← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 201

Sashe 8

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takardar dake a hannunta ta mi
a masa jiki asanyaye ya kar6a har zai bu
e muryar Dr din ta katse shi.

"Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne"
A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba.

"Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"?

Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata.

"Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..."
girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...."
bata
are maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta.

Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba,
ata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da
ata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata
azafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...'
kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya
ara kamata.

Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office.

Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da
Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi..

Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace.

Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan"
"Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..."
bata
are maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife
asa a haka suka shiga mota da ita.

Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya fa
a mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina.

Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan.

Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya!

Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba.

Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn.

Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha.

A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta.
lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi.

Saboda zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba.

Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba.

Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi.

Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa bu
e baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane.

Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin bu
e baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun.

Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata le
awa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir.

Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha.

A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi.

A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha.

Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya mi
e Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ru
e a hannunta.

Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta.

Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana
arewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare.

Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nanna
e, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace.

A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata.

Numfashi yaja tare da mi
a hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta.
Chapter 8 · 0% Book details