi kan kirjinshi, kukan ba
in ciki ya fashe da shi kamar ranshi zai fita, tuni zazzabi da ciwon kai sun kama shi.

Sheikh Imam ya
ara shiga damuwa daga shi har Aisha jin rashin imanin da Uncle musa yayi ma Benazir saboda kawai ta nemi ta tona masa asiri don ta
watarwa Aisha hakkin ta.

Cikin shesshekar Kuka Hajiya layla ta dinga
ura mashi ashariya tana tsine masa albarka, dama da
iyayyarsa aranta, bata ta6a son shi ba, kwata kwata baya burgeta saboda izzarshi, ta tsane shi ta tsani komai nasa.
wallar bakin ciki ce ta cika idanun Alhaji Ubaid, cikin rawar murya yake ambaton duk wata addu'a da ta zo bakinsa don ya samu sassaucin radadin da zuciyar sa ke yi masa.

Abie da ke zaune a gefensa dafa kafadarsa ya yi batare da ya iya furta kalma ba, kowa ya razana da jin abun da Musa ya aika ta.

Babu wanda zuciyar sa bata karaya ba..

"Har yanzu baku fayyace mana komai ba, Ina so in san wace irin sadaukarwa ce Musa ya yi da yarinyar Shureim da kuma yarinyar Benazir? suna a raye ko sun mutu?"
Cike da fargaba Abie ya yi tambayar, saboda yana son yasan in duk a tare suke da
an Iya.

Shiru su ka yi saboda basu da amsar tambayar da zasu ba Abie.
_Taj Ka fa
a masu komai, yanzu lokaci ne da kowa yakamata yasan gaskiya, Illa iyaka kowa ya yi hakuri da abun da zai ji_
Zuciyarsa ce ta raya ma shi.

Gyaran murya ya yi hankalin kowa ya dawo kan shi.
falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta, baka jin sautin komai sai na muyar Taj dake basu labari..

Ya fara ne daga kan labarin le
en asirin da suka yi wa matsafa shi da Uzair, rabuwarsa da Unaisah da hannun da kowan nan su ya fa
a, Alherin da Chief Owais ya yi masa da kuma ha
uwarsa da
arsa bayan shekaru..

Lokacin da ya fara basu labarin gidan kurkukun
addara, saida suka yi danasanin jin labarin shi, saboda matsanancin tashin hankalin da suka shiga, sun ru
e sosai, sun razana, zuciyarsu ta tsinke da jin irin azabtarwar da ake yi wa yaran da basu ji ba basu gani ba.

Babu wanda bai share
walla ba acikin su, kuka ne ya kubcewa Benazir da Anila kamar ransu zai fita, Hatta Hajiya Layla da Mami saida suka yi kuka na fitar hayyaci, shi Alhaji Ubaid ma kukan zuciya mai radadi ya kama yi, shi da Abie, musamman da ya zo kan labarin Unaizah abin ya ta6a zuciyoyin su.

Jin abun suke kamar ba a gaske ya ke faruwa ba saboda ru
un da suka shiga.

Bayan ya
arasa basu labarin, ya juya ya nufi sitting room din Chief ya
auko diary din Unaizah wanda tun shekaran jiya da ya shiga
akin ya gan shi akan table.

Bayan da ya dawo hannunsa ru
e da diary din, ya Mi
a masu ya ce yana so kowan nan su ya dubi hotunan dake a cikin diary din da kyau.

Alhaji Ubaid ya fara mika mawa hannunsa na kerma ya kar6a tare da bude shafin farko, wata zabura ya yi ya mike a firgice yake tambayar diary din wanene?

Mai ya kawo hoton Musa da na
arsa Zeenatu a cikinsa.." Da jin wannan maganar yasa Benazir ta mike cike da rashin kuzari ta nufe shi, hajiya Layla ma tuni ta mike tana le
a hoton ta furta, "Kai!

Ai Zeenatu ce wannan!

Da Musan!

Me ya kawo hotunansu anan?

Wace ce kuma wannan baturiyar?" Ta tambaya a ru
Kowa sai da ya duba hotunan, bayan da suka gama kallo, Taj ya fayyace masu komai game da diary din, ya ce yarinyar da suka gani ba Zeenatu bace sunan ta Unaizah, twin sister din yarinyar wurinsa ce da ya sadaukar tun tana jaririya ya rabata da mamanta ya kaita England gurin karuwarsa ta raine ta.

A bayanin da Taj ya yi masu suka fahimci yarinyar da yake yin magana akai itace ta kurkukun nan wadda ubanta ya yaudare ta.

Kansu ya daure tamau, lamarin ya girmi tunanin su!

Hajiya layla ta ce, "Anya Musa mutunne ba shai
an ba?" Ta ce ta na kokwanto, saboda rashin imaninsa ya yi over, kamar babu zuciya a kirjinsa, abun da ya fi basu takaici cin amanar da yayi ma hajiya Sarah, baiwar Allah batasan twins ne ta haifa ba, Har yar cikinsa bai bari ba, ya zata ji idan ta ji abin da ya yi ma
arta?

"Kakan Chief Owais Shine shugaban Kurkukun
addara, Kamar yadda Musa ya ha'ince ku, shima haka kakansu ya ha'ince su, ya dade yana sadaukar da jikokin family dinsu agidan kurkuku batare da sanin su ba.

Musa Yana
aya daga cikin Elders na kurkukun
addara, Shine Jan wuya, kawun Anila shima yana
aya daga cikin Elders..."
Duk da sanyin A.c din dake falon hakan bai hana su fitar da gumi ba, saboda tsantsar tashin hankalin da suke a ciki, gaba daya sun razana da jin maganarsa, rudu yasa suka shiga tambayar shi wani Owais din yake nufi kuma wani kakan nasa?"
"Obinna," ya fa
a masu ne saboda su kwantar da hankalinsu, su san cewa basu ka
ai ta shafa ba, hakika sun razana fiye da yadda suka razana da jin munanan laifukan da Musa ke aikatawa, kamar an kashe masu bakunansu gaba daya suka yi shiru kamar masu zaman makoki.

Abie ya ce, "Inama ace mafarki ne komai ke faruwa?

Wannan wace irin musiba ce ta kunno mana kai?

Wani irin neman duniya ne wannan da zaisa ka dinga azabtar da rayuwar bayin Allah wa
anda ba su ji ba ba su gani ba? ka manta da lahirar ka, Ka dauki rai ba a bakin komai ba?

Hakanan bawa ya jefa kansa cikin bala'e ya kuma jefa ahalinsa, ina amfanin irin wannan rayuwar da suka
aukarwa kansu?

Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." Ya fada yayin da hawaye ke zarya kan kuncinsa.

Jikina ya yi sanyi wai an jefi kaza da gishiri, wlh komai na duniyar nan ya sire min,
an adam ba abun yarda bane, In har uba zai iya kwanciya da
ar cikinsa meye kuwa bazai faru ba?

Da yawa wasu fitintinun da ke faruwa da mu daga laifukanmu ne, bawa shi ke ja ma kanshi, tayaya zamu ga daidai bayan irin zunubban da muke aikatawa, tayaya zamu zauna lafiya bayan irin fasadin da ake aikatawa a doron kasa?

A kashe wanda bai ji ba bai gani ba, ko a azabtar da shi, A tauye masa hakkinsa na rayuwa!

Meyasa wasu basa tunawa da cewa kamar yadda suka kashe wata rana suma mutuwar zata riske su kuma basu isa su dakatar da ita ba?Ina zaka je da hakkin rayukan dake akanka?

A ranar daka farka ka ganka a cikin
abari batare da komai na duniya da kake ta
ama da shi ba ya za ka yi? kafin ka aikata ba daidai ba ka fara tunanin menene makomarka?
Chapter 90 · 0% Book details