← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 201

Sashe 183

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta katse kiran ta kira layin daddynta Sheikh Khalid after yayi picking cikin harshen larabci
yace meyasa yanata kiranta bata picking? yana fata tana lafiya"
rasa amsar da zata bashi tayi.

Jin tayi shiru bata bashi amsa ba yasa shi furta"amsarki nake jira," numfashi taja tare da daidaita nutsuwarta kafin cikin sanyin murya tace"Alhamdulillah, ina cikin koshin lafiya baba, ina fata kaima haka"!
daga yanayin muryarta Ya fahimci babu kwanciyar hankali atare da Gimbiyar tashi.

"Meke damunki?

Naji muryarki da damuwa"
da sauri tace"babu abun da ke damuna, mura nakeyi, amma nasha magani, da sauki"
"Allah ya baki lafiya, ki kula min da kanki" ta amsa da ameen.
sun da
e suna yin waya kafin su ka yi sallama..
ewar da zatayi keda wuya sai ga khadima ta yi knocking kofa.

Fitowa tayi daga dakin Khadimar ta sanar da ita medical team zasu tafi suna jiranta, da sauri ta nufi Down, Khadimar ta take mata baya, tana karasa saukowa down ta iske medical team din, wannan karon da walwala akan fuskokin su ga dukkan alamu sunyi nasara.

Har suna ha
a baki gurin sanar da ita cigaban da suka fara samu akan Lafiyarsa sannan sukace kullum zasu dinga zuwa duba shi har zuwa lokacin da zaiji sauki, godiya tayi masu tare da jinjina, bayan sunyi sallama har suka tafi basu daina santin kyan patient dinsu ba, sun kamu da kaunar shi, sun kosa ya samu lafiya don suyi magana da shi, ba dan suna jin nauyi da shakkar gimbiya mujeedat ba da sai sun tambayeta menene alakarta da shi saboda sunyi mamakin yadda ta rude akan shi, da kuma kamanninsa da Nazli asaninsu bata da
a namiji amma sai gashi yau sunga wani zanka
an saurayi kyakkyawa daya tafi da imanin su, gashi ta garga
esu akan bataso kowa ya san wani abu game da kiransu da tayi da kuma yaron, sirrine in har suka sa6a sharadin data gindaya masu zasu fuskanci hukunci, shiyasa ko gulmarsa suka kasa yi sai dai suka bar abun aran su.

Lokacin da tashiga dakin akwance ta same shii Yana sharar bacci, bawan Allah ya sha alllurai.

A hankali ta zauna daga gefen gadon, Ta ruko hannun shi a cikin nata, ta sumbace ce ta
ago tana kallon fuskarsa dake asanye da oxygen mask.

"Allah ya baka Lafiya Omair, Allah ya tashi kafadunka, ya Allah ka musanya lafiyarshi da tawa, ni kamayar mun da ciwon nashi a jiki na, saboda ba zan juri ganinsa a mawuyacin hali ba, na damu da kai bugun zuciyata..."
duk wani motsinsa akan idanunta, Owais ya kirata yafi sau akirga duk bayan mintuna saiya kira ya tambayi ya jikin Danish saboda ya damu da shi.

Tsantsar kulawa take bashi kamar jinjiri, Lokacin sallah ka
ai ke sa tabar
akin, ko motsi ya yi sai ta tambayi yana lafiya?

Ba ci ba sha ko da chefs suka fa
a mata sun kammala shirya mata Lunch, tace masu bazata iya cin abinci ba, su tafi kawai, haka ta wuni har dare tana tare da shi.

A gefen shi ta kwana, ru
e da hannunsa a cikin nata..

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah, Har Danish Yayi One Week Agurin Mommyn sa, jikinsa Ya murmure lafiya tafara samuwa a jikin shi, ta ko'ina kulawa yake samu daga bangarori biyu, docs din da ke zuwa duba lafiyarsa kullum da kuma Mommynsa dake tsaye akan sa, itace mutun ta farko da ya ke fara yin tozali da ita a duk lokacin daya farka daga bacci, saboda tsantsar kaunar da take masa da kulawa bata bari ya yi komai da kansa in ba shiga toilet ya kama sa ba, abinci abaki ta ke bashi ya ci, da kanta ta ke wanke mashi sumar kanshi ta gyara mashi ita, bata barin shi cikin ka
aici.
tun aranar daya samu sau
i ta lura bayayin sallah, ta kasa yin shiru har dai ta tambayeshi meyasa baya yin sallah yace'' mata in zai iya tunawa shi ba musulmi ba ne, tayi ba
in ciki da jin cewa ba musulmi bane shi, amma data tambayesa yana son ya musulunta babu gaddama yace mata eh yana so, nan take ta biya mashi shahada ya kar6i musulunci, Kuma duk ita ta koya mashi yadda zaiyi alwala da sallah.

Har fita ta ke yi da shi tana nuna mashi wuraren sha
awata da ke a cikin gidan, duk don ta faranta masa rai saboda tana son ya saki jiki da ita sosai, sannu a hankali suka fara sha
uwa kullum sai sun shiga Personal gym din gidan a tare suke motsa jikin su, sometimes su shiga Private lounge su sha
ata abunsu harma suyi fira cikin nishadi ta dinga janshi da fira tun yana jin nauyin yin magana da ita harya fara sakewa sosai, wani lokacin kuma takan shiga library da shi ta dauko masu story books tana karanta mashi, sometime su shiga private cinema dinta su kalli movies, ba karamin nisha
i da ilmi ya ke samu ba, in ka gansu suna wasa da dariya ya yin da su ke yin fira sai ka yi zaton sun da
e da sanin juna.
in a short time ta mantar da shi trauma din daya fuskanta abaya, gatanta shi ta ke kamar ranta, tarairayarsa takeyi kamar
wai a cokali, bata son ko tari ya yi, idan dare yayi a kan bedroom counch ta ke kwana tana fuskantarsa yayin da ya ke yin bacci saman gadon ta, saboda bata iya barin shi a bedroom shi ka
Saboda shi ta kira ma'aikatan gidan dukan su, ta tarasu a falo ta nuna masu shi ta garga
e su akan karsu kuskura suyi ganganci gurin kula da shi, su
auke shi tamkar ran su, batason bacin ran shi, cikin girmamawa suka amsa mata da toh.

Ta kuma bawa Private chefs dinta Jotter da doc ya rubuta na diet din sa..

Saboda Omair ta dau
i hutun aikin ta, ta dakatar da duk wani business nata, gaba daya ta sadaukar masa da lokacin ta.

She becomes his role model, his mentor, and his influencer, Mommynsa ta siye zuciyar shi da kulawarta, soyayyarta, kyautatawarta agare sa, tayi brainwashing nashi, yanzu halayansa da
abi'unsa sun sauya, komai nasa natural ne, babu sihiri babu evils gaba daya sun bar jikin shi tun aranar farko da yayi rashin lafiyar nan, Allah ya yaye mashi su, zafin fitarsu ne yasa shi yin jinya.

Halayansa da
abi'unsa sun sauya sun dawo ainihin yadda Allah ya halicce shi da su, a lokaci yayi loosing memory dinsa baya tuna komai daya faru a baya, ko ta tambaye sa game da rayuwarsa ta baya sai yace mata bazai iya tuna komai ba.

Mommynsa ka
ai ya sani da hadiman dake yi masu hidima, sai kuma Chief Owais da kullum Ya ke kiransa awaya suyi video call ko suyi phone call duk da ya manta wanene shi?

Wata rayuwa su ka yi atare?

A lokacin Yana masa kallon Cousin brother dinsa da Mommynsa ta gabatar masa da shi.

Har Lokacin da Prime minister Ya kira ta awaya ya bu
aci Ya na son ganin su a Nigeria, baisan tana a tare da Omair ba, bata fa
a ma kowa ba, iya abun daya sani ta fa
a masa suna da hidindimu a dubai na bikin Ya'yan Uncle din ta, kuma idan ta tafi zatayi sati uku acan, ita ta fara zuwa dubai daga bayane su Nazli suka biyo ta, shi kuma a lokacin ya tafi Nigeria domin ya halarci family Meeting, hakan na nufin ko su Nazli basu san komai game da Omair ba.

A lokacin ta shiga damuwar tayaya zata tafi tabar danta dake bukatar kulawarta duk da akwai maids dake kula mata da shi.

Badan taso ba, Ta dam
a musu amanar shi, taja kunnansu sosai akan su kula mata da shi!

Ranar kamar kar su rabu, ya rurru
eta har bakin motarta da kyar ta shawo kan shi Yabarta ta tafi..

Daga guest house dinta ta wuce Zabeel palace the ruler's resident, kwana biyu tayi kafin su ka shirya tafowa Nigeria ita da Yazrin da Nazli.

Bayan da suka bar
asar, cikin ma'aikatan gidanta, aka samu wani munafuki Yaje har fadar Emir ya kai masa tsegumin Yaron da Mujeedat ta ke boyo agidan ta, ta bayan fage, Emir Khalid Ya turo Royal guards don su Binciko masa wanene yaron da ta ke boye"?

Ranar da guards suka zo palm Jumeira cikin guest house
in mujeedat, guards dinta na ganin su suka basu iznin shiga saboda sunsan Emir ne ya turo su.

A lokacin Omair Yana a zaune kan dining Chair, Chefs sun kewaye shi, ga abinci sun jera mashi akan table, sunata lallashin shi don yaci abinci ya
i ci sun rasa gane meke damun shi, ko magana bai yi masu tun bayan da Shiekha ta tafi! basu san kewa bace ke damun shi..

Sa'ilin da Royal guards din suka shigo dining din
Wata razana su ka yi da ganin Omair, su ka ru
e saboda ganin kyakkyawan matashi mai kama da ji
ar Emir.

Cikin sauri
aya daga cikin guard
in ya
auke shi hoto da wayarsa Ya tura ma Emir duk Fa Yana kallon su a lokacin baisan su wanene ba bai kuma san meya kawo su ba.

Ba'ajima da tura masa hoton ba sai ga kiransa bayan guard din ya yi picking Emir Ya Umarce su da su tabbatar sun tafo mashi da lu'u lu'un nan, Yana son ganin shi a cikin fadar shi"!

Bayan guard din Ya gama yin wayar da Emir, suka Umarci Omair daya taso su tafi fadar mai martaba Khalid Yana son ganin shi.

Rashin sani Yafi dare duhu, Omair baisan wanene mai martaba ba balle yayi musu biyayya ya bisu, hasalima ko kallo ba su ishe shi ba.

Tun suna bashi Umarni yana share su, har suka fara ha
a baki gurin yi masa tsawa akan Ya taso su tafi, kai a karshe da su ka ga ya
iya sai suka kama lallashin shi..
da sukaga dagaske bazai bisu ba, sai suka fara
arin
aukarsa ta tsiya, aikuwa Ya fara na
e hannuwan rigarsa zai yi dambe da su, wayaga Iliya
an mai
arfi.
Chapter 183 · 0% Book details