← Book details The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 201

Sashe 154

The Prison Of Destiny Final Step Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kema kin sauya sis, gyaran jikin nan ya kar6eki wlh, kamar kece amaryar ma" murmushi batool tayi"Albarkacinki nake ci Unaisah, shiyasa nima nake samu ana zuwa dani spa din, naso ace tare zamuyi aure arana daya, amma Allah bai nu
fa ba, daddy yace saina kammala karatu ko zai barni in kula masu zuwa neman aurena"
"Nima nayi fatan haka batool, amma karki damu, kema in sha Allah zakiyi aure nan bada jimawa ba"
"Na cika ki da surutu mrs owais, ki kwanta ki huta, Yau henne night ne, har nakosa time yayi wlh..."
Ta fa
a tare da lullu6e mata jikin ta da bargo
"Nan da wasu yan kwanaki a gadon mijin ki zaki dinga kwanciya" harara Unaisah tayi mata tana murmushi..

Tana jiyo motsin fitar Batool daga dakin sama sama kafin bacci mai da
i ya yi awon gaba da ita..

Wuraren
arfe 4 da rabi, Yan matan Amarya suka fara taruwa cikin gidan, idan kuka ji na ambaci yan matan amarya kunsan wa nake nufi, Abokananta na amana wato ex-prisoners.

Ringing din wayarta ne ya farkar da ita, slowly ta bu
e idanunta da suka kada jawur, tayi shiru tana kallon ceilling.

Har kiran ya katse batayi picking ba, wani kiran ne ya kara shigowa da sauri ta
auko wayar daga kan drawer ta yi picking tare da karawa a kunnanta.

"Na kira ki ne, don na tuna maki saura kwanaki ka
an ki zama matata"
murmushi tayi"I can't wait to own you my man"
Sautin kayataccen murmushinsa tajiyo mai ha
e da fitar numfashin sa.

"I saw your graduation pictures on social media, and people were commenting on them, I felt indescribable jealousy why did you share your photos? why babe?

Ba nace banda pics ba.."
yamutsa fuska tayi kamar tana a gaban shi"Am sorry, kasan ba yadda za'ai in hana photographers
aukar hoto na banma san sunyi ba, kuma wallahi bani nayi sharing din su ba, friends dina ne, amma zan kiyaye nan gaba"
"Okay, karki damu, na fahimce ki"
Yana kokarin katse kiran tayi saurin furta"am na manta ban fada maka ba, Yau Henna night ne, wani kalar lalle kake so inyi"?

"Unaisah, check your WhatsApp I'll send you a message, take care"
"Okay ka kulamin da kanka" daga haka su kayi sallama.

Saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet ta shige don tayi wanka.

Bayan mintuna, ta fito Jikinta sanye da bathrobe fara,
Closet ta nufa don ta shirya kanta, jim kadan ta fito jikinta sanye da kimono Robe.

Wayarta ta dauko ta shiga whatsapp chat dinsu don taga idan ya tura mata sakon
Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta sa'ilin da idanunta suka sauka akan screen din wayar tana karanta message din shi.
_I prefer maroon henna, zaifi dacewa da soft skin din hannun ki, When the henna is done, send me pictures so I can see"
Batasan ya akai ta ke jin dadi a duk lokacin data ga sakon shi ta whatsapp.

Reply ta yi masa "Okay Sir"
~______________________________~
Unexpected ta tsinkayi muryoyin su daga waje
"Our bride-to-be!

Sis!

Mrs Owais!

Unaisah!

Where are you?

It's time for the henna!

Masu lallen sun zo, we're waiting for you"
Kafin ta yi wani yunkuri suka turo kofar
akin nata, Ko sallama babu, zare eyes dinta tayi da mamakin ganinsu ta shiga furta sunayen su"Hibba!

Hawwa!

Rubina!

Hannah!

Saukar Yaushe?

Shine baku kira kun fadamin za ku zo ba"?

Ta fa
a tare da nufar su ta soma yin hugging din su.

"Muna sane muka ki sanar dake saboda mu baki mamaki" hanna ce ta fada tana dariya.

Hawwa tace"tun bayan sallar La'asar, muka iso, a gidan daddyn mu mu ka sauka.."
"Amma dai kun shammace ni wlh, naji dadin ganin ku mutan kaduna da lagos, da har na fidda rai da zuwanku"!
a baki su ka yi gurin furta
"mun yi missing na ki, muna tayaki murnar kammala karatu, ay mana afwa bamu halarta ba, mun zo a makare, fatan mun same ki lafiya"?

"Nima nayi missing naku, wlh karkuji komai zuwan da ku ka yi ya fanshe laifin ku..

"
ta fada tana kallon su, kowaccensu hutu ya zauna mata, sun
ara girma sun zama cikakkun yan mata, suturun jikinsu masu tsada.

"Ya gajiyar tafiya?

Ya kuma kuka baro mutanan gidan" har suna hada baki gurin furta"suna nan lafiyalou, sunce mu gaishe masu da amaryar su"
"Wow Sis kinga yadda kika canza?

Kinyi haske kin kara kyau, fatar ki sai
yalli take..."
rubina ce ta fada tana taba skin dinta" buge hannunta Unaisah tayi tana dariya.

Hibba Tace"wallahi nima abun da zance kenan, kin zama babbar mace, tubarkalla anya Unaisah baki shan maganin
ara hips da breast" zare mata idanu Unaisah tayi, gaba daya suka tuntsire da dariya..

Kamar daga sama suka tsinkayi muryar Batool daga bayan su..
an sa ido, Tubarkalla, komai na sis dina natural ne daga Allah, dama zuwa kukayi don ku sanya mata ido ko" ta fada da zolaya yayin da take karasa shigowa cikin dakin.

Dariya suka sanya gaba dayansu..

"Ba zuwa nayi don muyi fira ba, nazo ne don in fada maku ku fito mu sauka down lokacin
unshi yayi"
arashe maganar tare da ruko hannun Unaisah a cikin nata su ka yi gaba sauran suka bi bayan su.

Tunkan su
arasa saukowa down, suka hango sauran bridemaids din da ke shigowa.

Parveen ce agaba ta dauki wankan abaya, idanunta sanye da shade baki, Yadda kasan hajiya saratu na tafiya, Cikin dattako take taku
ai tana hura hanci, ta ruke hand bag a hannunta na hagu,
ayan hannun ta ru
e Cupcake din da take ci.

Sai shan
amshi ta ke yi kamar iska nayi mata wari, tana ji da kanta
iyar minister.

"Wa nake gani kamar foodie?

Dagaske ke ce"?

Hawwa ce ta fa
Muryar ta da taji ne yasa ta kai dubanta garesu tana ganin su ta washe baki tare da
aga masu hannu ta nufe su, bakomai ne ya basu dariya ba face ganin gefe da gefen bakinta da yayi dama dama da cake din da take ci.

Tana karasawa gurinsu suka soma rungumarta.

"Ni babu wanda zai rungume ni?

Ko baku ganni bane"?

A tare suka dago tare da duban
ofar shigowa falo, waro idanu waje su ka yi ganin Jemimah a tsaye ta ru
e qugunta, sanye take da lace ta coge daurin kallabi, Yarinya fa ta girma a yanzu takai kusan shekara goma sha biyar.

Su biyu ne su ka zo, tana a tare da yayarta Azeeza da ke tsaye a bayanta, itama ta
ara girma duk da har yanzu babu tsawo sai dai tana da dirin jiki, ayanzu ta wuce shekara ashirin da
auriya.

"Jemimah?

Wa ya gayyace ki?

Ba mun ce bamu san ganin Yara ba?

Ko akwai tsaranki anan ne.."?
da zolaya Parveen tayi maganar tare da nuna mata hanyar fita"Get Out"!
harara Jemimah ta watsa mata"ki bari idan bikin ki yazo sai ki hanani zuwa, kuma ai Sis Unaisah ne ta gayyace ni, ba ke ba"
"Gaskiya jemimah ki nemi tsararrakin ki, tayaya zaki zo cikin mu, akwai tsaranki ne"?
yacewa su ka yi da dariya..

Zura hannu tayi cikin purse dinta suka kura ido suna jira suga dame ta zo masu.

Pistol ta zaro, ta saita su da ita.

Gaba daya suka razana tare da du
ewa
asa suna rokonta karta harbesu, kwashewa tayi da dariya.

Bushewa da dariya Azeeza tayi tare da girgiza kai tace
"bafa bindigar gaske bace, ta wasan yaran ce.."
ajiyar zuciya suka sauke tare da mikewa tsaye gaba daya sunyi zaton bindigar gaske ce, saboda sunsan zata iya dauko ta daddyn ta..

"Duk wanda ya kara gigin kora ni, sai na fasa kan shi da bindigar nan" ta fada tana nuna kawunan su da bindigar, daga ka ganta kaga sangartacciya dabi'un ta irin na yara, tuntsirewa su ka yi da dariya..

Batool tace"Like father Like daughter, Jemimah wannan bindigar ta wacece kika dauko ko ta daddy mubarak ce"?

Azeeza tace"shiya siya mata hada kakin sojoji, saboda ta fa
a mashi idan ta gama karatu soja zata zama irin shi, don ta dinga zuwa ya
yalewa su ka yi da dariya cikin nisha
Kafin suka fara huggin dinsu irin gaisuwar da suka saba yiwa junansu duk idan suka hadu..

"Assalamu alaikum, me ake tattaunawa ne ba a jira na karaso ba...

" gaba daya suka jiyo tare da kallon su, kusan a tare suka shigo, Deeja ce tayi maganar, shigowarta kenan jikinta sanye da atampa, ta kashe daurin dankwalin ture kaga tsira, ga wani hadadden shade da tasaka ma idanun ta.

A kafa
a ta yafa veil din ta hannunta ruke da wayarta..

Cike da farin ciki suka hada baki gurin furta"DEEJA!"
"Na'am
an amanana!

Am sorry amaryar mu, banzo da wuri ba, yau natashi ba lafiya amma da sau
i yanzu Alhamdulillah".
ta fa
a tana nufar su, daya bayan daya ta yi hugging din su tare da manna masu peck a foreheads in su, duk su ka yi mata ya jiki? ta amsa da sau
Badajimawa ba, Sajeeda da Zeenatu suka shigo tare da Sarah da yasmin da sauran kawayensu wadanda gaba dayansu Ex-prisoners ne gaba dayansu sun daukin wanka na mutunci, sun kai su Ashirin bayan sun gama gaggaisawa da junan su nan fa wata sabuwar firar ta 6arke a tsakanin su, haniyar firar da su ke yi ta cika Gidan gaba
a ya, bakajin komai sai sautin surutun su da dariyar su.
arfe biyar daidai masu
unshi su ka
araso gidan.

A main Falo suka baje kolin su, sai da suka fara
awata seating area din falon da kayan decoration din su, daga daidai inda zasuyi zaman
unshin suka shimfi
a Red Rug (jan kilishi) daga kewayen shi floor sofa set ne daga saman kilishin wasu
uma
uman floor cushions ne a jere, kamar shimfi
ar sarki, daga tsakiyar rug din farantai ne
auke da kayayyakin
unshi.

Kafin su fara Aunty Danejo ta kawo masu soft drinks da snacks a cikin tray, sunji dadi har su ka yi mata godiya.

Music
in da su ka kunna a speakers ya kara
e ko'ina na gidan, hakan ba karamin armashi ya karawa daren na su ba.

Daga tsakiya Amarya ta zauna kan cushion.
Chapter 154 · 0% Book details