← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 201

Sashe 73

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karan batajin zata iya kyaleshi hakurinta ya kare, zuciyarta a wuya take, juyawa tayi cikin sauri ta nufi kitchen, jim kadan ta dawo hannunta ruke da bowl mai dauke da jajjagen attarugu, bayan ta shiga saida ta kulle kofar dakin, Ta yadda babu wanda zai iya fita, gadan gadan ta nufi gadon, ta daddage Ta watsa attagurin a gabansa da saman bakin shaidaniyar karuwarsa, ita ma dayar bata kyaleta ba, a cikin idanunta ta watsa mata sauran daya rage, Azabar zafin dayajine yasa shi mikewa daga zaune ya fara dura mata ashiriya, Karuwan nasa suna ta iface iface.

Saukowa yayi daga kan gadon, Yana ta kakkabe gabansa, cikin bacin rai ya nufe ta, da gudu ta fuce yabi bayanta, ga radadi yanaji amma dayake zuciyarsa a bace take, yafi so ya fara azabtar da ita kamar yadda ya saba, fucewa tayi daga falon, Yana kokarim zura kan shi don ya fito, bai aune ba, Yaji An dam
i keyarsa"You"re Under arrest dr chisom" wani irin faduwar gaba yaji mai hade da razana, a rikice ya dubesu, Isod agents ne kewaye da shi, matar tasa tana a bayansu sai haki ta ke yi..

"Uban wanene Ya turoku ku kama ni?

Laifin me na aikata?

Kuna da hankali kuwa, ku shigo har gidana ku kama ni?

Mai gadi da iznin ubanwa suka shigowa"?

Balbalesu da masifa yayi, shi dama borin kunya da hauka ake na
e shi.

"Ba neman izni muka zo nema ba, umarnine daga dg, bamu bukatar 6ata lokaci.." babu ruwansu da tsiraicin shi, da yayi yunkurin yin fada da su don ya gudu aikuwa suka hadu su biyar suka naka
a masa dukan tsiya, fuskarsa tayi rudu rudu da shatun marukansu.

Tasa
eyarshi sukayi, Matar tasa dayake wulakantawa, Ita ta taimaka mashi da mayafinta, ta daure mashi qugunshi saboda ta kare mashi mutuncin shi, ko tambayar jami'an laifin da yayi batayi ba, saboda tasan mijin nata criminal ne, kuma ita taimakonta su ka yi don tasan badan zuwansu ba, da wallahi har kasheta zai iyayi saboda bakar zuciyarsa, akan idonta suka tura shi cikin motarsu, sai da taga tafiyarsu, ta koma cikin falon, ta kulle kofar, a lokacin karuwan nasa sun fito daga dakin zir haihuwar uwarsu, akan floor suka zauna suna jiran ya dawo, sai jinyar wurin da ta zuba masu attaguri su ke yi.

Zagayawa tayi cikin san
a ta nufi kitchen ta dauko tabaryar karfe, ta dira akansu kamar Allah ya aikota ta dinga jibgarsu kamar ta samu jakuna, duk saida ta raunata gabban jikinsu, suka dinga ihu suna kuka tare da yi mata magiya suna rokonta tayi masu rai, a karshe da suka ga bata da niyar kyalesu, da gudu suka fuce daga gidan tana ta kiransu don su kar6i suturar su ko waiwayon ta ba su yi ba.

Lokacin da dr Adam Ya kira md Ya sanar da shi abun da ke faruwa, Yana a cikin Motarsa sai baza gudu ya ke yi zai tafi airport, don Ya gudu yabar
asar kafin su ritsa da shi, Yana driving zufa tana ta tsatstsafo ma shi saman fuskar shi, kwata kwata baida kwanciyar hankali, zullumi da fargaba sun cika zuciyar shi, Allah Allah ya ke yabar kasar.

Yana karasowa Airport din Ya suri akwatinsa da jakarsa Ya nufi ciki sai sauri yakeyi, sai daya kammala duk wani clearance harya shiga Jirgi Ya zauna a seat dinsa, jirgin yana gab da zai tashi Unfortunately, Isod soldiers suka ritsa da shi a cikin jirgin, suka fito da shi sai mazurai yakeyi yana rawar jiki, hatta suitcase dinsa da Jakarsa saida aka fiddo mashi da su, wato ya yi gudun gara ya fa
a gidan zago...
_______________________________
*NATASHA*
Yadda taga rana haka taga dare, Ta kasa runtsawa, damuwa da bakin ciki sun mata katutu a cikin zuciyar ta, a kan idonta
arfe 6 na suba tayi..

Tana tsaka da yin safa da marwa cikin dakin da Owais Ya kulleta, cikin kunci da bacin rai take jan tsoki tare da
wafa, ranta yakai makura agurin Baci, Ummi kawai takeso ta gani don taji meyasa taci amanarta?

Meyasa zata matsa mata tazo Nigeria don a wulakanta rayuwarta?

Tabbas bazata kyale ta ba, Alwashi ta daukarwa kanta saita Fa
awa big boss komai da su ka yi mata..

Kwatsam tajiyo motsin bude
ofa, afusace ta nufi kofar, kafin ta karasa suka shigo su biyu, Ummi ce sanye da dogon hijab, Chief Owais yana abiye da bayanta bayan da ya shigo ya kulle
ofar, kukan Kura Natasha tayi ta dira agaban Ummi ta sha
e gaban hijabin ta...

"Kin yaudare ni ummi, Meyasa zakiyi min haka?

Meyasa?

Dama kin kirani ne don inzo Nigeria a wulakanta rayuwa ta?

Tun jiya nake a kulle kamar dabba?"?

In a calm Voice Ummi tace"Natasha, Ki kwantar da hankalin ki, Kinsan wacece ni kin kuma san halina, ba canzawa wa nayi ba, Ba yaudararki nayi ba, kuma ban kiraki don a wulakanta ki ba...."
bata kare maganar ba Natasha ta katse ta cikin fushi tace "Bazan taba yarda da ke ba Ummi, bayan haka ki sani bazan
yaleki ba, saina fadama big boss abunda kikayi min keda wannan mutumin..." ta fa
a tana nuna Owais da Yatsan ta..

Da sauri Ummi ta buge hannunta"karki kuskura ki
ara nunasa da yatsa idan ba so kike ki rasa yatsanki ba, meke damunki ne?

Ki nutsu ki saurare ni mana!

Zan yi maki bayanin da zaki fahimce ni!

Ni bazan cutar dake ba, ba kuma zan bari a cutar dake ba.."
girgiza kai tayi"ba zan taba fahimtarki ba Ummi, na gama yarda dake..."
"Kin fiye taurin kai Natasha, In har ba zaki saurareni ba zaki dawwama a kulle cikin dakin nan, ba zan iya taimakon ki ba ba"!

Ta fada tare da duban Chief Owais"am really sorry da halin Natasha, tana da wuyar sha'ani ba kowa ke iya zama da ita ba sai wanda ya saba da ita..."
jinjina mata kai yai"karki damu Ummi, na saba mu'amala da mutane masu taurin kai da kafiya irin ta, dama na kawo ta ne saboda kin damu da rashin ganin ta.."
Natasha dake kallonsu sai rarraba kwartayen idanun ta ke yi akan su, cikin rudu da rashin fahimtar manufarsu akanta.

"Ba zaku fadamin dalilin ku na kulle ni ba?

Laifin me na aikata?

Ko ina da alaka da ku ne?

Idan big boss ne yayi maku laifi ni meye ruwana a ciki?

Bani da akaka da shi! yarinya kuma da kake tuhuma ta akai na fada maka kudi ya biya don raine ta, kuma ni bansan yar wacece ba, bayan haka na fada maka ya kar6i abunsa!

Meyasa kuke so ku haukata ni ne eyeeh?

Ku barni in koma
asata!

Idan ba haka ba zan tona maku asirin kunyi garkuwa dani idan na ku6uta daga tarkon ku, Idan kuma big boss Yaji ku kuka da kanku..." ta fa
a tana nuna su da yatsan ta.

Basu saurareta ba, Suka fuce tana kokarin biyosu kofar ta datse.

"Har yanzu baku tabbatar da abunda kuke zargi akan Big boss ba, ni nasan bai da sanya hannu, pls bana son tuhumar da kuke yi masa ya shafi Natasha, Ba ta da laifi, batason kowa a Nigeria ba, gashi har ta fara yi min kallon naci amanarta, Pls ka sassauta mata, Ku barta ta tafi koda ba zata zauna anan ba"
"Kinsan meta aikata"?

A
an ru
e ta dube shi"Sir bangane me kake nufi ba?

Ji ya tazo kasar nan, wani laifi ne tayi"?

Atakaice Ya labarta mata abun daya faru jiya da daddare bayan ya ritsa ta a dakin su Unaisah.

Dafe kai tay da hannu daya, Kunya da takaici Ya hana ta saka idanun ta Cikin na Owais..

Da tasan Natasha zata aikata abun kunyar nan da bata amsa bukatarshi na kiranta ba.

"Am sorry sir, ban sani ba, bansan Natasha zatayi masu haka ba, da ban bari ba, ni banma san lokacin da ta fuce daga
aki na ba, na riga nayi bacci..."
"Karki damu, Na fahimce ki, amma Natasha zata kasance a kulle cikin
akin nan, har zuwa lokacin da zamu kammala binciken mu a kanta, sannan bana son kowa ya san tana anan, daga ni saike, sai kuma chef din da zai din ga kawo mata abinci, ina fata bata fada ma musan game da zuwanta ba..." jinjina mashi kai tayi.

"But pls, Ku kula da ita, abun da ta aikata ma Unaisah banji dadin shi ba, Tasa naji kunya wlh, amma ka yi hakuri, kasan dabi'ar turawa basu gudun abun kunya"
Da sakin fuska yace"na sani, Nima cikinsu nataso, asalima kakata baturiyace amma ba irin natasha ba.." ya fa
a da zolaya duk don ya kwantar mata da hankali, murmushi ta yi ta
an ji sanyi aran ta..
~_______________________________
around karfe biyu na rana suka kammala shirin tafiya Airport, fitowa su kayi daga bedroom dinsu, yana sanye da suit ya lullu6e fuskarshi da mask, ya kuma saka shade baki a idanunsa.
hannunsa daya ruke yake da suitcase dinsa, yayin da
ayan hannunsa ke a ruke da passports din su.

A falo ya tsaya yana jiran ta
"Kiyi sauri mu tafi, kada lokaci ya
ure mana.." tana daga ciki ta amsa mashi da toh..
gabansa sai faduwa ya ke yi rass rass, in har ba barin kasar nan yayi ba baida sauran kwanciyar hankali, Allah Allah yake ta fito su tafi..

Har ya bude baki zai kara yi mata magana, sai gata ta fito daga dakin, sanye da Black abaya, ta saka nikab kamar yadda Ya umarce ta da tayi, ko idanunta baka iya gani.

"Pravin ni ban saba da nikab ba, bana jin dadin shi, duk a takure nake"..

"Hakuri zakiyi mu tafi"
A lokaci ji take kamar ta fasa ihu saboda damuwar rashin taimakon da Turai batayi mata ba, Yanzu tana ji tana gani zata tafi tabar Ahlin Obie, tun dazu da ya ke ta mata fa
an tayi sauri ta shirya tana sane ta tsaya yin nawa duk don saboda ta sanya rai zasu neme su.

Pravin kwata kwata baisan ta yi waya ba, ta ki fada masa ne saboda tasan zai hana, kuma jiya turai ta ce karta fa
a masa.
Chapter 73 · 0% Book details